BURIN MANYAN MUTANE DA MA’DAUKAKIYAR HIMMA A RAYUWA (Dr. Mansur Sokoto)

Dr. Mansur Sokoto
BURIN MANYAN
MUTANE DA
MA'DAUKAKIYAR
HIMMA A RAYUWA
Abu Nu'aim ya ruwaito
a cikin "Hilya", da Ibnu
Asakir a cikin "Tarikh",
daga Abdurrahman Ibnu
Abiz Zinad, daga
babansa ya ce:
ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﺠﺮ ﻣﺼﻌﺐ
ﻭﻋﺮﻭﺓ ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ
ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ، ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ :
ﺗﻤﻨﻮﺍ، ﻓﻘﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ
ﺍﻟﺨﻼﻓﺔ، ﻭﻗﺎﻝ ﻋﺮﻭﺓ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ
ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺃﻥ ﻳﺆﺧﺬ ﻋﻨﻲ
ﺍﻟﻌﻠﻢ، ﻭﻗﺎﻝ ﻣﺼﻌﺐ: ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ
ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ ﺇﻣﺮﺓ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ،
ﻭﺍﻟﺠﻤﻊ ﺑﻴﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺑﻨﺖ
ﻃﻠﺤﺔ ﻭﺳﻜﻴﻨﺔ ﺑﻨﺖ
ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ، ﻭﻗﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﻋﻤﺮ: »ﺃﻣﺎ ﺃﻧﺎ ﻓﺄﺗﻤﻨﻰ
ﺍﻟﻤﻐﻔﺮﺓ « ﻗﺎﻝ: ﻓﻨﺎﻟﻮﺍ ﻛﻠﻬﻢ
ﻣﺎ ﺗﻤﻨﻮﺍ، ﻭﻟﻌﻞ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺪ
ﻏﻔﺮ ﻟﻪ ".
Ya ce:
"Mus'ab da Urwatu da
Abdullahi bn Zubair (ra)
(duka su 3 'ya'yan
Zubair bn Auwam (ra)
ne), da Abdullahi bn
Umar (ra) sun hadu a
Hijru Isma'ila (a jikin
dakin Ka'aba), sai suka
ce: kowa ya fadi
burinsa, sai Abdullahi bn
Zubair (ra) ya ce:
"Amma ni Khalifanci
nake buri".
Sai Urwatu ya ce:
"Ni kuma ina burin a
dauki ilmi a wajena".
Sai Mus'ab ya ce:
"Ni kuma ina burin
sarautar Iraqi, kuma in
auri A'ishatu bnt Dalha,
da Sukaina bnt
Hussain".
Sai Abdullahi bn Umar
(ra) ya ce:
"Amma ni kuma ina
burin samun gafarar
Allah ne".
Sai Abuz Zinad ya ce:
kuma dukkansu kowa
burinsa ya cika, ya
samu abin da yake so,
shi kuma Abdullahi bn
Umar (ra) da fatan
Allah ya gafarta masa".
Duba:
ﺣﻠﻴﺔ ﺍﻷﻭﻟﻴﺎﺀ ﻭﻃﺒﻘﺎﺕ
ﺍﻷﺻﻔﻴﺎﺀ )309 /1 (، )/2
176 (، ﻭﺗﺎﺭﻳﺦ ﺩﻣﺸﻖ ﻻﺑﻦ
ﻋﺴﺎﻛﺮ )267 /40 (، )/58
219 (، ﻭﺳﻴﺮ ﺃﻋﻼﻡ ﺍﻟﻨﺒﻼﺀ ﻁ
ﺍﻟﺮﺳﺎﻟﺔ )141 /4 (، ) /4
431).
Wadannan duka
manyan mutane ne,
mutum biyu a cikinsu
Sahabban Annabi (saw)
ne, su ne Abdullahi bn
Umar (ra) da Abdullahi
bn Zubair (ra), su kuma
Urwatu bn Zubair da
Mus'ab bn Zubair suna
cikin Tabi'ai ne.
Dukansu 'ya'yan Zubair
(ra) su uku kowa Allah
ya cika masa burinsa a
zahiri, saboda abin da
suke buri abu ne da zai
iya bayyana wa mutane
a nan duniya.
Shi Abdullahi bn Zubair
(ra) ya zama khalifa,
daga baya aka kashe
shi, Abdul Malik bn
Marwan ya zama
khalifa a bayansa.
Haka shi ma Mus'ab ya
zama Gomnan Iraqi a
lokacin khalifancin
yayansa Abdullah bn
Zubair (ra), kuma ya
auri wa'dannan mata
guda biyu, wadanda
babu kamarsu a
wannan lokaci, wajen
kyau da daukaka a cikin
mata, su ne A'ishatu
'yar Sahabi Dalhat bn
Ubaidillah (ra), da
Sukaina 'yar Sahabi jikan
Annabi (saw) Husaini bn
Aliyu bn Abi Dalib (ra).
Shi kuma Urwatu bn
Zubair ya zama babban
malamin hadisi a
zamanin Tabi'ai, shi ya
sa ba za ka iya iyakance
sunansa a cikin
littatafan hadisi ba,
saboda yawan ruwaito
hadisai.
Duka abin da ya gabata
babbar alama ce da
take nuna shi ma
Abdullahi bn Umar (ra)
Allah ya cika masa
burinsa, saboda nasa
burin ya fi girma da
falala, kuma ya fi nuna
bukatuwa zuwa ga
Allah (T).
MU MA BABBAN
BURINMU A DUNIYA SHI
NE; SAMUN GAFARAR
ALLAH DA YARDARSA.
YA ALLAH KA CIKA
MANA BURINMU.
— Aliyu Sani
8 April 2014 at 16:08

Advertisements

HAKKOKIN MUSULMAI A KAN JUNANSU (Dr. Mansur Sokoto)

HAKKOKIN MUSULMAI A
KAN JUNANSU
– Hakika Allah ya umurci
Musulmai da hadin kai
wajen tsayar da Addini,
Allah ya ce:
{ ﺃَﻥْ ﺃَﻗِﻴﻤُﻮﺍ ﺍﻟﺪِّﻳﻦَ ﻭَﻟَﺎ
ﺗَﺘَﻔَﺮَّﻗُﻮﺍ ﻓِﻴﻪِ{ ]ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ :
13]
"Ku tsayar da Addini
kada ku rarraba a
cikinsa".
Sai Allah ya hanesu ga
rarrabuwa. Kuma
wannan shi ne abin da
ya shar'anta mana,
kuma ya yi wasiyyansa
ga Shugabannin
Manzanni; Muhammad
(saw), Ibrahim (saw),
Musa (saw), Isa (saw),
Nuhu (saw).
– Kuma Allah ya hanesu
a kan sabani, inda ya ce:
{ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻨَﺎﺯَﻋُﻮﺍ ﻓَﺘَﻔْﺸَﻠُﻮﺍ
ﻭَﺗَﺬْﻫَﺐَ ﺭِﻳﺤُﻜُﻢْ { ]ﺍﻷﻧﻔﺎﻝ :
46]
"Kada ku yi jayayya a
tsakaninku sai ku
karaya, karfinku ya
kare".
– Kuma ya umurcesu da
taimakekeniya, inda ya
ce:
{ ﻭَﺗَﻌَﺎﻭَﻧُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺒِﺮِّ
ﻭَﺍﻟﺘَّﻘْﻮَﻯ { ]ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ2 : ]
"Ku taimaki juna a kan
aiyukan alheri, da jin
tsoron Allah".
Wannan ya sa Shari'a ta
ba mu labarin cewa;
musulmai suna da
hakkoki a kan junansu,
kuma ta yi kira ga a
kula da su, kuma a
kiyayesu, don al'ummar
musulmi ta zama
al'umma mai karfi da
hadin kai, mai tausayin
juna, wacce tsaro da
zaman lafiya zai
jagoranceta.
* Daga cikin hakkokin
musulmi a kan dan
uwansa musulmi akwai:
1. Kada ya ZAGE shi, ko
ya TSINE masa, kuma
kada ya FASIKANTAR
da shi, ko ya KAFIRTA
shi.
– Annabi (saw) ya ce:
« ﺳﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﺴﻮﻕ
ﻭﻗﺘﺎﻟﻪ ﻛﻔﺮ»
"Zagin musulmi
FASIKANCI ne, yakarsa
kuma KAFIRCI ne".
– Kuma ya ce:
« ﻻ ﻳﺮﻣﻲ ﺭﺟﻞ ﺭﺟﻼ
ﺑﺎﻟﻔﺴﻮﻕ، ﻭﻻ ﻳﺮﻣﻴﻪ
ﺑﺎﻟﻜﻔﺮ، ﺇﻻ ﺍﺭﺗﺪﺕ ﻋﻠﻴﻪ، ﺇﻥ
ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﺻﺎﺣﺒﻪ ﻛﺬﻟﻚ »
"Babu mutumin da zai
jefi wani mutum da
fasikanci, ko ya jefe shi
da kafirci face kalmar
ta dawo kansa, in
wancan mutumin nasa
bai kasance hakan ba".
– Kuma du ya ce:
« ﻭﻟﻌﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﻛﻘﺘﻠﻪ،
ﻭﻣﻦ ﺭﻣﻰ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﺑﻜﻔﺮ ﻓﻬﻮ
ﻛﻘﺘﻠﻪ »
"Tsine wa mumini
kamar kashe shi ne,
duk wanda ya jefi
mumini da kafirci kamar
ya kashe shi ne".
Ma'ana; tsine masa
haramun ne kamar
yadda kisansa haramun
ne, kuma dadai suke a
zunubi.
Saboda haka wajibi ne a
kan kowane musulmi
ya san wannan hakki da
yake kansa, kuma ya
kiyaye shi a kan dan
uwansa musulmi, don a
zama al'umma guda
daya, kamar yadda
Allah yake so, kuma ya
yi umurni.
– Aliyu Sani

FARKON SHIGA ALJANNAH (SAWW).

FARKON SHIGA
ALJANNAH (SAWW).
*************
*************
******
Farkon wanda zai shiga
Aljannah aranar
Alqiyamah shine
Annabinmu
Muhammadu (saww)
kamar yadda Imamu
Muslim ya ruwaito daga
Sayyiduna Anas bn Malik
(rta) yace Manzon Allah
(saww) yace:
"ZAN ZO KOFAR
ALJANNAH ARANAR
ALQIYAMAH, SAI IN
KWANKWASA, SAI MAI
TSARONTA (WATO
MALA'IKA RIDHWAN)
YACE : "KAI WANENE?".
ZAN CE MASA
"MUHAMMADU NE". SAI
YACE : "SABODA KAI
AKA UMURCENI KAR IN
BUDE MA WANI KAFIN
KA".
Acikin wata ruwayar
kuma yace: "NINE NAFI
DUKKAN ANNABAWA
YAWAN MABIYA, KUMA
NINE FARKON WANDA
ZAI KWANKWASA
(KOFAR ALJANNAH)."
(Muslim ne ya
ruwaitoshi).
Acikin ruwayar Abu
Hurairah kuma Annabi
(saww) yace: "MUNE NA
KARSHE KUMA MUNE NA
FARKO ARANAR
ALKIYAMAH. KUMA
MUNE FARKON
WADANDA ZASU SHIGA
ALJANNAH".
(Bukhariy da Muslim ne
suka ruwaitoshi).
Akwai kuma hadisan da
suka nuna cewar
Talakawan wannan
al'ummar sai sun riga
mawadata (Masu kudi)
shiga Aljannah, kamar
yadda Imamu Ahmad
da Tirmidhiy suka
ruwaito Daga Sayyiduna
Abu Hurairah (ra) yace
Manzon Allah (saww)
yace:
"TALAKAWAN
MUSULMAI ZASU RIGA
SHIGA ALJANNAH KAFIN
MAWADATANSU DA
TSAWON RABIN WUNI
GUDA, WATO SHEKARU
DARI BIYAR KENAN (500
years).
Imamu Muslim kuma ya
ruwaito daga Sayyiduna
Abdullahi bn Amru bn
Al-Aas (ra) yace
Manzon Allah (saww)
yace:
"TALAKAWA DAGA
CIKIN SAHABBAN DA
SUKAYI HIJIRA, ZASU
RIGA MAWADATANSU
SHIGA ALJANNAH
ARANAR ALKIYAMAH
DA TSAWON SHEKARU
ARBA'IN".
(Muslim ne ya
ruwaitoshi).
Don haka ya kai 'dan
uwa, Kada wadata tasa
ka rika yin Girman kai ko
Alfahari. Domin girman
kai babu inda zai kaika
sai wuta. Kuma koda ka
tsaya ka bi Allah, sai
Talakawa sun rigaka
shiga Aljannah kamar
yadda Sahihan hadisan
nan suka tabbatar.
Ba wani abu ne zai
kawo maka wannan
jinkirin shiga Aljannar
ba, illa hisabin dukiyarka
da za'ayi ma. Domin ba
zaka gushe daga gaban
Zatin Allah ba, sai an
tambayeka akan
kowanne kwabo da Sisi
da Naira da dollars : Ta
ina ka sameta? Kuma ta
ina ka 'batar da ita?.
Acikin bin Allah, ko
kuma bin sha'awar son
zuciyarka?
Shi kuwa Talaka bashi
da komai sai ransa. Don
haka babu abin
tambaya sosai akansa.
Amma duk da haka ina
jan hankalin 'Yan uwana
Talakawa cewa mu
Zage damtse wajen
neman ilimi da bauta ma
Allah ta hanyoyin da
suka dace domin samun
babban rabo awajen
Allah. Kar mu sake
wasu sun fimu jin dadi
aduniya, kuma alahirar
ma su sha gabanmu.
Hakika mun gode ma
Allah da ya sanyamu
acikin wannan al'ummar
ta Annabi Muhammad
(saww). Allah yasa
muna daga cikin sahun
farkon wadanda zasu
shiga Aljannah aranar
Alqiyamah. Acikin
Makobtaka da
Masoyinmu (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU
WHATSAPP
(15-09-1437)
20-06-2016.

FALALA ASHIRIN (20) MARABA DA RAMADAN

Mal.Aminu Ibrahim
Daurawa
FALALA ASHIRIN (20)
MARABA DA RAMADAN
1, A cikin sa aka saukar
da Alkurani mai girma,
Bakara 185
2, Dukkan littafan Allah
mai girma, a cikin sa aka
saukar da su, takardun
Annabi Ibrahim a daran
farko na watan,
Attaurar Annabi Musa a
ranar 6 ga watan, Injilar
Annabi Isa 13 ga
watan, Alkur'anin
Annabi Muhammad
saw, a ranar 24 ga
watan, Musnad Ahmad,
shaik Albaniy ya
ingantashi.
3, Ana bude Kofofin
Aljannah a cikin watan,
4, Ana rufe kofofin
wuta
5, Ana daure
kangararrun shedanu
6, Ana bude kofofin
Rahma
7, Ana bude kofofin
sama
8, mai kira yana kira, ya
mai neman alkhairi
gabato, ya mai neman
sharri, kayi nisa
9, A ko wanne dare,
Allah yana yanta bayi
daga wuta
10, A cikin watan akwai
daran lailatul kadri
wanda yafi wata dubu,
11, Ana kankare
zunubin shekara, Annabi
saw yace, Daga
Ramadana Zuwa
Ramadan aka kankare
zanubi duka, mutukar
an nisaci kaba'ira
12, An durmuza hancin,
Duk wanda Ramadana
ya kama har ya wuce
baiyi aikin da zaayi
masa Rahma ba.
13, Umra a cikin watan
Ramadan daidai yake da
aikin hajji tare da
Annabi, saw a wajan
lada.
14, watan da akafi
shiga I'itikaf, a goman
karshe
15, Watan da ake amsa
Addu'a
16, Watan da akeson
yawaita Karatun
Alkur'ani mai girma,
akalla sauka hudu, duk
sati daya.
17,Watan Alkhairi da
kyauta da ciyarwa, da
samun dumbin lada, duk
wanda ya ciyar da mai
azumi, zai kara samun
lada kamar yayi azumi.
18, Watan da akafi
yawan kiyamul laifi da
tarawih da Tahujjud da
Asham, don kara
kusanci da Allah.
19, Watan neman
nasara akan makiya,
Sahabbai sukanyi
amfani da watan
Ramadan, wajan addua
mai tsanani akan
makiya.
20, watan sada
zumunta,da karfafa,
yan uwantaka ta
musulunci,
Allah ka kaimu
Ramadan, da imani da
son Allah da Manzonsa,
Ka karbi ibadun mu ka
yafe mana. Ya Hayyu Ya
Qayyum.

SAMUN MASU WA’AZI CIKIN AL’UMMA BABBAN ALHERI NE : Dr Ibrahim Jalo Jalingo

SAMUN MASU WA'AZI
CIKIN AL'UMMA BABBAN
ALHERI NE:
Lalle a samu mutane
cikin wata al'umma
suna tashi suna yin
wa'azi, suna kiran
jama'a da su tsaida
Sunnah, su gusar da
bidi'ah, su lazimci
gaskiya cikin dukkan
lamari, su yaki karya
cikin dukkan kome, lalle
wannan alheri ne babba.
Idan wani ya ce: ai irin
wannan aiki yana
jawowa mai yin shi
wahalhalu da yawa:
wani lokaci ya kan zama
sanadiyyar mutuwarsa,
ko dukansa, ko zaginsa,
ko cin mutuncinsa, ko
rasa wani hakki nasa da
ya kamata ya samu,
saboda haka abin da ya
fi shi ne kowa ya kame
bakinsa, domin samun
lafiyar jikinsa, da
mutuncinsa. To sai a ba
shi amsa da cewa: Ai
malamai magada suke
ga Annabawa, su kuwa
Annabawa ba gadon
kudi suka bari ba, a'a
gadon ilmin sanin
gaskiya ne da kuma aiki
da gaskiyar ko ana ha-
maza-ha-mata. Wannan
shi ne ma ya sa wasu
daga cikinsu suka rasa
rayukansu, wasu kuwa
aka dudduke su, wasu
kuwa aka zazzage su,
wasu kuwa aka cicci
mutuncinsu tamhanyoyi
daban daban.
Misali: babu irin cin
mutuncin da ba a yi wa
Annabi Muhammad mai
tsira da amincin Allah
ba, an yayyake shi, an
masa raunuka daban-
daban, an masa
jamhuru an ce shi
tababbe ne mahaukaci,
an ce mai raba kan
jama'a ne, mai kawo
hargitsi cikin al'umma ne
…..,,
Babban malamin Sunnah
masanin Hadithi, da
Tafsiri, da Tarihi, da
Sirah, Ibnu Katheer ya
ce cikin littafinsa
Albidayatu wannihayah
3/55-56:-
((ﻋﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﺒﻴﺮ
ﻭﻋﻜﺮﻣﺔ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ
ﻗﺎﻝ: ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻠﻴﺔ ﻣﻦ ﺍﺷﺮﺍﻑ
ﻗﺮﻳﺶ ﻭﻋﺪﺩ ﺃﺳﻤﺎﺀﻫﻢ ﺑﻌﺪ
ﻏﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﻋﻨﺪ ﻇﻬﺮ
ﺍﻟﻜﻌﺒﺔ، ﻓﻘﺎﻝ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﺒﻌﺾ :
ﺍﺑﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻓﻜﻠﻤﻮﻩ،
ﻭﺧﺎﺻﻤﻮﻩ ﺣﺘﻰ ﺗﻌﺬﺭﻭﺍ
ﻓﻴﻪ، ﻓﺒﻌﺜﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻥ ﺍﺷﺮﺍﻑ
ﻗﻮﻣﻚ ﻗﺪ ﺍﺟﺘﻤﻌﻮﺍ ﻟﻚ
ﻟﻴﻜﻠﻤﻮﻙ، ﻓﺠﺎﺀﻫﻢ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺳﺮﻳﻌﺎ، ﻭﻫﻮ ﻳﻈﻦ ﺍﻧﻪ ﻗﺪ
'ﺑﺪﺍ ﻟﻬﻢ ﻓﻲ ﺃﻣﺮﻩ ﺑﺪﺀ، ﻭﻛﺎﻥ
ﺣﺮﻳﺼﺎ ﻳﺤﺐ ﺭﺷﺪﻫﻢ ﻭﻳﻌﺰ
ﻋﻠﻴﻪ ﻋﻨﺘﻬﻢ، ﺣﺘﻰ ﺟﻠﺲ
ﺍﻟﻴﻬﻢ. ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ: ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻧﺎ
ﻗﺪ ﺑﻌﺜﻨﺎ ﺇﻟﻴﻚ ﻟﻨﻌﺬﺭ ﻓﻴﻚ،
ﻭﺍﻧﺎ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻧﻌﻠﻢ ﺭﺟﻼ ﻣﻦ
ﺍﻟﻌﺮﺏ ﺍﺩﺧﻞ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻪ ﻣﺎ
ﺃﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻣﻚ؛ ﻟﻘﺪ
ﺷﺘﻤﺖ ﺍﻵﺑﺎﺀ ﻭﻋﺒﺖ ﺍﻟﺪﻳﻦ،
ﻭﺳﻔﻬﺖ ﺍﻵﻟﻬﺔ ﻭﻓﺮﻗﺖ
ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ، ﻭﻣﺎ ﺑﻘﻲ ﻣﻦ ﻗﺒﻴﺢ
ﺍﻻ ﻭﻗﺪ ﺟﺌﺘﻪ ﻓﻴﻤﺎ ﺑﻴﻨﻨﺎ
ﻭﺑﻴﻨﻚ ..)).
Ma'ana: ((Daga Sa'id
Daga Jubair da Ikrimah,
daga Dan Abbas ya ce:
Shugabannin
Quraishawa sun hadu a
Dakin Ka'abah, sannan
suka aika wa Annabi
mai tsira da amincin
Allah cewa suna
bukatar zama da shi,
nan-da-nan Annabi mai
tsira da amincin Allah ya
je ya same su saboda
tsammanin da yake yi
na cewa za su
musulunta ne, domin
yana son musu alheri,
kuma ba ya son abin da
zai wahalce su. Da ya zo
ya zauna a inda suke sai
suka ce da shi: Ya
Muhammad! Lalle, mun
aika Maka ne domin mu
yanke uzurinmu gare
ka, wallahi mu ba mu
taba ganin wani mutum
daga cikin Larabawa da
ya kawo musiba cikin
jama'arsa, kamar yadda
ka kawo musiba cikin
jama'arka ba. Hakika ka
zagi iyayenmu, kuma ka
aibanta addininmu,
sannan ka maida
mahankaltanmu
wawaye, ka kuma zagi
allolinmu, ka raba
kawunan jama'armu.
Babu dai wani
mummunan abu da ya
rage wanda ba ka
sanya shi tsakaninmu
ba..)).
Kun ga dai abin mamaki
karara a nan,
Quraishawa dai kafurai
ne masu bautar
gumaka, mashaya giya,
maciya riba, masu
aikata kusan dukkan
nau'i na sabo, amma
kuma su ne suka sa
Annabi a gaba suna
zazzaro masa
wadannan maganganu!!
Suna cewa shi mai raba
kawunan jama'a ne
saboda kawai ya ce da
su su bi Addinin gaskiya,
su kuma lazimci gaskiya
su daina karya, da
hasada, da hikdu, su
daina karban umurnin
kowa matukar dai ya
saba wa umurnin Allah
Madaukakin Sarki.
Wannan ita ce al'adar
karkatattu cikin ko
wane zamani, sawa'un
kafurai ne masu bautar
gumaka, ko kuwa
Yahudawa ne da
Nasara, ko kuwa cikin
jumlar Musulmi ne suke.
A lokacin da Sheik
Muhammad Dan
Abdullwahhab, ya fara
yi wa jama'arsa wa'azin
su daina ayyuka irin na
shirka da bidi'ah, su
tuba su yi riko da
Alkur'ani da Sunnah,
haka da yawa daga cikin
masu mulkinsu, da
malamansu da jahilansu
suka yi caa a kansa,
suka cutar da shi cuta
mai yawa!
A lokacin da Sheik
Uthmanu Dan Fodiyo ya
fara yi wa jama'ar
kasar Hausa wa'azin su
bar ayyuka irin na
shirka, da bidi'ah, su
dawo zuwa ga Alkur'ani
da Sunnah, da yawa
daga cikin sarakuna da
malaman zamaninsa da
jahilan da ke tare da su,
sun yi ta musguna
masa ta hanyoyi daban-
daban.
A lokacin da Sheik
Abubakar Mahmud Gumi
ya fara yin wa'azi kan
barnar da take gudana a
zamaninsa ta bidi'ar
sufaye da abin da ya yi
kama da haka, ya kuma
shiga rubuce-rubuce
domin bayyanar da
gaskiyar lamari cikin
haka, lalle sarakuna, da
malamai, da kuma
jahilan da ke tare da su
sun yi caa a kansa, sun
yi kokarin kashe shi ba
sau daya ba, ba sau
biyu ba, sun yi kokarin
bata masa suna ta
hanyoyi daban daban.
Allah Ya tabbatar da
dugaduganmu a kan
gaskiya da adalci, Ya
kuma raba al'ummarmu
da sharrin azzalumai na
boye da na bayyane.
Ameen.
April 13 at 12:21pm ·

MUNAFUKAI BA SAHABBAI BANE

MUNAFUKAI BA
SAHABBAI BANE
GABATARWA
ﺃﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ
ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻦ ﺑﻪ
ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ
ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ
ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪ
ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ،
ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ،
ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ،
ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪًﺍ ﻋﺒﺪﻩ
ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﺃﻣﺎ ﺑﻌﺪ: ﻓﺈﻥ
ﺃﺻﺪﻑ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ
ﺗﻌﺎﻟﻰ ، ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻬﺪﻱ
ﻫﺪﻱ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﻭﺷﺮ
ﺍﻷﻣﻮﺭ ﻣﺤﺪﺛﺎﺗﻬﻤﺎ، ﻭﻛﻞ
ﻣﺤﺪﺛﺔ ﺑﺪﻋﺔ، ﻭﻛﻞ ﺑﺪﻋﺔ
ﺿﻼﻟﺔ، ﻭﻛﻞ ﺿﻼﻟﺔ ﻓﻲ
ﺍﻟﻨﺎﺭ .
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺻﻞ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ
ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﻛﻤﺎ
ﺻﻠﻴﺖ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ
ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻓﻲ
ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﺇﻧﻚ ﺣﻤﻴﺪ
ﻣﺠﻴﺪ، ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ
ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﻛﻤﺎ
ﺑﺎﺭﻛﺖ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ
ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ
ﻓﻲ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﺇﻧﻚ ﺣﻤﻴﺪ
ﻣﺠﻴﺪ .
Bayan haka; nazabi
nayi rubutu ne akan
wannan mas'alar
domin shubuhar da
ake kawowa
al'ummar annabi.
Yawanci idan mu
ahlussunnah mukayi
rubutu gameda
ayoyinda suke
magana akan falalar
sahabbban manzon
Allah SAW gaba
dayansu, sai kaji
masu wata
batacciyar aqida suna
cewa ai ba dukkan
sahabbai ake nufi ba.
tunda ai munafikai
suna ciki, harma
wasu suce maka
yawancin sahabban
duk munafikai ne.
wal'iyazubillah.
Hakan yasaba da
aqida ingantacciya ta
ahlussunnah
walja'ama.
Shiyasa nayi nufin
fito wa na
barrantarda sahabbai
daga cikin wadancan
batattun
(munafukai). Duk
dayake nasan akwai
malamai dasuka
tabayin maganganu
gameda wannan
mas'alar, to amma
nima zanyi nawa
domin idan nayi
kuskure sai
malamaina da
abokanai n su gyara
min, kunga ahaka
ahaka wataran nima
sai nazama malami.
Ina fata Allah yamin
muwafaqa a cikin
rubutuna kuma yasa
nayi domin shi ba
domin na birge ba.
SASHI NA FARKO
Wanene sahabi?
Kalmar sahabi kalma
ce ta larabci wadda
asalinta shine 'sahib'
Ma'anarta biyu ce,
akwai ta yare akwai
ta malaman shari'ah,
Toh dayake rubutuna
yana da alaqa ne da
shari'a zan maida
hankali ne kadai akan
abnd yashafi shari'ah.
Idan akace wannan
sahabin annabi ne to
ana nufin abinda zan
kawo yanzu.
ﺃﻥ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﻲ ﻫﻮ ﻣﻦ ﻟﻘﻲ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﺣﻴﺎﺗﻪ ﻣﺆﻣﻨﺎً
ﺑﻪ ﻭﻣﺎﺕ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﺳﻼﻡ
Ma'ana: hakika sahabi
shine wanda yataba
gamuwa da annabi,
sannan suka shiga
musulunci a lokacin
rayuwarsa, sannan
kuma suka mutu a
cikin musulunci.
Kaga kenan fadin
cewa wanda ya taba
gamuwa da annabi
hakan yashigar da
makafi aciki.
Fadin cewa wanda ya
musulunta alokacin
rayuwar annabi
yafitar da wanda ya
musulunta bayan
wafatin manzon
Allah SAW.
Fadin cewa wanda ya
mutu a musulunci ya
fitarda wanda yayi
ridda kafin ya mutu.
kaga kenan sai
mutum ya cika
wadannan sharudda
kafin yasmi matsayi
da kirarin sahabi.
SASHI NA BIYU
Suwanene
munafukai???
munafukai sune
wadanda suke boye
kafurci kuma suke
bayyana musulunci.
fadin cewa suna
boye kafirci yana
nufin cewa kafiran
ne.
fadin cewa suna
bayyana musulunci
yana nuna cewa
karya sukeyi ba
musulman bane.
wani zaice menene
dalilin fadin haka?
sai ince nafadi hakan
ne bisa karkashin
fadin ubangiji acikin
suratu baqara.
Allah yace:
ﻭَﻣِﻦَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﻣَﻦْ ﻳَﻘُﻮﻝُ
ﺁﻣَﻨَّﺎ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺑِﺎﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ
ﻭَﻣَﺎ ﻫُﻢْ ﺑِﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ
ma'ana: alah yace
daga cikin mutane
akwai wadanda suke
cewa sunyi imani da
allah da ranar lahira,
amma su din ba
masu imani bane.
sannan awata ayar
allah yace:
ﻭَﺇِﺫَﺍ ﻟَﻘُﻮﺍ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ
ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺁﻣَﻨَّﺎ ﻭَﺇِﺫَﺍ ﺧَﻠَﻮْﺍ ﺇِﻟَﻰ
ﺷَﻴَﺎﻃِﻴﻨِﻬِﻢْ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺇِﻧَّﺎ
ﻣَﻌَﻜُﻢْ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻧَﺤْﻦُ
ﻣُﺴْﺘَﻬْﺰِﺋُﻮﻥَ
ma'ana: allah yace (su
wadannan mutanen)
idan suka gamuda
wadanda sukayi
imani sai suce ai
suma sunyi imani,
idan kuma suka
koma wajen
shaidanunsu sai suce
ai muma muna tare
daku, ai kawai
munayiwa wadancan
izgili ne.
idan ka kula zakaga
da allah yazo kan
masu imani ai bai
jinginasu da
munafikai ba, amma
dayazo kan
shaidanun sai ya
jinginasu da
munafukan.
sannan awata ayar
allah yace:
ﺇِﺫَﺍ ﺟَﺎﺀَﻙَ ﺍﻟْﻤُﻨَﺎﻓِﻘُﻮﻥَ
ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﻧَﺸْﻬَﺪُ ﺇِﻧَّﻚَ ﻟَﺮَﺳُﻮﻝُ
ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻳَﻌْﻠَﻢُ ﺇِﻧَّﻚَ
ﻟَﺮَﺳُﻮﻟُﻪُ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻳَﺸْﻬَﺪُ ﺇِﻥَّ
ﺍﻟْﻤُﻨَﺎﻓِﻘِﻴﻦَ ﻟَﻜَﺎﺫِﺑُﻮﻥَ
ma'ana: allah yace:
idan munafukai
sukazo maka suna
cemaka suna cewa
sun shaida kai
manzon allah ne, ai
dama allah yasan kai
manzonsa ne,
sannan kuma allah
yana shaidawa cewa
munafukai karya
sukeyi (basu yarda
kai manzon allah
bane).
idan muka dubi
sakamakon da
wadannan ayoyi suke
bamu zamuga cewa
su munafikai kawai
suna fadan musulunci
ne abaki amma sam-
sam babu shi acikin
zuciyoyinsu.
wani zai iya cewa ai
sun hada ne tsakanin
musuluncin da
kafircin.
sai muce masa ai
ba'a hada musulunci
da kowane addini.
idan kuwa mutum
yahada musulunci da
wani addini to kawai
yazama dan wancan
addinin kuma baya
cikin musulunci.
allah yace:
ﻭَﻣَﻦْ ﻳَﺒْﺘَﻎِ ﻏَﻴْﺮَ ﺍﻟْﺈِﺳْﻠَﺎﻡِ
ﺩِﻳﻨًﺎ ﻓَﻠَﻦْ ﻳُﻘْﺒَﻞَ ﻣِﻨْﻪُ ﻭَﻫُﻮَ
ﻓِﻲ ﺍﻟْﺂﺧِﺮَﺓِ ﻣِﻦَ
ﺍﻟْﺨَﺎﺳِﺮِﻳﻦَ
ma'ana: duk wanda
yanemi wani addini
wanda ba musulunci
ba to baza'a amsa
daga gareshi ba,
kuma a ranar lahira
yana cikin tababbu.
SASHI NA UKU
menene yahana
munafukai shiga jerin
sahabbai?
ian baka manta ba
abaya mun kawo
maka sharuddan da
mutun zai cika kafi
yazama sahabi.
sannan kuma kaamar
yadda muka fada
shsruddan guda uku
ne.
idan har jka tuna
wannan kuma
kahada da ma'anar
da aka bayar gameda
munafukai zaka gano
cewa ba sahabbai
bane.
kankawo abin a
rarrabe domin a
fahimce shi dalla
dalla.
kamar yadda aka
fada cewa sharadi na
farko na zama sahabi
shine gamuwa da
annabi.
ko shakka babu cewa
munafukai sun cika
wannan sharadin na
farko saboda sun
rayu lokaci daya da
annabi.
to sun cika sharadi
daya saura biyu.
sannan sharadi na
biyu shine dole
yazamanto mutum
musulmi ne lokacinda
yagamuda annabin.
to a karkashin
wannan maganar
zamuga babu su aciki
, saboda su ai basuyi
imanin ba. ayoyi da
yawa sun nuna cewa
munafukai kafirai ne
ba musulmi ba. kaga
kuwa babu tayadda
za'ayi kafiri yazama
sahabin annabi indai a
ma'anarta ta shari'ah
ne. amma in a
ma'anar yare ne
wannan zasu iya
zama. mukuwa muna
magana ne akan
shari'ah ba yare ba.
domin annabinmu ba
yare yazo koya mana
ba, shari'ah yazo
koya mana.
wani zaice menene
dalili akan cewa
munafukai kafirai ne?
kaduba ayoyin da
nakawo abaya
dakuma wadanda
amkawo anan gaba
kadan inshaallah, idan
kahadasu zaka gano
cewa kafirai ne. ga
ayoyin kkamar haka:-
allah yace:
ﻭَﻣَﺎ ﻣَﻨَﻌَﻬُﻢْ ﺃَﻥْ ﺗُﻘْﺒَﻞَ
ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﻧَﻔَﻘَﺎﺗُﻬُﻢْ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧَّﻬُﻢْ
ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺑِﺮَﺳُﻮﻟِﻪِ
ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺄْﺗُﻮﻥَ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﺇِﻟَّﺎ
ﻭَﻫُﻢْ ﻛُﺴَﺎﻟَﻰ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﻨْﻔِﻘُﻮﻥَ
ﺇِﻟَّﺎ ﻭَﻫُﻢْ ﻛَﺎﺭِﻫُﻮﻥَ
ma'ana: allah yace:
babu abinda yahana a
amshi sadakarsu sai
don kawai sun
kafircewa allah da
manzonsa, sannan
basu zuwa sannan
sai a kasalance (ba
ason ransu ba)
sannan basu bada
sadaka sai ransu
yana ki.
wannan ayar tanuna
cewa kafirai ne,
dama ai si arne duk
ainda zaiyi koda mai
kyau ne to bashi da
lada awajen allah
awata ayar kuma
allah yace:-
ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺼَﻞِّ ﻋَﻠَﻰ ﺃَﺣَﺪٍ ﻣِﻨْﻬُﻢْ
ﻣَﺎﺕَ ﺃَﺑَﺪًﺍ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻘُﻢْ ﻋَﻠَﻰ
ﻗَﺒْﺮِﻩِ ﺇِﻧَّﻬُﻢْ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ
ﻭَﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﻣَﺎﺗُﻮﺍ ﻭَﻫُﻢْ
ﻓَﺎﺳِﻘُﻮﻥَ
ma'ana: daga yanzu
kadena yin sallah(ta
gawa) akan duk
wanda yamutu daga
cikinsu (munafukai)
kuma kadena
tsayawa kana
addu'ah akan
qabarinsu. hakika su
sun kafircewa allah
kuma sun mutu suna
fasikai.
itama wannar ayar
takara nuna mana
cewa kafirai ne.
awata ayar daban
kuma allah yace:
ﻭَﻟَﺎ ﺗُﻌْﺠِﺒْﻚَ ﺃَﻣْﻮَﺍﻟُﻬُﻢْ
ﻭَﺃَﻭْﻟَﺎﺩُﻫُﻢْ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ
ﺃَﻥْ ﻳُﻌَﺬِّﺑَﻬُﻢْ ﺑِﻬَﺎ ﻓِﻲ ﺍﻟﺪُّﻧْﻴَﺎ
ﻭَﺗَﺰْﻫَﻖَ ﺃَﻧْﻔُﺴُﻬُﻢْ ﻭَﻫُﻢْ
ﻛَﺎﻓِﺮُﻭﻥَ
ma'ana: allah yacewa
annabi; kada
dukiyoyinsu da
yayayensu su baka
mamaki ko su
birgeka, allah yanaso
ya azabtar dasu ne
dasu a duniya kuma
ransu yana fita ne
alhalin suna kafirai
(kamar yadda ibn
abbas yafassara)
sannan allah yace:-
ﻳَﺤْﺬَﺭُ ﺍﻟْﻤُﻨَﺎﻓِﻘُﻮﻥَ ﺃَﻥْ
ﺗُﻨَﺰَّﻝَ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢْ ﺳُﻮﺭَﺓٌ
ﺗُﻨَﺒِّﺌُﻬُﻢْ ﺑِﻤَﺎ ﻓِﻲ ﻗُﻠُﻮﺑِﻬِﻢْ
ﻗُﻞِ ﺍﺳْﺘَﻬْﺰِﺋُﻮﺍ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ
ﻣُﺨْﺮِﺝٌ ﻣَﺎ ﺗَﺤْﺬَﺭُﻭﻥَ
ma'ana: munafukai
suna tsoron kada
asaukarda ayarda
zata bayyana abinda
yake cikin
zuciyoyinsu. yakai
annabi kace musu
sucigaba da yin izgili
watarn allah zai
baiyana abinda suke
tsoro.
sannan allah yace:-
ﻭَﺃَﻣَّﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻓِﻲ ﻗُﻠُﻮﺑِﻬِﻢْ
ﻣَﺮَﺽٌ ﻓَﺰَﺍﺩَﺗْﻬُﻢْ ﺭِﺟْﺴًﺎ
ﺇِﻟَﻰ ﺭِﺟْﺴِﻬِﻢْ ﻭَﻣَﺎﺗُﻮﺍ
ﻭَﻫُﻢْ ﻛَﺎﻓِﺮُﻭﻥ
ma'ana:ammasu
wadanda suke da
rashin lafiya a
zuciyarsu
(munafukai) idann
aya gtasauka sai
takara musu datti
akan dattinda
zuciyarsu take dashi
kuma sun mutu suna
kafirai.
allah yace:-
ﻳَﺤْﻠِﻔُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻣَﺎ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ
ﻭَﻟَﻘَﺪْ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﻛَﻠِﻤَﺔَ ﺍﻟْﻜُﻔْﺮِ
ﻭَﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﺑَﻌْﺪَ ﺇِﺳْﻠَﺎﻣِﻬِﻢْ
ﻭَﻫَﻤُّﻮﺍ ﺑِﻤَﺎ ﻟَﻢْ ﻳَﻨَﺎﻟُﻮﺍ
ma'ana(wata rana
wani munafuki yana
gida tareda dansa sai
yafadi munnunar
magana gameda
anabi, sa yaron yaje
yafadawa annabi, da
aka kirawo mutumin
domin kare kansa sai
ya rantse akan bai
fada ba), sai allah
yasaukarda aya yace:
munafunafukai suna
rantsuwa wai basu
fadi abinda akace sun
fada ba. amma karya
ne hakika sun fadi
kalmar kafirci (domin
yiwa allah da
manzonsa izgili kafirci
ne) kuma sun kafirta
bayan imaninsu.
kuma hakika suna
burin abinda bazasu
samuna (na
kyakkyawan rabo a
lahira). amma kamar
yadda ya tabbata
cewa mutumin ya
musulunta daga
baya.
sannan allah yace:
ﺍﺳْﺘَﻐْﻔِﺮْ ﻟَﻬُﻢْ ﺃَﻭْ ﻟَﺎ
ﺗَﺴْﺘَﻐْﻔِﺮْ ﻟَﻬُﻢْ ﺇِﻥْ
ﺗَﺴْﺘَﻐْﻔِﺮْ ﻟَﻬُﻢْ ﺳَﺒْﻌِﻴﻦَ
ﻣَﺮَّﺓً ﻓَﻠَﻦْ ﻳَﻐْﻔِﺮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻟَﻬُﻢْ
ﺫَﻟِﻚَ ﺑِﺄَﻧَّﻬُﻢْ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ
ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻟَﺎ
ﻳَﻬْﺪِﻱ ﺍﻟْﻘَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻔَﺎﺳِﻘِﻴﻦَ
ma'ana: allah yana
gayawa manzonsa
yace: ko kanema
musu gafara ko
karka nema musu
gafara, koda zaka
nema musu gafara
sau saba'in allah
bazai gafarta musu
ba. hakan kuwa zai
farune saboda sun
kafircewa allah da
manzonsa.
ayoyin suna da yawa
amma anan zan
tsaya da kawo su.
idan baka manta ba
muna magana ne
acikin sharadi ba biyu
na zama sahabi.
kaga kenan koda sun
cika sharadi na farko
to basu cika na biyu
ba.
ammafa idan
munafiki yatuba a
lokacin annabi kuma
har ya mutu acikin
musulunci to yazama
sahabi.
saikuma sharadi na
uku.
sharadi na uku shine
dole sai mutum
yamutiu a musulunci.
ayoyinda nakawo
abaya kuwa sun
tabbatar mana da
cewa munafukai
basu mutu a
musulunci ba.
sannan koda mutum
yagamuda annabi
kuma yayi imani
dashi a lokacin
rayuwarsa amma
kuma sai yai ridda
kuma har ya mutu
ahaka to ba sahabi
bane, idan kuma
yatuba bayan riddar
kuma yariga yacika
wadancan sharudan
guda biyu to sahabi
ne.
anan zan takaita
wannan rubutun
nawa. fatana shine
allah yasa sakon ya
isa inda ake bukata.
kamar kullum ina nan
ina jiran gyara,
tambaya ko shawara
gameda wannan
rubutun dama sauran
rubututtuka na.
wassalamu alaikum
warahmatullah.
AWAISU HARUNA
MUHAMMAD
AL'ARABEE FAGGE

Sifiyanu Bawa Gwandu, Hudubar jumua’a Daga Masallacin JIBWIS dake Gwandu L/G kebbi state.

Sifiyanu Bawa
Gwandu
Hudubar jumua'a ta yau
Daga Masallacin JIBWIS
dake Gwandu L/G kebbi
state.
Tare Da: imam
Muhammad yabani
Gwandu jihar kebbi.
(1)Imam Muhammad
yabani Yafara hudubar
sa ne yayi magana akan
yadda sahabbai suke
Son Annabi da kuma
kaunar annabi kuma
yayi magana akan yan
shi'a masu zagin
sahabbai
(2)imam yayi bayani
akan mauduin hadin kai
a musulunci yayi
kwakwaran bayani
akan cewa kowace
Al,umma tana samon
cigaba ne ta hanyar
hadin kai bata hassada
da kiyayya da juna ba
kuma yakara kira ga
masu mulki suyi tafiya
a bai daya domin
susamu cigaba da
nasarori akan al,umma
baki daya
(3)imam daga karshe
yajanyo Al,umma cewa
musani wannan duniya
ba gidan zama bace Mu
mayarda hankalinmu
wajen ibada da
taimakawa iyayenmu
musani cewa duniyar
nan zamu barta komai
Daren dadewa, Allah
yayi muna jagora Allah
ya taimake musulunci
da musulmi
yakaskantarda kafirci
ga kafirai imam yarufe
yana cewa, Lallai Allah
da malaikunsa suna yin
salati ga Annanbi yaku
wadanda sukayi imani
kuyi salati a garesa
wasallimu taslima
Sifiyanu Bawa Gwandu
Jibwis Nigeria social
media
Gwandu L/G kebbi state
chapter
(26 Rabiul Auwal
1437Ah)(8/1/2016)