Category Archives: Jibwis Nigeria

BA A KAFA KUNGIYAR IZALAH A KAN MAZHABAR MALIKIYYAH BA: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

1. Ba a kafa Kungiyar Izalah a kan
mazhabar Malikiyyah ko wanin
Malikiyyah ba daga cikin Mazhabobin da
ke cikin fage, a’a an kafa ta ne a kan yin aiki da Alkur’ani da Hadithi da kuma
Ijma’i.
2. A inda duk mazhabar Malikiyyah ko
waninta suka dace da Alkur’ani da
Hadithi da kuma Ijma’i, to lalle kungiyar
Izalah na tare da su a nan, a inda kuma mazhabar Malikiyyah ko waninta suka
saba wa Alkur’ani da Hadithi da kuma
Ijma’i to lalle kungiyar Izalah ba ta tare
da su a nan.
3. Lalle abin takaici ne har kullum ‘yan
bidi’ar da ba sa jin kunyar yi wa Duniya karya su rika cewa: an kafa kungiyar
Izalah ne a kan Alkur’ani da Hadithi da
kuma Mazhabar Malikiyya!
4. Tabbas babu inda lafazin ambaton
mazhabar Malikiyyah ya zo koda sau
daya ne a cikin constitution din Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis
Sunnah. Babu inda za a sami lafazin
Mazhabar Malikiyyah a rubuce tun daga
shafin farko na Constitution din Kungiyar
har zuwa shafinsa na karshe.
5. Lalle abin da yake rubuce cikin constitution din Kungiyar Jama’atu
Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah shi
ne: Ita kungiya ce ta addinin Musulunci
tsantsa kamar yadda Annabi
Muhammadu mai tsira da amincin Allah
ya taho ta shi, wacce take dogara da Alkur’ani da Hadithan Manzon Allah da
kuma Ijma’i.
6. Wannan shi ne hakikanin Kungiyar
Izalah da constitution dinta, ba wai
karairayin da wasu yan bidi’ah ke yadawa
ba game da ita. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Advertisements

WA’AZIN KASA A GARIN KANGIWA NA JIHAR KEBBI

Shugaban kungiyar Izala Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban Majalisar Malamai Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo
Daraktan agaji Injiniya Mustapha Imam Sitti
A madadin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunna ta tarayyar Najeriya, suna farin cikin gayyatar ‘yan uwa musulmi zuwa wajen wa’azin kasa da zata gabatar a garin kangiwa dake jihar Kebbi a Naijeriya A Ranakun Asabar 25 da Lahadi 26 ga wannan wata na februru a shekata ta 2017 in Allah ya yarda.
-Babban Bako na Musamman : Mai girma gwamnan jihar kebbi, Sanata, Atiku Bagudu Abubakar
-Manyan Baki sun hada da:
– Mataimakin Gwamnan jihar kebbi,
Alhaji kanal, Sama’ila Yombe Dabai (mai ritaya)
-Sanata mai wakiltar kebbi ta tsakiya,
Alhaji Muhammadu Adamu Aliero.
-Sanata mai wakiltar Kebbi ta Arewa, Dr. Yahaya Abdullahi Argungu
-Dan Majalisar tarayya mai wakiltar, Arewa Dandi
Alhaji Dakta Hussaini Sulaiman Kangiwa
-Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Suru da Bagudo Abdullahi Hassan Suru.
-Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza Engr. Abdullahi Umar Muslim
-Uban taro: Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Isma’ila Muhammadu Mera .(CON)
Masu masaukin Baki:
Alhaji Yusuf Sulaiman (Mai arewan Kangiwa)
-Hon. Muhammad Hamid
Kantoman karamar hukumar Mulki ta kangiwa
-shugaban Izalar jihar kebbi, Ustaz Aliyu Abubakar Dan’agaji jega.
Malamai masu wa’azi:
-Sheikh Dr. Alhassan Sa’id Adam Jos
-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe
Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe
-Sheikh Habibu Yahaya Kaura
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Barr. Ibrahim Sabi’u Jibia
-Sheikh Sheikh Khalid Usman Khalid
-Sheikh Abdulbasir Isah Unguwar mai kawo
-Sheikh Umar Jega
-Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi rijiyar lemo
-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Usman Birnin Kebbi
-Alaramma Bashir Gombe
-Alaramma Yusuf Suru
Da sauran malamai da alarammomi na kungiyar
Allah ya bada ikon halarta Amin.
Sanarwa daga Babban Sakataren kungiyar, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe
JIBWIS NIGERIA