ZAN IYA AURAN WACCE NA YI ZAMAN DADIRO DA ITA ?

ZAN IYA AURAN WACCE NA YI ZAMAN
DADIRO DA ITA ?
Tambaya:
As SALAMUN alaikum , Malamai ya
halarta musulmi ya musuluntar da matar
da yayi zaman daduro da ita bayan hakan ya aure ta , limanmin da ya goyi
bayan hakan yayi daide? Please is very
important”
Amsa:
Wa alaikum as salam, ya halatta sabida
babu alaka tsakanin dadironsu da auransu bayan ta musulunta Mutukar sun
tuba, saboda musulunci yana rusa abin
da ya gabace shi na zunubi kamar yadda
ya tabbata a hadisin Amru bn Al’ass.
Idan musulmi ya yi zina ya tuba, to Allah
yana gafarta dükkan zunuban da suke hakkinsa ne, kamar yadda aya ta:53 a
suratu Zumar ta tabbatar hakan
Allah ne mafi Sani.
Dr. Jamilu Zarewa
1\2\2016.

Advertisements

*HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA*

*HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum Don Allah malam a
taimaka min da bayani game da sababin
da yasa ake yin azumi??
*Amsa:* Wa alaikum assalam Azumi ginshiki ne,
daga cikin turakun musulunci, wadanda
addinin musulunci, ba zai cika ba sai da
su, Allah da manzonsa sun yi umarni da
shi, saboda wasu muhimman manufofi,
ga wasu daga ciki : *1.* Samun tsoron Allah, saboda mai
azumi yana barin abin da yake so saboda
Allah, hakan zai sa, ya kara samun tsoron
Allah.
*2.* Samun kariya daga Shaidan, saboda
azumi yana takure hanyoyin Shaidan, wannan ya sa zunubai suke karanci a
Ramadan.
*3.* Tuna talakawa da wahalar da suke
ciki, saboda duk lokacin da mai kudi ya
dandana yunwa zai tuna halin da
talakawa suke ciki . *4.* Sabawa rai wajen barin abin da take
so, da kuma hakuri akan abin da take
sha’awa.
*5.* Kankare zunubai da kuma samun
daukakar daraja, saboda azumi yana
gyara zuciya, da kuma rai. *6.* Samun lafiyar jiki, saboda azumi
yana kariya daga cututtuka masu yawa,
kamar yadda likitoci suka tabbatar da
hakan.
*7.* Ta hanyar azumi mutum zai saba da
yin aikin don Allah, saboda azumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.
Allah ne mafi sani *Amsawa* *DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
29/1/2013

*SAHABI, DAN SAHABI, JIKAN SAHABI, BABAN SAHABI ! ! !*

*SAHABI, DAN SAHABI, JIKAN SAHABI,
BABAN SAHABI ! ! !* *Tambaya*
Assalamu alaikum, don Allah akwai
sahabin da kakansa sahabi ne, babansa
sahabi, dansa kuma sahabi ?, ina son
karin bayani malam ?
*Amsa* Wa alaikum salam.
To malam sahabin da yake kakansa
sahabi, dansa sahabi, babansa sahabi,
shi ne : Abdurrahman dan Abi-bakr bn Abi
Khuhafah kamar yadda Ibnu Salah da
Ibnul-jauzy suka ambata. Saboda mahaifinsa Abubakar sahabi ne, hakanan
kakansa Abu khuhafah shi ma sahabi ne
sannan dansa Muhammad sahabi ne,
Ibnu Hajar yana cewa : Ba mu san
mutum hudu da ‘ya’yansu wadanda suka
ga Annabi s.a.w ba sai wadannan. Abin da yake nufi shi ne : Muhammad da
mahaifinsa Abdurrahman da kakansa
Abubakar da kakansa na biyu Abu-
kuhafah dukkansu sun ga Annabi s.a.w.
don haka su kadai suka samu wannan
darajar, Allah ya kara musu yarda . Don neman karin bayani duba tarjamar
Muhammad Bn Abdurrahman Bn Abi-bakr
Bn Abi-khuhafah a Usudul-gabah a
lamba ta : 6083.
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
31/1/2015

*SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI ?*

*SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN
ALBASHI ?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum
Malam yaya zakkar ma’aikaci ya kamata
ta zamo? Domin wasu ma’aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa
zakkah to amma wasu sukanyi gini ko
sayen filaye ko gonaki da kudin kafin
shekara ta zagayo sun kare
*Amsa*
Waalaikumussalam To dan’uwa, hukuncin wannan albashi
zai fara ne daga lokacin da ya shiga
mulkinsa, don haka mutukar ba su
shekara ba, to babu zakka a ciki, domin
ba kawai samun nisabI ne ya ke wajabta
zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka
shiga mulkinsa, don haka duk albashin
da ya kai nisabin zakka, kuma aka ajjiye
shi ya shekara to ya wajaba a fitar masa
da zakka, amma mutukar shekara ba ta
zagayo masa ba, to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi.
saidai yana daga cikin dabarun da sharia
ta haramta, mutum ya yi abin da zai
sarayar masa da wajibi da gangan, don
haka mutukar ya sayi filayan ne da nufin
kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa Allah.
Allah ne ma fi sani
*Dr. Jameel Zarewa*
13/3/2014

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

YADDA AKE WARWARE
SIHIRI Tambaya :Assalamu
alaikum Dan Allah malam a fitar
dani cikin duhu game da abin da yake
damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin
malami ai mata naganin ciwon mara dz yake
damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma
likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai
malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai
yi mata magani nan take ta haife abinda yake
cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai,
sai take min magana in kawo kudi a sayi
tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya
malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne
shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin
wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan
bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin
biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina
da matsala , ta bangaren aqeeda mun
banbanta? Wassalam na gode malam Allah ya qara
basira. Amsa : To ‘yar’uwa tabbas ba a warware
sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware
sihiri ta hanyar ayoyin Alqur’ani, wasu malaman
sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta
hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da
Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa
ta 122, na suratul A’araf, sai kuma aya ta :
79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da
aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za’a karanta su,
sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya
guda bakwai, sannan ayi wanka da shi .
Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada
wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba’a
yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah. Ya
wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki
sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi yana cewa :” “Duk wanda ya
je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah
ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba’in”
kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai
lamba ta : 2230. Kin ga in mutum ya mutu a
wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma
tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita,
a wani hadisin kuma yana cewa : “Duk wanda
ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to
tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya
zo da shi” kamar yadda ya zo a Sunanu-
abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904, kuma Albani
ya inganta shi . INA GANIN DA IRIN
WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO
KAN HANYA. Allah ne mafi sani . DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN AUREN HANNU (Masturbation) ? DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN AUREN HANNU
(Masturbation) ?Tambaya:
Assalmu alaikum, Allah ya kara
ma malam lapiya da imani, malam
dan Allah menene hukumci masturbation
(Istimna’i) a musulunci Amsa: Wa alaikum
assalam,To ‘yar’uwa Babu nassi ingantacce
bayyananne yankakke da yake haramta
wasa da al’aura har maniyyi ya fito, saidai wasu
malaman sun haramta auran hannu saboda
aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan
bukatar sha’awa ta hanyar matar aure ko bayi
kawai, wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba
ba’a iya biyan bukata ta hanyar su. Yin wasa
da al’aura har maniyyi ya fita yana haddasa
matsaloli a likitance, saidai yana daga cikin
ka’idojin shari’a ; idan cututtuka biyu suka hadu
ya zama babu yadda za’a yi sai an aikata daya
daga ciki sai a zabi karama a aikata, wannan
yasa Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka
halatta auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma
ba shi da halin da zai yi aure. Idan mu ka ce
auran hannu haramun ne, saidai barnar dake
cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta
alfarma a ciki, sannan tana kaiwa ga
cakuduwar nasaba, ta yadda za’a haifi ‘ya’ya gantalallu,
marasa asali, wannan ya sa magana ta biyu ita
ce mafi inganci, mutukar an samu
sharudan da suka gabata . Don neman Karin
bayani duba : Muhallah 12\407 da Majmu’ul
fataawaa 34\146> Allah ne mafi sani.

MACE ZA TA IYA BAWA MIJINTA ZAKKA ? DR. JAMILU ZAREWA

*MACE ZA TA IYA BAWA
MIJINTA ZAKKA ?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum. Malam
Menene sahihi akan mace
tabawa mijnta zakkah ? *Amsa* Wa alaikum assalam,
ya halatta a zancen mafi yawan
malamai saboda hadisin Zainab
matar Abdullahi Dan Mas’ud
wanda Bukhari ya rawaito a
sahihinsa a lamba ta:(1462) da kuma Muslim a hadisi mai lamba
ta: (1000) lokacin da ta nemi
fatwa akan bawa mijinta sadaka
kuma Annabi S A W. ya halatta
mata hakan. Malaman sun kafa hujja da
wannan hadisin saboda kalmar
sadaka ta kunshi farilla da sunna
. Aya ta (60) a suratu Attaubah ta
yi bayanin nau’o’i takwas na
mutanen da ake bawa zakka,
daga ciki akwai talaka, hakan sai
ya nuna mutukar miji talaka ne
matarsa za ta iya ba shi zakka, tun da ba’a samu dalilin da ya
fitar da shi ba.
Saidai Ibnul Munzir ya hakaito
ijma’i cewa: “Bai halatta miji ya
bawa matarsa zakka ba idan
tana fama da talauci, tun da zai iya wadatata ta hanyar ciyarwar
da Allah ya wajabta masa.
Don neman karin bayani duba:
Sharhul Mumti’i (6/168) da kuma
Fataawa Allajnah Adda’imah
(10/62) Allah ne mafi sani.
*Dr, Jamilu Zarewa*
21/11 /2017