GUDUNMAWAR SAHABBAN MANZON ALLAH WAJEN KAFUWAR DAULAR MUSULUNCI TA FARKO

GUDUNMAWAR SAHABBAN MANZON ALLAH WAJEN KAFUWAR DAULAR MUSULUNCI TA FARKO

Taron Kara wa Juna
Sani A Kan Gudunmawar
Sahabban Manzon Allah
Wajen Kafuwar Daular
Musulunci ta Farko
Dutse 30-31/Maris
2013M (18-19 J. Ula
1434H)
Wannan Taro samu halartan
Manya-manyan Malaman
Sunnah Sahararru a wannan
kasa tamu mai albarka kuma
sun gabatar da kasidu masu
Muhimmancin gaske. Kana iya
downloading ka kuma saurari
dukkan Maqaloli da aka
gabatar ta wadannan links
dake kasa.
Hakanan mai buqatan samun
Maqalolin a rubuce yana iya
rubuta imel dinsa a akwatin
comment.
01 Gabatarwa Daga Dr.
Abubakar Muhd Sani
02 Sahabban Manzon Allah
Kamar Yadda Hadisai Suka
Bayyanasu Daga Sheikh
Dr. Mansur Sokoto
03 Matan Manzon Allah a
Idon Al ummar Musulmi Daga
SheikhMuhammad Rabi’u
Rijiyar Lemo
04 Taimakon Da Sayyadina
Aliyu da Ya yansa Suka Bawa
Khalifofin Manzon Allah Uku
Daga Prof. Umar Labdo
05 Aqidar Al ummar Musulmi
Dangane Da Sahabban Annabi
S.A.W Daga Sheikh Ibrahim
Disina
06A Sahabban Manzon Allah
S.A.W. a Mahangar Al qurani
Mai Tsarki Daga Dr. Muhd
Muslim Ibrahim
06B Meye Gudummawata
Dangane da Wannan Seminar
Daga Engr. Bashir Aliyu
07 Alaqar Halifofin Manzon
Allah S.A.W. da Junansu Daga
Dr. Abubakar Muhd Sani
08 Hatsarin Sukan Sahabbai
A Shariar Musulunci Daga
Sheikh Salisu Muhd Gumel
09 Matsayin Annabi S.A.W a
Idon Sahabbansa Daga
Dr. Muhd Sani UmarRijiyar
Lemo
010 Aqidar Malaman Malikiya
Dangane da Sahabban Annabi
S.A.W. Daga Dr. Ibrahim Jalo
Jalingo
Dafata ‘ya uwa zasu taimaka
ta duk hanyar Da ta dace
wajen Yada wadannan
Karatuka masu Matiqar
Muhimmanci ga al’ummar
Musulmi.

danna nan domin saukewa

SAKON KHUDUBAR JUMU’AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE GARIN MADINA

Sheikh Isa Ali
Pantami
SAKON KHUDUBAR
JUMU'AH DAGA
MASALLACIN MANZON
ALLAH (SAW) DAKE
GARIN MADINA DAGA
BAKIN SHEIKH, DR,
IMAM BABA ALIYYU BN
ABDURRAHMAN AL-
HUZHAIFIY (Rahimahul
Laah). JUMU'AH 21/
Rabiul-Awwal/ 1437AH
(1/1/2016CE).
Dattijon Arziki, Dr
Huzhaifiy (Hafizhahul
Laah) yayi khudubar
akan "DARAJAR
ADDU'AH DA
MATSAYINTA GA
MUSULMI."
1) Imam ya fara
khuduba da yabo ga
Allah (SWT) da Salati ga
Annabi (SAW) da
adduar alheri ga
Sahabbai (RH) da sauran
Salihan bayi.
2) Sannan yayi
wasiyyar Taqawah ga
Musulmai, cewa ita
taqawah ribar rayuwa
dukka ya tattara gare
ta ne.
3) Allah ya kaddara
dukkan alheri yana da
sababin aukuwarsa,
haka kuma kuma
dukkan sharri yana da
dalilan faruwarsa. Wajibi
ne muyi riko da dalilan
alheri, kuma mu nisanci
dalilan aukuwar sharri.
4) Duk wanda yayi riko
da alheri da kuma
hanyoyin alheri na
Duniya da Lahira, Allah
zai saka masa da
Aljannah. Allah (SWT)
yana cewa: Shin akwai
sakamakon alheri in ba
alheri ba? Maanarsa duk
wanda ya aikata alheri,
Allah zai saka masa da
alherin Duniya da lahira.
5) Addu'ah tana da
amfani cikin dukka abun
da ya faru ga Mutum a
rayuwa, da cikin dukkan
abunda bai faru ba.
6) Dalilan da ke kawo
wa mutum gyaruwa,
da rabautuwa, da
nagarta shine "Adduah
bil Ikhlas" wato yin
addu'ah da tsarkake
zuciya a cikinta.
7) Lalle Allah yace mu
roke Shi zai amsa mana.
Allah yana cewa a cikin
Qur'ani: "…Ku roke Ni zan
amsa muku. Lalle ne
wadanda suka yi
girman kai daga yimin
ibadah (addu'ah) zasu
shiga Jahannama…"
8) Annabi (SAW) yana
cewa: addu'ah itace
ibadah. (Abu-Daud da
Tirmizhiy suka ruwaito)
.
9) Allah ya karantar da
mu adduah, idan ba dan
ya koya mana ba, da
bamu iya ba.
10) Babu lokacin da
Musulmai ke bukatar
addu'ah kamar wannan
zamani na FITINTINU.
Zamani ne da musifu
suka yi yawa a Duniya.
Zamani da MUNANAN
AQIDU, MASU BATAR
DA JAMA'AH SUKA
YAWAITA. Zamani da
KAFURAI suka yi
chaaaaa akan Musulmai.
11) Wannan zamani
dole mu dage da
adduah. Domin shine
zamanin da Allah yake
cewa: "Wallahi zamu
jarrabeku da wani abu
na tsoro, da yunwa, da
tauyewan dukiyoyi da
rayuka. Amma kayi
bushara ga masu
hakuri."
12) Annabi (SAW) ya
karantar da mu addu'ar
Yunus (AS) na cewa:
Laa'ilaha illa Anta,
subhaaanaKa inni kuntu
minaz Zhalimin."
Annabinmu yace: babu
musulmin da zai yi
addu'ah da wannan
addu'ah face Allah ya
amsa ma sa.
13) Adduah tana saukar
da ALBARKA a rayuwa
kuma tana bada kariya
daga sharri. Kamar
yadda Allah ya amsa
addu'ar Annabi Ayyub
(AS) ya ba shi waraka
daga cuta.
14) Zuwan Dujal shine
mafi girman fitina da
Duniya ke fustanka.
Amma duk da haka
addu'ah tana
taimakawa wajen
samun tsira daga
fitintinun Dujal din.
15) addu'ar da Annabi
(SAW) yayi wa
Sahabbansa (RA) a
Badar na daga cikin
dalilin NASARAR
MUSULMAI A DUNIYA.
Wannan Nasara kuma
har zuwa ranar
Kiyaamah.
ADDU'AH TANA DA
SHARUDDA DA YAWA.
DAGA CIKINSU AKWAI:
16) CIN HALAL yana
daga cikin sharuddan
karban addu'ah. Kamar
yadda Annabi (SAW) ya
karantar da Sa'ad Bn
Abi Waqqas (RA).
17) RIKO DA SUNNAH
yana daga cikin
sharuddan karban
addu'ah.
18) Duk wanda aka
zalunce shi, Allah yana
amsa addu'ar sa, ko da
KAFURI ne, ko da DAN
BIDI'AH ne, Allah yana
amsa addu'ar su idan an
ZALUNCE SU.
19) Ikhlasi shima
sharadin amsa addu'ah
ne.
20) Yabon Allah lokacin
adduar.
21) Rashin gaggawa
lokacin adduah.
22) Dauwama kan yin
adduah shima sharadin
karban adduah ne.
AKWAI LOKUTAN
KARBAN ADDUAH SUNE:
23) Sulusin dare na
karshe. Wato ka shi
daya na ukun dare na
karshe.
24) Tsakanin kiran
Sallah da ta da iqamah.
25) bayan kammala
saukan karatun Qur'ani.
26) Lokacin ganin
Ka'abah.
27) lokacin ba da
Sadaqa.
28) Lokacin saukan
ruwan sama.
29) sannan haramun ne
yin adduah ta hanyar
rokon matattu.
30) Duk wanda yayi wa
Allah tarayya da wani a
cikin adduah, kuma ya
daidai Allah da waninSa
lalle yayi SHIRKA MAI
GIRMA.
RUFEWA:
31) Babban limamin yayi
Salati ga Annabi (SAW)
da salatin Ibraahimiyya.
32) Adduah da Sahabbai
da Tabi'ai da wanda
suka biyo bayansu da
kyautatawa.
33) Adduah ta
Musamman ga
Alkhulaafu Arrashidun,
Abubakar da Umar da
Uthman da Aliyyu
(Radhiyallahu anhum),
Allah ya kara yarda da
su.
34) Yayi Adduar neman
gafara ga Matattunmu
gaba daya, Allah ya
gafarta musu.
35) Yayi Addu'ah ga
marassa lafiya, Allah ya
basu lafiya.
36) Yayi Allah ya karya
Azzuluman da ke kashe
bayin Allah a kasar
Sham.
37) Yaa Allah ka taimaki
addininKa.
38) Yayi addu'ar Yaa
Allah ka datar da
"Khaadimul Haramayn"
ga duk abun da Ka ke
so, kuma ka yar da da
shi.
39) Allah ka bamu ruwa
mai albarka.
Fassarawa: Isa Ali
Ibrahim Pantami
(21/03/1437AH. Kai
tsaye daga Haramin
Madinah).
Yaa Allah ka bamu ikon
aiki da khudubar da
darussa da ke cikinta,
kuma ka amsa mana
addu'o'inmu,…

YIN MURNAR SABUWAR SHEKARA, MUSAMMAN TA KIRISTOCI BA TA DA ASALI! (Sheikh Isa Ali Pantami)

YIN MURNAR SABUWAR
SHEKARA, MUSAMMAN
TA KIRISTOCI BA TA
DA ASALI! (Sheikh Isa Ali
Pantami)

YIN MURNAR SABUWAR
SHEKARA, MUSAMMAN
TA KIRISTOCI BA TA
DA ASALI!
Manzon Allah (SAW)
yana cewa: "Yana daga
kyawun Musuluncin
Mutum, ya bar abun da
bai shafe shi ba.
” [Sunan al-Tirmidhî and
Sunan Ibn Mâjah]. Yaa
Allah ka bamu ikon
tsayawa akan Sunnah,…
ENGLISH: a Muslim
doesn't celebrate the
new year, particularly
gregorian calendar.
Allah’s Messenger
(SAW) says: “From the
perfection of a person’s
Islam is his leaving
alone what does not
concern him."
May Allah guide us to be
consistent in following
the teachings of the
Prophet,…

MUHIMMANCIN KARANTA “AMANAR- RASUL” LOKACIN KWANCIYA – Sheikh Isa Ali Pantami

Sheikh Isa Ali
Pantami
MUHIMMANCIN
KARANTA "AMANAR-
RASUL" LOKACIN
KWANCIYA: Yaa Allah ka
sa mu wanye lafiya,…
Annabi (SAW) yana
cewa: Duk wanda ya
karanta ayoyi biyu
(Amanar-RASUL) na
karshen Suratul-
Baqarah lokacin
kwanciya sun wadatar
masa- daga Komai da
Komai (Bukhari ya
riwaito a Hadith 5009).
Yaa Allah ka bamu ikon
karantawa, kuma ka
wadatar mana daga
dukkan abunda yake
gabanmu a rayuwa,…

Jahadin Danfodio 001 to 003 – sheik albani zaria

Assalamu'alaikum warahmatullahi wabarakatuhu .

drop down to download this Islamic islamic lecture.

 • TITLE:-
  Jahadin Danfodio 001 to 003
 • SCHOLER NAME:- Sheik Muhammad Auwal Adam Albani zaria

 • LANGUAGE:- hausa language
 • TYPE:- mp3
 • DURATION OF EACH ONE:- 1:27:41

 • SIZE OF EACH ONE:- 10 MB
 • UPLOADED BY:- darulfikr.com

 • PUBLISHED BY:- Abubakar Nuhu Koso
 • Jahadin Danfodio 001 download now
 • Jahadin Danfodio 002 download now
 • Jahadin Danfodio 003 download now
 • To Download other files of Muhadara by Sheik Albani Zaria click here

 • To download more islamic files by many scholars click www.darulfikr.com

Jahiliyyah No 1 to 5 – sheik albani zaria

Assalamu'alaikum warahmatullahi wabarakatuhu .

drop down to download this Islamic islamic lecture.

 • TITLE:- Jahiliyyah No 1 to 5

 • SCHOLER NAME:- Sheik Muhammad Auwal Adam Albani zaria

 • LANGUAGE:- hausa language
 • TYPE:- mp3
 • DURATION OF EACH ONE:- 1:36:08

 • SIZE OF EACH ONE:- 11 MB
 • UPLOADED BY:- darulfikr.com

 • PUBLISHED BY:- Abubakar Nuhu Koso
 • Jahiliyyah no 1 download now
 • Jahiliyyah no 2 download now
 • Jahiliyyah no 3 download now
 • Jahiliyyah no 4 download now
 • Jahiliyyah no 5 download now
 • To Download other files of Muhadara by Sheik Albani Zaria click here

 • To download more islamic files by many scholars click www.darulfikr.com