KEBANTACCIYAR SALLAH A DAREN NISFU SHA’ABAAN. (Dr. Mansur Sokoto)

Dr. Mansur Sokoto
KEBANTACCIYAR
SALLAH A DAREN NISFU
SHA'ABAAN.
Malaman hadisi sun ce:
Babu wani hadisin da ya
tabbata daga Manzon
Allah (saw) game da
wannan sallar da ake
kira Salatul Alfiyya. Sai
hadisai qagaggu da
raunana. Kadan daga
cikin irin wadannan
hadisai akwai hadisin da
aka jinginawa
Sayyadina Aliyyu wai ya
ce: Manzon Allah (saw)
ya ce;
ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ
ﺷﻌﺒﺎﻥ ، ﻓﻘﻮﻣﻮﺍ ﻟﻴﻠﻬﺎ
ﻭﺻﻮﻣﻮﺍ ﻧﻬﺎﺭﻫﺎ ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﻳﻨﺰﻝ ﻓﻴﻬﺎ ﻟﻐﺮﻭﺏ ﺍﻟﺸﻤﺲ
ﺇﻟﻰ ﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ، ﻓﻴﻘﻮﻝ
ﺃﻻ ﻣﺴﺘﻐﻔﺮ ﻓﺄﻏﻔﺮ ﻟﻪ ، ﺃﻻ
ﻣﺴﺘﺮﺯﻕ ﻓﺄﺭﺯﻗﻪ ، ﺃﻻ
ﻣﺒﺘﻠﻰ ﻓﺄﻋﺎﻓﻴﻪ ، ﺃﻻ ﺳﺎﺋﻞ
ﻓﺄﻋﻄﻴﻪ ، ﺃﻻ ﻛﺬﺍ ﺃﻻ ﻛﺬﺍ
ﺣﺘﻰ ﻳﻄﻠﻊ ﺍﻟﻔﺠﺮ
Ma'ana:
“Idan daren Nisfu
Sha'aban ya zo ku raya
darensa da Qiyamullaili,
kuma ku azumci
yininsa, domin Allah
Madaukakin Sarki yana
saukowa zuwa saman
duniya daga zarar rana
ta fadi, yana cewa: shin
akwai mai neman
gafara ana gafarta
masa, ina mai neman
arziki na arzuta shi, ina
wanda Allah ya jarrabe
shi na yaye masa, ina
mai kaza da kaza har
zuwa ketaowar alfijir."
Amma sallar da ake kira
Salatul Alfiyya, salla ce
da ba ta da asali a cikin
addinin musulunci, kuma
an rawaito hadisai
masu yawa game da
bayanin siffarta da
falalarta, sai dai
dukkaninsu babu wanda
ya tabbata daga
Manzon Allah (saw).
Daga cikin wadannan
hadisan akwai hadisin
da aka jinginawa
Sayyadina Aliyyuyu Ibn
Abi Dalib wai ya ce:
Manzon Allah (saw) ya
ce:
ﻳﺎ ﻋﻠﻲ ﻣﻦ ﺻﻠﻰ ﻣﺎﺋﺔ ﺭﻛﻌﺔ
ﻓﻲ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ ﺷﻌﺒﺎﻥ
ﻳﻘﺮﺃ ﻓﻲ ﻛﻞ ﺭﻛﻌﺔ ﺑﻔﺎﺗﺤﺔ
ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭ )ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ (
ﻋﺸﺮ ﻣﺮﺍﺕ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻳﺎ
ﻋﻠﻲ ﻣﺎ ﻣﻦ ﻋﺒﺪ ﻳﺼﻠﻲ ﻫﺬﻩ
ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﺇﻻ ﻗﻀﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ
ﻭﺟﻞ ﻟﻪ ﻛﻞ ﺣﺎﺟﺔ ﻃﻠﺒﻬﺎ
ﺗﻠﻚ ﺍﻟﻠﻴﻠﺔ ﻗﻴﻞ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ
ﻛﺘﺒﻪ ﺷﻘﻴﺎ ﺃﻳﺠﻌﻠﻪ ﺳﻌﻴﺪﺍ
ﻗﺎﻝ ﻭﺍﻟﺬﻱ ﺑﻌﺜﻨﻲ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻳﺎ
ﻋﻠﻲ ﺇﻧﻪ ﻣﻜﺘﻮﺏ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻮﺡ
ﺇﻥ ﻓﻼﻥ ﺑﻦ ﻓﻼﻥ ﺧﻠﻖ ﺷﻘﻴﺎ
ﻳﻤﺤﻮﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻳﺠﻌﻠﻪ ﺳﻌﻴﺪﺍ …
Ma'ana:
“Ya Aliyyu! Duk wanda
ya yi salla raka'a dari a
daren Nisfu Sha'aban,
ya karanta Fatiha da
Qulhuw Allahu goma. Sai
Annabi ya ce: ya Aliyyu!
Babu wani bawa da zai
yi wannan sallar, face
Allah mai girma da
buwaya ya biya masa
buqatunsa da zai nema
a wannan daren. Sai aka
ce; ya Manzon Allah ko
da Allah ya rubuta shi a
cikin marasa rabo zai
mai da shi mai rabo? Sai
Manzon Allah (saw) ya
ce: na rantse da wanda
ya aiko ni da gaskiya,
haqiqa an rubuta a jikin
Lauhul Hamfuz cewa:
wane dan wane dan
wane an halicce shi
shaqiyyi, amma sai
Allah ya shafe shi ya
mai da shi marabauci…"
Haka kuma an sami
wani hadisi daga Amr
Ibn Miqdam daga Ja'afar
Ibn Muhammad daga
babansa ya ce:
ﻣﻦ ﻗﺮﺍ ﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﻨﺼﻒ ﻣﻦ
ﺷﻌﺒﺎﻥ ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ ﺃﻟﻒ
ﻣﺮﺓ ﻓﻲ ﻣﺎﺋﺔ ﺭﻛﻌﺔ ﻟﻢ ﻳﻤﺖ
ﺣﺘﻰ ﻳﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻟﻴﻪ ﻣﺎﺋﺔ
ﻣﻠﻚ ﺛﻼﺛﻮﻥ ﻳﺒﺸﺮﻭﻧﻪ
ﺑﺎﻟﺠﻨﺔ ﻭﺛﻼﺛﻮﻥ ﻳﺆﻣﻨﻮﻧﻪ
ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺬﺍﺏ ﻭﺛﻼﺛﻮﻥ
ﻳﻘﻮﻣﻮﻧﻪ ﺃﻥ ﻳﺨﻄﺊ
ﻭﻋﺸﺮﺓ ﺃﻣﻼﻙ ﻳﻜﺘﺒﻮﻥ
ﺃﻋﺪﺍﺀﻩ
Ma'ana:
“Wanda ya karanta
Qulhuw Allahu Ahad
qafa dubu a raka'a
goma, ba zai mutu ba
har sai Allah ya aiko
masa da mala'iku guda
dari, guda talatin daga
cikinsu za su yi masa
albishir da aljanna, guda
talatin za su amintar da
shi daga azaba, guda
talatin za su daidaita
shi kada ya yi kuskure a
rayuwarsa, guda goma
kuma za su rubuta
maqiyansa."
– Sheikh Abdulwahhab
Abdullah (Imamu
Ahlissunnati Wa
Jama'ah Kano).

Advertisements