DUNIYA MAKARANTA 002

“`Idan kwalba ta fashe za’aji kukan fashewar ta ne sau daya (1) amma za’a taka ta sau goma (10) haka mummunar magana take idan aka fadeta, za’aji ta ne sau daya (1) amma zata dade tana zungurar zukata…….”“`
“`Kada ka bayyana murnarka a gaban Wanda yake cikin damuwa, kada ka fadi yawan dukiyarka a gaban talaka. Kula da damuwar jama’a yana cikin alamun imani……”“`
“`Shan toka da tsare suke sawa a qosa da kai, yawan raha da sakin jiki kan jawo maka wulaqanci. Ka lizimci tsakiya a komai shine alheri…..”

Advertisements