Category Archives: HUDUBAH

Illar cin mutuncin mutane (2) @aminiyya

Illar cin mutuncin
mutane (2)
Category: Mumbarin
musulunci Published on
Friday, 11 December
2015 15:13 Written by
Hudubar Sheikh
Abdurrahma As-Sudais,
Babban Limamin
Masallacin Ka’aba Hits:
135
Ku sani -Allah Ya
kubutar da ni da ku –
lallai ukubar cin mutunci
tana da muni da gaunin
da take girgiza farillai,
masu hankali ke tsoro
daga gare ta. An karbo
daga Anas bin Malik
(RA) cewa: “Lallai
Annabi (SAW) ya ce:
“Lokacin da aka yi
mi’iraji da ni, na wuce ta
wurin wadansu mutane
suna da farata na bakin
karfe, suna yayyage
fuskokinsu da
kirazansu. Sai na ce: “Su
wane ne wadannan ya
Jibrilu?” Sai ya ce:
“Wadannan su ne masu
cin naman mutane,
suna cin mutuncinsu.”
Abu Dawuda ya ruwaito
a Sunnan dinsa.
Al’ummar Musulmi!
Gaskiya hakki ne a kan
kowane Musulmi da
Musulma idan ya ji ana
cin mutuncin wani dan
uwansa ya ja
hankalinsa (mai cin
mutuncin), ya kwabe
shi, ya shiryar da shi, ya
yi masa nasiha, ya hana
shi. Ya kama hannunsa
cikin kyautatawa ya
shiryar da shi ya
gargade shi kan aiki da
jita-jita da karya da
suke jawowa a fada ga
hallaka da yaduwar
hassada. Cin mutuncin
wadansu bai haifar da
komai sai hallaka da
barna. Manzon Allah
(SAW) yana cewa:
“Wanda ya ci mutuncin
dan uwansa za a yi
masa suturar wuta (a
Lahira).” Ibn Abu Shaiba
ya ruwaito shi a cikin
Musnaf dinsa.
Ya jama’ar Musulmi!
Domin a kubutar da
jama’a daga illar
wadannan mutane,
babu makawa a kame
hannuwansu da rusa
manufofinsu da
dabbaka hukunce-
hukuncen shari’a a
kansu, har ya zamo
mutuncin mutane bai
zama wata iyaka abar
halattawa ga kowane
jaki da doki ba, bai zamo
abin ketawa da takewa
ga kowane wawa da
gailo ba.
Ta hanyar yin haka ne
za mu gina wa kanmu
da al’ummarmu tushen
zaman lafiya na
gaskiya, soyayya da
kauna su samu wurin
zama a tsakaninmu,
kyawawan dabi’u da
’yan uwantaka su ginu,
kuma cikin izinin Allah
mu kawar da kyamar
juna da cutarwa, a
samu al’umma mai
inganci, mai makoma
tagari da zukata masu
tsarki da salama da
jama’a mai karfin
gwiwa da azama.
Domin dunkulewar
al’umma yana tare ne
da dinkewar daidaikun
jama’arta, dinkewar
daidaikun jama’arta
yana damfare ne da
haduwar zukatansu da
daukakar himmarsu da
martabarsu da
salamarsu da hadin
kansu.
Wannan shi ne abin
fata, wannan ake son
gani, kuma muna fatar
samun taufiki na
gaskiya da aiki na ikhlasi
daga Allah.
Ina neman tsarin Allah
daga Shaidan jefaffe.
“Ya ku wadanda suka yi
imani! Ku nisanci abu
mai yawa na zato. Lallai
sashin zato laifi ne.
Kuma kada ku yi rahoto
(leken sirri), kuma kada
sashinku ya yi gibar
sashi. Shin dayanku na
son ya ci naman dan
uwansa yana matacce?
To ku ki shi (cin naman).
Kuma ku bi Allah da
takawa. Lallai Allah Mai
karbar tuba ne, Mai jin
kai.” (k:49:12)
Allah Ya yi mini albarka
da ku a cikin bin
Alkur’ani da Sunnah. Ya
amfanar da mu da abin
da ke cikinsu na ayoyi
da ambato da hikima.
Ina fadin wannan
magana tawa, ina
neman gafarar Allah Mai
girma da daukaka a
gare ni da ku da sauran
Musulmi daga dukkan
kuskure da laifi, ku nemi
gafararSa, ku tuba gare
Shi, lallai ne Shi Mai
yawan gafara ne, Mai jin
kai.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga
Allah majibincin masu
takawa. Kuma na
shaida babu abin
bautawa da gaskiya sai
Allah Shi kadai ba Ya da
abokin tarayya a gare
Shi, kuma na shaida lallai
Annabinmu Muhammad
bawan Allah ne kuma
ManzonSa, abin koyin
masu neman tsarkaka,
Tsira da Amincin Allah
su kara tabbata a gare
shi da alayensa
tsarkaka ma’abuta rabo
da sahabbansa masu
da’a masu tsere wajen
aikin kwarai da
wadanda suka biyo su
da kyautatawa har
zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ya bayin
Allah! Ku bi Allah da
takawa a boye da fili,
ku kiyaye mutuncin
Musulmi da mafifitan
shiriya da sunnoni sai ku
rabauta da mafiya
girman albarkoki da
rahamomi da
kyaututtukan baiwa
daga Allah.
’Yan uwa a cikin imani!
A cikin shiriyar Ubangiji
da manhajar gyara ta
Alkur’ani muna da
magani mafi dacewa ga
gubar nan ta cin
mutuncin mutane.
Alkur’ani ya dora
Musulmi a kan kame
harshe da tsarkake shi,
wannan yana cikin fadin
Allah Madaukaki cewa:
“Don me a lokacin da
kuka ji shi (zancen cin
mutuncin wadansu),
muminai maza da
muminai mata ba su yi
zaton alheri game da
kansu ba, kuma suka
ce, “Wannan kiren karya
bayyananne?” (k:24:12).
Ta yin haka sai a
kubuta daga shakkun
zukata, a tsarakaka
daga hassada da kyara,
a wayi gari mutunci ya
tsaru daga giba da
annamimanci da kiren
karya da shaidar zur.
Haka ma ya zo a cikin
magana mai inganci mai
fasaha daga
masoyinmu mai
cetonmu (SAW):
“Musulmi shi ne wanda
Musulmi suka kubuta
daga (cutarwar)
harshensa da
hannunsa.” Buhari da
Musulim suka ruwaito
shi. Kuma da haka sai
kyawawan dabi’u su
cika, karimci ya yadu, a
wayi gari ’yan
uwantaka da soyayya
su bunkasa su yi karfi.
Hadin kai ya ginu ya
karfafa a tsakanin
jama’a. Son Allah ya
samu wurin zama
daram a zukatanmu.
Wannan a wurin Allah
ba abu ne mai wahala
ba.
Da wannan sai ku yi
salati da taslimi a bisa
Annabi masoyi mai
girma, mai matsayi
madaukaki da girma,
mai daukakar girma mai
karimci kamar yadda
Maulanmu Mai jin kai Ya
umarce ku a cikin Abin
saukarwa Mai hikima,
(Alkur’ani), Wanda Ya
girma Ya daukaka Ya ce:
“Lallai ne Allah da
mala’ikunSa suna salati
ga Annabi. Ya ku
wadanda suka yi imani!
Ku yi salati a gare shi,
kuma ku yi sallama
domin amintarwa a
gare shi.” (k:33:56). Shi
kuma (SAW) ya ce:
“Wanda ya yi min salati
sau daya, Allah Zai yi
masa salati sau goma a
madadinta.”
Allahumma faj’al
salatuka wassalamu
muda’afan,
Linabiyyikal mukhtari
khairi mushaffa’i.
Almusdafal hadi ilaika
Muhammadin,
Wal ali wal as’habi
summat tabi’i.
Ya Ubangiji! Ka kara
tsira da aminci da
albarka a bisa Bashirun
Nazirun kuma Sirajun
Munir (SAW) da
alayensa da
sahabbansa.
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (3)(1)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi(11)
Shin kana cikin ’yan
gatan Allah a Ranar
kiyama?(1)
Kyauta da kyauta – yi
don Allah ba ta rage
dukiyar musulmi (2)
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (4)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (1)
Illar cin mutuncin
mutane (2)
Kyauta da kyauta-yi don
Allah ba ta rage dukiyar
Musulmi
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa(5)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (7)
Illar cin mutuncin
mutane (1)
Manuniya kan ladubban
yin addu’a (3)
Yadda ya kamata mu
kasance a rayuwarmu
ta yau da kullum(1)
are da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi
Musulmi da farfagandar
makiya(1)
B

Advertisements

Illar cin mutuncin mutane (1) @aminiyya

Illar cin mutuncin
mutane (1)
Category: Mumbarin
musulunci Published on
Friday, 04 December
2015 14:58 Written by
Hudubar Sheikh
Abdurrahma As-Sudais
Babban Limamin
Masallacin Ka’aba Hits:
193
Gabatarwa: Bayan haka,
ya ku bayin Allah! Ku bi
Allah Madaukaki da
takawa a cikin magana
da aiki. Ku yi maSa
takawa bisa tawali’u da
bin umarninSa safe da
maraice, kuna masu
tabbatar da girma da
daukaka da fiffiko da
kamalarSa. “Kuma
wanda ya bi Allah da
takawa, Allah zai
kankare masa munanan
ayyukansa, kuma Ya
girmama masa
sakamako.” (k:65:5).
Ya ku Musulmi! A yayin
da duniya ke fama da
fitintinu masu yawa,
jere da juna, take fama
da munanan bala’o’i
marasa iyaka, wadanda
suke girgiza zukata
suka shallake tunani da
hankulan jama’a, sai ga
zamani ya zo da wani
sabon abu da ke bata
tunani ke raunana
tunanin zababbu da
gama-garin jama’a,
yana bijiro da al’umma
zuwa ga rarrabuwa da
rugujewa, yana
kekketawa da yayyaga
hadin kan jama’ar
Musulmi da zaman
lafiyarta. Al’umma ba
ta ji zafi ba, face
saboda aukuwarsa,
jama’a da daidaikun
mutane ba su gushe ba,
face wannan abu yana
kekketa su yana karya
su, yana jefa su cikin
fushin zubar da jini.
Wannan abu – Allah Ya
tsare ku – shi ne cin
mutuncin mutane da
bata martabarsu da
tuhumar barrantattu
daga cikinsu da niyyar
cin zarafinsu. Hakika
wannan abin ki ne,
kuma kaiton yin haka,
Allah wadaran wannan
abin zargi da wawaye
suke riko da shi, hali ne
da ke kaiwa ga watsa
kazafi da kiren-karya da
kalamai masu jawo
fasadi a tsakanin
Musulmi, ya kawo juya
baya ga juna da kaurace
musu. Hakan na lalata
zamantakewa ya jawo
kirkirar karya a kan
mutum ba kunya ba
tsoro, ba don komai ba,
sai don a zubar da
mutuncin wani haka
kawai, kuma a haifar da
cutarwa marar iyaka da
za ta daidaita zaman
jama’a ta girgiza tushen
zaman al’umma.
Saboda wadannan
miyagun abubuwa da
wannan dabi’a ke
jawowa na dagula
al’amura da bata zaman
lafiya, sai gargadi mai
karfi da tattalin narkon
azaba mai tsanani ya zo
a cikin Alkur’ani da
Sunnah kan munin
makomar duk mai kiren-
karya yana watsawa:
“Kuma wadanda suke
cutar muminai maza da
muminai mata, ba da
wani abu da suka aikata
ba, to, lallai sun dauki
kiren-karya da zunubi
bayyananne.” (k:33:58).
Daga Abu Huraira (RA)
ya ce: “Lallai Annabi
(SAW) ya ce: “Riba tana
da matakai ko nau’o’i
har saba’in. Mafi
saukinta shi ne misalin
mutum ya yi zina da
mahaifiyarsa. Kuma lallai
mafi girman riba, shi ne
mutum ya rika cin
mutuncin dan uwansa.”
Bazzaru ya ruwaito shi
a cikin Musnad dinsa sai
Ibn Abu Shaiba a
Musnaf dinsa.
Allahu Akbar! Me ya kai
girman mutuncin
Musulmi? Me ya kai
daukaka da karimcinsa?
Domin haka ne shari’a
ta tsare shi kada a zagi
mutum kada a fada
masa mummunar
magana kada a auka
wa mutincinsa, kada a
soke shi kada a yi masa
kazafi. Kai kiyaye
mutunci, mafi kyan abin
da ake nema ne, kuma
mafi girman manufofin
shari’a kamar yadda
ma’abuta ilimi irin su
Shadabi da wadansu
suka bayyana.
Ya ku muminai! Bin
aibobin mutane da
al’aurorinsu don gano
nakasunsu da
gazawarsu da
kazantarsu mummunar
hanya ce mai
halakarwa. dabi’a ce ta
mutanen da ake zargi
kuma kazanta ce, kuma
ta saba wa shari’ar
Allah Madaukaki da
shiriyar ManzonSa
(SAW) wanda yake
cewa: “Albarka ta
tabbata ga wanda ya
shagaltu da
laifuffukansa daga
laifuffukan mutane.”
Bazzaru ya ruwaito a
Musnad dinsa sai Baihaki
a Shu’ubarsa.
Wani magabaci yana
cewa: “Mun riski
magabatan kwarai ba
su ganin ibada ta
takaita a kan Sallah da
Zakka kawai, a’a suna
ganin ta hada da
kamewa daga taba
mutuncin mutane.”
Kuma Malik bin Dinar
(Allah Ya yi masa
rahama) ya kasance
yana yawan cewa: “Ya
ishi mutum zunubi a ce
bai kasance salihi ba,
saboda yana aukawa ga
cin mutuncin mutane.”
Kuma mafi muni daga
cikin cin mutunci shi ne a
rika kazafi kiri-kiri a soki
mutum a bata shi a ce
ba haka yake nufi ba a
zuciyarsa, a tuhumi
niyyarsa da manufarsa.
A kutsa cikin dukkan
siffofi na gaibi da ke
cikin zuciyarsa a yi
masa kazafin aibubbuka
da barna da babu
wanda ya san
hakikaninsu ban da Allah
Madaukaki. Kuma a yi ta
watsawa da yayata
wadannan abubuwa ta
hanyar kiyayya da rudin
mutane a kawata
kalmomi na karya a
basar da jahilai a watsa
sharruruka. Ina abin da
ya kai wannan zama
abin bakin ciki, tir da
wannan abin bakin ciki!
Kuma karin abin bakin
ciki da ke cikin wannan
muguwar dabi’a ta keta
rigar mutuncin mutane,
shi ne, yadda ire-iren
wadannan karairayi
suke zama tamkar
gaskiya a wurin
mutane. Su zamo su ne
daidai, su ne gaskiya.
Ku ji tsoron Allah! Ku ji
tsoron Allah! Ba yadda
za a yi haka ya zama
gaskiya, wannan ba
wani abu ba ne, face
jahilci da mugun zato da
suke haifar da aibu da
gadar da zunubi. Masu
yin haka Allah Ubangijin
talikai Ya siffanta su da
cewa: “Ba mu zato,
face zato mai rauni,
kuma ba mu zama
masu yakini
ba.” (k:45:32).
Kowane lafazi za a
taskace shi a cikin
littattafan ayyukanmu
domin Ranar Hisabi, a
cikinsa za mu ga aikin
sharrin da muka furta
da bata wani da muka
yi a cikin lafazi da labari
an rubuta su lafazi-
lafazi.
Ya ’yan uwa a cikin
imani! Ana yin haka ne
alhali miyagun abubuwa
suna karuwa, munanan
ayyuka suna dada
yaduwa, cin mutunci ya
zama babban abin ado a
tsakanin al’umma.
Malamanta sun zamo
abin dariya, wanda yake
cin mutuncinsu ya zama
hazaki abin koyi a
tsakanin mutane, ya
zama tauraro, saboda
yana tozarta lamarinsu,
yana bata su ta
kafafen sadarwa na
zamani!
Duk inda ka juya abin da
za ka gani, shi ne suka
da zagi da soki burutsu
da cin dunduniya ta
amfani da alkaluma a
yada dafin mujirimanci
da harsuna masu guba
a ci mutuncin mafifitan
cikin al’umma,
barrantattu da salihai
da masu tsarkinsu,
wandanda suke rayuwa
domin gyara da maganin
cututtukan al’umma!
Hakika mai tsira da
amincin Allah ya fadi a
cikin mashahuriyar
hudubarsa a Ranar Arfa
cewa: “Lallai jininku da
dukiyarku da
mutuncinku haramun ne
(katangaggu ne) a
tsakaninku, kamar
yadda wannan rana
taku take (da martaba)
a wannan gari naku, a
wannan wata naku
(masu alfarma).” Kuma
(SAW) ya ce: “Kowane
Musulmi haramu ne a
kan dan uwansa
Musulmi ya taba jininsa
ko dukiyarsa ko
mutuncinsa.” Muslim ya
ruwaito.
Imam Ahmad (Allah Ya
yi masa rahama) ya ce:
“Ban taba ganin wani
yana magana a cikin
mutane ba (yana cin
mutuncinsu), face
(mutuncinsa) ya zube.”
Shaihul Islam Ibn
Taimiyya (Allah Ya yi
masa rahama) ya ce:
“Magana kan mutane
wajibi ne ta kasance
bisa ilimi da adalci ba da
jahilci da zalunci ba.
Kuma auka wa
mutuncincu ya fi satar
dukiyarsu muni.”
“Ya mai keta mutuncin
mutane mai yanke,
Hanyoyin kauna da
soyayya, za ka rayu ba
abin mutuntawa ba.
Da ka kasance
’yantacce daga tsatso
mai girma,
Ba za ka kasance mai
keta mutuncin Musulmi
ba.”
Don haka ya ku ’yan
uwa a cikin imani! Lallai
mai kutsawa a cikin
mutuncin Musulmi,
kuma mafi muni da
kebantar girman masu
karkata, shi ne mai cin
mutuncin shugabannin
Musulmi da malamai da
masu gyara. Halinsa shi
ne juya wa Allah baya
da bijire maSa, mai
komawa zuwa ga
tsanani, bai san ya yi
godiya da shukura ga
ma’abucin falala ba,
balle ya san kima da
matsayinsa.
Hakika an wayi gari
wadansu mutane
musamman saboda
samuwar sababbin
hanyoyin sadarwa, sun
zamo ba su da sukuni,
ba su da hakuri, face
sun kekketa mutuncin
mutane da munanan
kalamai da zunde da
tuhume-tuhume. Tir da
manufa da burinsu.
Suna rubuta zur da
alkalumansu, suna boye
gaskiya. Da haka
tunaninsu ke umartarsu
domin su samu damar
wargaza hadin kan
al’ummar Musulmi da
muminai ta hanyar
rubuce-rubucen son
zuciya da bin son
rayukan kungiyoyi da
mazhabobinsu, ba su
yin aiki face ga
wadansu kungiyoyin
asiri da burinsu shi ne
wargaza hadin kai da
zaman lafiyar al’ummar
Musulmi.
Ya ku masu keta
mutunci domin ganin
bayan Musulmi da kawo
karshensu! Ku nisanci
wadannan miyagun
abubuwa masu
fusatarwa, ku ciru daga
wadannan abubuwa
masu halakarwa, ku yi
kwadayi zuwa addini ta
hanyar neman tsira da
salama gabanin
aukuwar mutuwa mai
zuwa afke da nadama:
“Kuma ba domin falalar
Allah ba a kanku da
rahamarSa, a cikin
duniya da Lahira. Lallai
ne, da azaba mai girma
ta shafe ku a cikin abin
da kuka kutsa da
magana a
cikinsa.” (k:24:14).
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (3)(1)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi(11)
Shin kana cikin ’yan
gatan Allah a Ranar
kiyama?(1)
Kyauta da kyauta – yi
don Allah ba ta rage
dukiyar musulmi (2)
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa (4)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (1)
Illar cin mutuncin
mutane (2)
Kyauta da kyauta-yi don
Allah ba ta rage dukiyar
Musulmi
Mu nazarci wasu
sinadaran kyautata
rayuwa(5)
Tare da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi (7)
Illar cin mutuncin
mutane (1)
Manuniya kan ladubban
yin addu’a (3)
Yadda ya kamata mu
kasance a rayuwarmu
ta yau da kullum(1)
are da Sheikh Yunus
Is’hak Almashgool,
Bauchi
Musulmi da farfagandar
makiya(1)

Sheikh Isa Ali Pantami SAKON KHUDBAH DAGA MASALLACIN ANNABI (SAW) DAGA BAKIN SHAYKH DR HUSAIN BN ABDUL’AZIZ ALUSH- SHAYKH (HafizahulLaah)

Sheikh Isa Ali
Pantami
SAKON KHUDBAH DAGA
MASALLACIN ANNABI
(SAW) DAGA BAKIN
SHAYKH DR HUSAIN BN
ABDUL'AZIZ ALUSH-
SHAYKH (HafizahulLaah)
.
Bil hakika na saurari
Qhudbah mai ratsa jiki
da tasiri a zuciyar mai
yin Khudbar, kuma mai
tasiri a zukatan masu
sauraro a Masallacin
Fiyayyen Halitta (SAW).
Gaskiya khudbar na da
tsawo sosai, amma ga
dan kadan daga cikin
ma'anar ta.
1) Wasiyyar Allah ga
bayinSa shine muyi
taqawa zuwa gare Shi,
sannan mu bauta ma
sa SHI kadai.
2) Dukkan al'ummar da
su kayi wa Allah da
ManzonSa biyayya suna
samun rayuwa mai
da'di da kuma taimakon
Allah.
3) Dukkan wanda suka
juyawa dokokin Allah da
ManzonSa suna shiga
rayuwa mai 'kunci da
tsanani da 'kas'kanci.
4) Annabi (SAW) da
Sahabbansa (RA) sun yi
imani da Allah da
ayyuka masu Nagarta,
wannan ya basu nasara
da kuma taimako daga
gun Allah (SWT).
5) Mafiya yawan 'kunci
da kaskanci da tsanani
da al'ummah ta fad'a
ciki, sa'bon Allah ne ya
kai al'ummah. Domin
dukkan al'ummar da ta
yi watsi da taimakon
addini ta shagaltu da
neman Duniya kadai,
Allah yana 'dora ma ta
kaskanci. Don haka
masu neman canji dole
suyi biyayya ga Allah.
LIMAMIN YAYI ADDU'O'I
KAMAR HAKA:
1) Yaa Allah ka gyara
halayen Musulmai a
Duniya.
2) Yaa Allah duk wanda
aka ba shi jagorancin
al'ummah sai ya
tausasa mu su, Yaa
Allah ka tausasa ma sa.
Yaa Allah duk wanda
aka ba shi Jagorancin
al'ummah sannan ya
tsananta musu, Yaa
Allah ka tsananta
masa.
3) Yaa Allah ka shayar
da mu ruwan sama mai
albarka.
4) Yaa Allah ka
magance mana
damuwowin mu.
5) Yaa Allah ka amintar
da mu,…
Wannan shine sakon a
takaice. Muna addu'ar
Allah ka kar'bi wannan
addu'o'in kuma ka bamu
ikon aikin da sa'kon
khudbar,…

Hudubar Jumu’a Daga Masallacin Jumu’a na Biyu dake garin Numan a Jihar Adamawa – Sheik Nuruddeen Tukur Numan,

Hudubar Jumu'a Daga
Masallacin Jumu'a na
Biyu dake garin Numan
a Jihar Adamawa –
Sheik Nuruddeen Tukur
Numan, Na ranar
(21/02/1437 =
04/12/2015),

  1. click to download
  2. •Ga masu matsalar downloading sai subi ta wannan link dake kasa: click download

ayi sauraro lafiya.
Domin samu karin hudubabi da mudahara shiga
darulfikr.com