002 Suratul Baqarah

(Sura 2) 1 A. L̃. M̃. 2 Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a
cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.(1) 3 Waɗanda suke yin ĩmãni game da
gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma
daga abin da Muka azurta su suna
ciyarwa. 4 Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da
abin da aka saukar zuwa gare ka, da
abin da aka saukar daga gabãninka,
kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni. 5 Waɗannan suna kan shiriya, daga
Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne
mãsu cin nasara. 6 Lalle ne waɗanda suka kãfirta(1)
daidai ne a kansu, shin kã yi musu
gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba
zã su yi ĩmãni ba. 7 Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu,
da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su
akwai wata yãna; kuma suna da wata
azãba mai girma. 8 Kuma akwai daga mutãne wanda(2)
yake cewa: “Mun yi imani da Allah
kuma da Yinin Lãhira.” Alhãli kuwa su
ba muminai ba ne. 9 Suna yaudarayya da Allah da
waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli bã su
yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su
sakankancħwa! 10 A cikin zukãtansu akwai wata cũta.
Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma
suna da azãba mai raɗaɗi sabõda abin
da suka kasance suna yi na ƙarya. 11 Kuma idan aka ce musu: “Kada ku yi
ɓarna a cikin ƙasa,” sukan ce: “Mũ mãsu
kyautatawa kawai ne!” 12 To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna,
kuma amma bã su sansancewa. 13 Kuma idan aka ce musu: “ku yi
ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi
ĩmãni,” sukan ce: “Zã mu yi ĩmãni ne
kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?”
To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma
amma bã su sani. 14 Kuma idan sun haɗu da waɗanda
suka yi ĩmãni,sukan ce: “Mun yi ĩmãni.
“Kuma idan sun wõfinta zuwa ga
shaiɗãnunsu,(3) sukan ce: “Lalle ne
muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai
ne.” 15 Allah Yana yin izgili(4) gare su kuma
Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna
ɗimuwa. 16 Waɗannan su ne waɗanda suka
sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai
yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu
shiryuwa ba. 17 Misãlinsu(1) shĩ ne kamar misãlin
wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta
haskake abin da yake għfensa (na abin
tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma
Ya bar su a cikin duffai, bã su gani. 18 Kurãme, bħbãye, makãfi, sabõda
haka bã su kõmõwa. 19 Ko kuwa kamar girgije mai zuba(2)
daga sama, a cikinsa akwai duffai da
tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar
yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga
tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa.
Kuma Allah Mai kħwayewa ne gã kãfirai! 20 Walƙiyar tana yin kusa ta fizge
gannansu, ko da yaushe ta haskakã
musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma
idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye.
Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da
jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne. 21 Yã ku mutãne! Ku bauta(3) wa
Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ
da waɗanda suke daga gabãninku,
tsammãninku ku kãre kanku ! 22 Wanda Ya sanya muku ƙasa
shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya
saukar da ruwa daga sama, sa´an nan
Ya fitar da abinci daga ´ya´yan itãce
game da shi, sabõda ku. Sabõda haka
kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane. 23 Kuma idan kun kasance a cikin
shakka daga abin da Muka sassaukar
ga Bãwanmu, to, ku zõ da sũra guda
daga misalinsa (Alƙur´ãni). Kuma ku
kirãwo shaidunku (4) baicin Allah, idan
kun kasance mãsu gaskiya. 24 To, idan ba ku aikata (kãwo sura)
ba, to, bã zã ku aikata ba, sabõda
haka, ku ji tsoron wuta, wadda
makãmashinta mutãne da duwãtsu ne,
an yi tattalinta dõmin kãfirai. 25 Kuma ka bãyar da bishãra ga
waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka
aikata ayyuka na ƙwarai, cħwa lallene,
suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na
gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da
yaushe aka azurta su da abinci daga wasu ´ya´yan itãce daga gare su,(1)
sai su ce: “Wannan shi ne aka azurta
mu da shi daga gabãnin haka,” Kuma a
je musu da shi yana mai kama da juna,
Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure
mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne. 26 Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya
bayyana wani misãli, kõwane iri ne,
sauro da abin da yake bisa gare shi.
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai
su san cewa lalle shi ne gaskiya daga
Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: “Mħne ne Allah
Ya yi nufi da wannan(2) ya zama
misãli?” na ɓatar da wasu mãsu yawa
da shi, kuma Yana shiryar da wasu
mãsu yawa da shi, kuma bã Ya ɓatarwa
da shi fãce fasiƙai. 27 Waɗanda suke warware alƙawarin
Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su
yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi
a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa,
waɗannan sũ ne mãsu hasãra. 28 Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli
kuwa kun kasance matattu sa´an nan
Ya rãyar da ku, sa´nnan kuma Ya
matar da ku, sa´an nan kuma Ya rãya
ku, sa´an nan zuwa gare Shi ake mayar
da ku? 29 Shi ne Wanda Ya halitta muku abin
da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa´an
nan kuma Ya daidaita(3) zuwa sama,
sa´an nan Ya aikata su sammai
bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai
Masani ne. 30 Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya
ce ga malã´iku: “Lalle ne, Ni Mai sanya
wani halĩfa ne a cikin ƙasa,” suka ce:
“Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai
yi ɓarna a cikinta, kuma ya zubar da
jinainai alhali kuwa mu, muna yi maka tasbihi game da gõde maka, kuma(1)
muna tsarkakewa gareka” Ya ce: “Lalle
ne, Ni

001 Suratul Fatiha

1 Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
2 Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu/talikai;
3 Mai/mafi rahama, Mai/mafi jin ƙai;
4 Mai nuna Mulkin/Mamallakin Rãnar Sakamako.
5 Kai (kaɗai) muke bautawa, kuma Kai (kaɗai) muke neman taimakonKa.
6 Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
7 Hanyar waɗanda Ka yi wa ni’ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.