Binciken malaman Kimiyya kan tsibirin Bamuda (1); Daga jaridar aminiya

Binciken malaman
Kimiyya kan
tsibirin Bamuda (1)
Category: Kimiyya da
fasaha Published on
Friday, 27 June 2014
01:00 Written by
Maimaici Mai Fa’ida Hits:
3007
Assalaamu
alaikum Baban
Sadik, da fatan
alheri a gare ka.
Don Allah idan zai yiwu
ka maimaita mana
kasidar “Tsibirin
Bamuda” mana. Lokacin
da na fara karanta
jaridar Aminiya ka riga
ka gabatar da kasidar,
kuma ni ba ni da
adireshin Imel balle in ce
a turo mini. Kuma na
lura lallai babu kasidar
da ta kai wannan kasida
ta Tsibirin Bamuda farin
jini. Da fatan za ka
taimaka, idan babu
damuwa. Allah Ya kara
basira, amin. – Ummu
Haidar, Gombe
Wa alaikumus salam,
Maman Haidar barka da
warhaka. Lallai kamar
yadda kika fada,
wannan kasida mai
take: “Binciken Malaman
Kimiyya kan Tsibirin
Bamuda (Bermuda
Triangle),” ta shahara
sosai, nesa ba kusa ba.
Ni kaina ban san sau
nawa na aika wa masu
karatu ba, a bisa
bukatarsu. kasida ce da
na rubuta tun shekarar
2007; shekaru kusan
bakwai kenan a halin
yanzu. Amma ko cikin
makon da ya gabata
akwai wadanda suka
bukaci in tura musu,
kuma na tura. Sannan
akwai masu karatu
irinki, marasa adireshi
ko akwatin Imel, kuma
masu sha’awar ace sun
kara karanta wannan
kasida a karo na biyu ko
ma farko. Ganin sakonki
ne ya kara mini kaimi
wajen kara yin nazari
kan kasidar, da gyara
wasu kalmomi don kara
musu amo da tsari a
ka’idojin rubutu, duk da
cewa babu wani abu
sabo da ya sake
aukuwa na mamaki a
wannan tsibiri tsakanin
bayyanar kasidar a
karon farko zuwa
yanzu. Da fatan
wadanda ba su samu
karanta kasidar ba a
karon farko za su
amfana. Allah sa mu
dace, amin.
Mabudin Kunnuwa
Duk da cewa akwai
bigirorin duniya da dama
da abubuwan mamaki
ke faruwa a cikinsu ba
tare da dan adam ya
fahimci musabbabansu
ba, Tsibirin Bamuda
(Bermuda Island ko
Bermuda Triangle) ne
kadai ya fi shahara a
bakunan mutane
sanadiyyar haka.
Wannan shahara ta
samo asali ne daga
nahiyar Kudancin
Amurka (South
America), a hankali
labarin ya ci gaba da
yaduwa zuwa sauran
kasashen duniya.
Manyan ababen
mamakin da ake ikirarin
suna faruwa a muhallin
tekun da wannan tsibiri
yake sun hada da
bacewar jiragen sama –
masu dauke da fasinjoji
‘yan kasuwa ko na soji
– da jiragen ruwa –
manya da kanana da na
shawagi. Idan suka
bace a galibin lokuta, ba
a ganin buraguzan jirgin
balle a kaddamar da
bincike kan dalilan da
suka haddasa faruwar
hadarin. Wannan
al’amari abin al’ajabi, a
cewar masu bayar da
labarai, bai tsaya a
bacewar jirage ba tare
da ganin buraguzansu
kadai ba, har da wasu
labarai masu caza
kwakwalwa kan irin
yanayin da tekun ke
kasancewa na launi da
kuma sulmuya a wasu
lokutan, ko kuma wasu
irin dabi’u da ake ikirarin
gira-gizan da ke saman
tekun ke shiga, a yayin
aukuwar hadarurrukan
da suka fara faruwa
shekaru kusan dari biyu
da suka gabata. Ire-iren
wadannan labarai sun
samo asali ne daga irin
jawaban da masu lura
da na’urar filin saukan
jiragen sama da ke
tsibirin ke bayarwa. Ko
wadanda ake tarawa
wajen binciken da
hukumomin gwamnatin
Amurka da ke lura da
ire-iren wadannan
hadarurruka ke yi. Da
wannan, marubuta
suka sa wa wannan
muhalli suna: The
Bermuda Triangle
(Kusurwar Bamuda), ko
kuma The Debil’s
Triangle (Kusurwar
Shedan).
A halin yanzu da dama
cikin wadanda suka
taba jin labarin wannan
bigire na Bamuda, sun
yarda cewa wani wuri
ne mai cike da almara,
kamar yadda galibin
turawa masu bincike
suka fada. Da kuma
cewa babu wanda ya
san abin da ke haddasa
wannan al’amari, sai
Allah (ga wadanda suka
yarda da Allah kenan),
ko kuma dabi’a ta
shu’umcin wurin. Wasu
suka ce aljanu ne a
wurin. Wasu suka ce
akwai wasu halittu ne
na musamman da a
harshen Turanci ake
kira Aliens, masu
haddasa hakan. Wasu
suka ce a a, irin yanayin
wurin ne kawai. Da dai
sauran ra’ayoyi masu
kama da haka. Shin,
meye gaskiyar
wadannan zace-zace da
ake ta yi kan wannan
tsibiri? Wani irin bincike
aka yi wajen gano
hakan? Jiragen ruwa da
na sama guda nawa
suka bace a wannan
mahalli? Rayuka nawa
suka salwanta? Wa da
wa suka yi rubuce-
rubuce kan haka cikin
Malam Kimiyya da masu
sha’awar rubutu kan
al’amuran mamaki a
duniya? Meye ra’ayin
nazarin da Malaman
Kimiyya suka yi kan
dalilin faruwar
wadannan abubuwan
mamaki? Shin, wai ma
tukun, a duniya akwai
wasu wurare ne masu
irin wannan dabi’a, ko
dai tsibirin Bamuda ne
kadai? In eh akwai, to
me ya sa na tsibirin
Bamuda ya sha
bamban, ya shahara
fiye da sauran a
duniya? Wadannan, da
ma wasu tambayoyi, za
mu samu amsoshinsu
cikin makonni masu
zuwa in Allah Ya yarda.
A Ina Tsibirin Yake?
Kafin mu yi nisa, asalin
tsibirin Bamuda, watau
Bermuda Islands, yana
gab da tsakiyar tekun
Atlantika ne, Arewa da
Jihar Fulorida da ke
Amurka. Kuma duk da
cewa ana danganta
wannan wuri ko
kusurwa da tsibirin
Bamuda, sai dai ba a
wannan tsibiri kadai
wannan kusurwa yake
ba. Kusurwar Bamuda
wani wuri ne da ya hada
manyan gabar tekunan
kasashe guda uku da ke
nahiyar Arewaci da
kuma kudancin
Amurka. Kusurwar
farko ta faro ne daga
gabar Fulorida ta kasar
Amurka, ta zarce zuwa
gabar babban tsibirin
Puerto Rico da ke
yamma maso-kudu da
gabar Fulorida. Daga
tsibirin Puerto Rico
kuma kusurwar ta cilla
Arewa, inda ta tike a
gabar tsibirin Bamuda
da ke kusa da tsakiyar
tekun Atlantika.
Wannan wuri ko
mahalllin teku da ke
tsakanin wadannan
gabobi guda uku, shi ake
kira The Bermuda
Triangle, ko The Debil’s
Triangle.
An danganta wannan
kusurwa da tsibirin
Bamuda ne saboda a
nan ya tike, kuma
galibin ababen hawa
kamar su jiragen sama
da na ruwa wadanda
ake amfani da su
wajen kasuwanci da
shawagi da atisayen
soji a wannan nahiya,
duk a can suke tikewa
kafin su komo inda suka
taso. Ko kuma daga can
suke wucewa zuwa
wasu nahiyoyin, irin su
Turai da Arewacin
Amurka da kasashen
Asiya.
Wannan kusurwa ta
Bamuda ita ce bigiren da
jiragen sama da na
ruwa ke shawagi fiye
da kowane wuri a
duniya. An kiyasta
cewa akalla akan samu
sawun jiragen sama
daga wannan nahiya
zuwa kasashen turai da
sauran nahiyoyi, sama
da dubu hamsin a
shekara. Bayan haka,
akwai jiragen ruwa da
na kasuwanci da na
shawagi ko yawon bude
ido, da kuma jiragen
saman atisayen soji da
Hukumar Sojin Amurka
ke turawa suna
shawagi, watau kai-
komo don yin atisaye.
Har wa yau akwai masu
shawagi da kananan
kwale-kwalen
shakatawa wadanda a
harshen turanci ake kira
Pleasure Boats, da
kuma jiragen ruwan
tsere da ake kira
Yatchers. Bayan haka,
akwai filayen saukan
jiragen sama a dukkan
kusurwoyin nan uku,
tare da tashar jiragen
ruwa masu karban
manya da kananan
jiragen da ke shawagi a
wannan wuri. Sannan
kuma sai miliyoyin masu
zuwa yawon bude ido
daga sauran kasashen
duniya, musamman ma
Amurka da Turai. A
takaice dai, wannan
wuri rayayyen wuri ne
da sawun jirgin ruwa da
na sama da na masu
ziyara ba su daukewa;
daga shekara zuwa
shekara.
Zai dace mai karatu ya
rike wannan karatu kan
yawan zirga-zirgar da
ake yi a wannan wuri,
domin zai taimaka
masa wajen karba ko
rashin karbar dalilan da
wasu marubuta suka
bayar wajen yanke
hukuncinsu na karshe.
Yaushe Abin Ya Fara?
Wannan kusurwa da
ake wa take da
“Kusurwar Shedan” – ko
Debil’s Triangle – ya
fara cin jiragen sama da
na ruwa ne shekaru
kusan dari biyu da suka
gabata, duk da cewa ba
a fara fahimtar hakan
ba sai wajen shekaru
casa’in zuwa dari da
suka wuce. Daga nan
ne aka fara danganta
hadarurrukan da suka
gabata da wannan
yanayi mai ban
mamaki. Kamar yadda
bayanai suka gabata,
wannan kusurwa ta
Bamuda ta yi kaurin
suna ne wajen
hadararruka masu ban
mamaki, inda bayan
hadarin ake rasa abin da
ya haddasa shi, ko
kuma a ma kasa samun
buraguzai ko
gawawwakin wadanda
suka rasa rayukansu da
ma na jirgin gaba daya.
A wasu lokuta a kan
samu sakon neman
agaji daga direbobin
jiragen sama cewa suna
ganin wasu abubuwa
masu ban tsoro ko
firgitarwa. Kafin a
mayar da jawabin ceto
garesu, sai kawai a
nemi hanyar sadarwa a
rasa. Wani kuma zai
bugo ne cewa ba ya
ganin gabansa, bayan
kuma a na’urar lura da
yanayin sararin
samaniya babu wata
matsala da na’urar ke
hangowa: babu yanayin
hazo mai firgitarwa,
babu ruwan sama, babu
alamar mahaukaciyar
guguwa mai yi wa
jiragen ruwa dibar karan
mahaukaciya, amma sai
kawai a ji hanyar
sadarwar ta yanke.
Mafi shahara daga cikin
abubuwan mamaki da
suka faru a wannan
kusurwa shi ne hadarin
tawagan jiragen kai hari
da darkake abokan gaba
na kasar Amurka masu
suna Flight 19, wadanda
hukumar sojin sama na
kasar Amurka ta aika
don yin shawagi a
wannan kusurwa cikin
shekarar 1945. Duk da
cewa ana lura da tafiyar
wannan tawaga na
jirage ta hanyar na’ura
hangen nesa sadda
suka baro cikin kasar
Amurka, sai dai cikin
lokaci guda kawai sai
aka neme su aka rasa.
Da aka nemi sadarwa
da shugaban tawagar,
sai ya ce: “A yanzu
muna shiga wani irin
farin ruwa ne…al’amura
sun fara lalacewa.
Bamu san inda muke ba
a halin yanzu…ruwan
kore ne…a a, fari ne!”,
sai sadarwa ta yanke a
tsakanin masu lura da
na’urar da wannan
shugaban tawaga.
Bayan faruwar wannan
lamari, an yi ta bincike
cikin teku ba a samu
buraguzan wadannan
jirage ba balle wadanda
suke ciki. Babu wanda
ke da wani bayani
gamsasshe kan abin da
ya haddasa wannan
hadari har zuwa yau,
balle bayani kan
hakikanin wurin da abin
ya auku. A lokacin da
aka tura wata tawaga
ta manema jirage, da
suka isa wurin da
na’urar ta sanar da
faduwarsu, babu abin
da aka gani a wurin.
Daga nan aka ci gaba da
samun ire-iren
wadannan hadarurruka
masu ban mamaki da
al’ajabi. Wasu a kan
samu bayanai kan
batansu, bayan tsawon
lokaci; wasu kuma ko
alama ba a samu, sai
dai kawai a hakura.
Chelsea ta kori Jose
Mourinho
…Real Madrid za ta dibar
wa Rafa Benitez wa’adi
Man. United da
Manchester City sun
kebe Naira biliyan 348
don sayo Messi da
Neymar
Za a sayar da kulob din
FC Giwa
A watan gobe za a fara
gasar Firimiya ta
Najeriya
NFF ta yi wa ’yan
wasan U-23 ruwan
Naira
Madrid ta fara zawarcin
Mesut Ozil
CAF za ta karrama
Osimhen, Nwakali da
Amunike A Abuja
Gwamnan Neja ya
kalubalanci kungiyar
kwallon Gora ta Niger
Flickers
Ya tuka keke daga
Indiya zuwa Sweden
saboda soyayya
Yana fuskatar daurin
shekara 37 kan zagin
karen sarki
bayyade mu’amalar
kafafen sadarwar
zamani a basashen
duniya (I)
Matakan Sulhunta
Ma’aurata
Mawaka sun nuna
rashin gamsuwa da
kalankuwar Kaduna
Dokokin fim sun raba
kan hukuma da ’yan fim
din Hausa

Advertisements