KANA SADA ZUMUNTA ? (Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa)

••••••••DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA•••••••••
••••••••••••••••••••••••
KANA SADA ZUMUNTA ?
1-Allah taala yayi Umarni da sada zumunta.
Suratul bakara 36, Suratul Isra'i 26, Suratul Rum 38, Suratul bakara 210, Suratul Nisa'i 2 .
2- Sada zumunta yana kara tsawon rai, Bukari 5986, Muslum 2557.
3- sada zumunta yana kara arziki, Bukari 5986
4- sada zumunta yana cikin abubuwan da akayi Umarni dashi, tun farkon musulunci, bayan tauhidi, Bukari 7
5- sada zumunta dalili ne na shiga Aljannah, Bukari 5983
6- sada zumunta yana cikin abubuwan da Allah yake so. Sahihut-targib 2/667.
7- sada zumunta yana tseratarwa daga azaba, Abu Dauda
4902
8- sada zumunta wasiyyar da Annabi saw yayi wa Al'ummarsa. Sahihut-targib 2/669
9- Sada zumunta siffar muminai ce.
10 Sada zumunta yana sawa a karfi aikin mutum. Sahihut-targib 2/674
11- sada zumunta yana cikin siffofin masu hankali.
12- Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya dinka sada zumunta,. Bukari da Muslum.
13- Sada zumunta yana kare mutum daga laantar Allah , Tafsir Ibn kasir Suratul Ra'adi,25.
14- Yin Sadaka ga yan uwan zumunta, yana jawo lada biyu, na Sadaka dana zumunta. Sahihu,Sunanil Tirmiziy. 1/202 .
15, Sada zumunta yana kara soyayya tsananin dangi da yan'uwa .
16- Sada zumunta yana kara hadin kai tsananin yan'uwa.
17- Wanda baya sada zumunta bazai shiga Aljannah ba.
18- Allah taala ya yiwa mahaifa alkawari zai sadar da wanda ya sadar da ita, zai yankewa wanda ya yanketa.
19 , mai sada zumunta shine wanda ko baa zo masa ba, shi zai je.
20, Baya cikin sada zumunta sai wanda yazo maka kawai zaka je masa.
2 February at 22:31

DAUKE ABINDA ZAI CUCI MUTANE AKAN HANYA SADAKA NE (Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa)

••••••••DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA•••••••••
••••••••••••••••••••••••
DAUKE ABINDA ZAI CUCI MUTANE AKAN HANYA SADAKA NE
WANI SAHABI YA TAMBAYI MANZON ALLAH SAW, CEWA: NUNA MINI ABINDA ZAI KAINI ALJANNAH, SAI YACE : KA DAUKE ABINDA ZAI CUCI MUTANE DAGA KAN HANYA. MUSLUM YA RUWAITO

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE

••••••••DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA•••••••••
••••••••••••••••••••••••
SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE
Shawarwari 60 ga matan aure domin samun zamantakewa mai inganci, da aure mai albarka, kamar yadda muka Bawa maza suma shawara 60.
1.Ta rike masa amana,
2. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon Allah bane.
3. Ta kula da dukiyarsa
4. Ta kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman lafiya
5. TA girmama shi a gaban idansa
6. TA kare girmansa a bayan idansa
7. Ta so abinda yake so, koda ba abin so bane a wajenta
8. Ta ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane awajenta
9. Ta damu da duk abin da ya damu dashi.
10. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga gareshi
11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi .
12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi
13.Idan ya bata kadan taga yawansa
14.Idan ya bata da yawa tayi godiya
15.Ta farka daga bacci kafin ya farka
16.Sai yayi bacci kafin tayi
17.Tayi hakuri idan yayi fushi
18 Tayi taushi idan yayi tsauri
19.Ta lallashe shi idan ya hasala
20.kada ta nuna raki a gabansa
21.kada tayi kuka alhali yana dariya
22.kada tayi dariya alhali yana kuka
23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu
24.kada ta matsa masa da bukatu
25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida
26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai
27.kada ta dinka kushe tsarinsa
28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta
29.Ta dinka girmama shi a wajen kawayenta
30.Ta dinka nuna masa abu mai kyau
31.Ta dinka boye abu mummuna
32.Idan ya kawo wata damuwa gareta, ta taimake shi ya warware ta
33.Idan ya nuna baya son wani abu ta daina
34.Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa
35.Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki
36.Ta tsaya da jinyar sa idan yana rashin lafiya
37.Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako
38.Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatu
39.Tayi masa rakiya lokacin fita ta tareshi a lokacin da ya dawo
40.Ta tausasa harshe a lokacin da take magana dashi
41.Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta
42.Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge
43.Tayi masa bankwana a lokacin balaguro
44.Tayi ado karshen iyawarta
45.Ta bayyana halaye masu kyau
46.Ishara ta ishi mai hankali ta kula wannan sosai
47.Ta bayyana kanta a matsayin mace
48.Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai
49.Ta cika zuciyarsa da sonta idansa da kwalliyarta
50.Tayi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so
51.Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata mummuna
52.Ta yafe masa idan ya munana mata
53.Ta karbi uzurinsa
54.kada tayi sallar nafila sai ta sanar masa
55.kada ta dau azumi sai ya sani.
56.kada ta fita daga gida sai ya sani.
57.Ta iya girki kala-kala.
58.kazantar jiki ta dade tana kashe aure a kula.
59.kada ta shigar da wani gidansa sai da izni.
60.kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai
Allah ya zaunar damu lafiya da iyalan mu

ABUBUWAN DA ANNABI (SAW) YA NEMI TSARI DA SU. (Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa)

••••••••DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA•••••••••
••••••••••••••••••••••••
ABUBUWAN DA ANNABI (SAW) YA NEMI TSARI DA SU.
WADANNAN ABUBUWA DA SUKAZO A HADISAI ANNABI SAW YA NEMI TSARI DA SU.
1, ZUCIYAR DA BATA TSORAN ALLAH.
2, FITINAR ZUCIYA
3, SHARRIN, JI ,DA GANI
4, TSORO
5, ROWA
6, BAKIN CIKI
7, DAMUWA
8, BACIN RAI
9, HASARA
10, SABON ALLAH
11, KASALA
12, GAJIYAWA
13, KASKANCI
14, KARANCI
15, TALAUCI,
16, FITINAR KABARI,
17, ZUCIYAR DA BATA KOSHI
18, YUNWA
19, CIN AMANA
20, TABEWA
21, MUNAFINCI
22, BASHI
23, FITINAR WADATA
24, FITINAR DUNIYA
25, SHARRIN MAZAKUTA
26, KAFURCI
27, BATA
28, RINJAYAN MAKIYA
29, DARIYAR MAKIYA
30, MUMMMUNAN TSUFA
31, MUMMUNAR HUKUNCI
32, TABEWA A RAYUWA
33, CIWON HAUKA
34, KAMBUN BAKA
35, KASKANCIN RAYUWA
36, KOMAWA BAYA A RAYUWA
37, ADDU'AR WANDA AKA ZALUNTA
38, MUMMMUNAR MAKOMA
39, MUMMUNAN MAKOCI
40, RINJAYAN MAZAJE
41, FITINAR DUJAL
42, AZABAR JAHANNAMA
43, SHARRIN SHEDANUN MUTANE
44, FITINAR RAYUWA
45, FITINAR MUTUWA
46, AZABAR KABARI,
47, SHARRIN ABINDA AKA SANA ANTA.
48, SHARRIN ABINDA AKA AIKATA
49 , SHARRIN ABINDA MUTUM BAIYI BA
50, SHARRIN GIRGIZAR KASA
51, GANGAROWA DAGA TUDU
52, RUSOWAR GINI AKA
53, NEMAN TSARI DA YARDAR ALLAH DAGA FUSHIN SA.
54, NEMAN TSARI DAGA MATSATSIN FILIN ALKIYAMA
55, NEMAN TSARI DAGA ADDU' AR DA BAA AMSAWA.
56, NEMAN TSARI DAGA BUSHEWAR ZUCIYA
57, NEMAN TSARI DAGA RIYA.
58, NEMAN TSARI DAGA FASIKANCI.
59, NEMAN TSARI DAGA JI, DA JIYARWA
60, NEMAN TSARI CIWAN KUTURTA.
61 NEMAN TSARI DAGA HAUKA
62, NEMAN TSARI KURUMTA DA BEBENTA KA.
63, NEMAN TSARI DAGA MUMMUNAN CIWO
64, NEMAN TSARI DAGA KADA KA BATA KO KA BATAR DA WANI
65, NEMAN TSARI DAGA KADA KA ZAME KO A ZAMAR DA KAI.
66, NEMAN TSARI KADA KAZALUNCI WANI KO A ZALUNCEKA
67, NEMAN TSARI DAGA RAI MAI ZARI,
68, NE MAN TSARI DAGA MUMMUNAN MAKOCI.
69, TSARI DAGA MUMMUNAR RANA.
70, TSARI DAGA MUMMUNAN DARE
71, TSARI DAGA MUMMUNAN LOKACI,
72, TSARI DAGA MUMMUNAN ABOKI
73, TSARI DAGA MUMMMUNAN MAKOCI
74, TSARI DAGA YUNWA
75, TSARI DAGA GOBARA.
76 TSARI DAGA DULMIYA A RUWA
77, TSARI DAGA MUMMUNAR CIKAWA
78, TSARI DAGA GUDU A FILIN DAGA
79. NEMAN TSARI DAGA HARBIN KUNAMA
80, TSARI DAGA MUMMUNAN HALI.
81, TSARI DAGA RINJAYAN MIKIYI
82, TSARI DAGA SHIRKA
83, NEMAN TSARI DA KALMOMIN ALLAH DAGA SHARRIN ABINDA YA HALATTA.
84, NEMAN TSARI DAGA GUSHEWAR NIIMAH
85, TSARI DAGA JUYAWA DAGA YANAYI MAI KYAU ZUWA MUMMMUNA
86, DA SAUKAR AZABA
87, DAGA DUKKAN FISHIN ALLAH
88, SHARRIN HARSHE
89, SHARRIN BUSHEWAR ZUCIYA
90, SHARRIN ILMI FARA AMFANI,
91, SHARRIN MASU TSAFI DA SIHIRI
ALLAH YA TSARE MU BAKI DAYAN WADANNAN ABUBUWA, DAN RAHAMAR SA DA JIN KANSA, AMEEN
19 December 2014 at 15:57

IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.? (Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa)

••••••••DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA•••••••••
••••••••••••••••••••••••
IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.?
Manzon Allah saw yace: Imani yana da rassa guda Sitttin bakwai , ko sabain da bakwai, mafi daraja, shine ,Lailaha illalahu, mafi karanta dauke abu mai cutarwa daga hanya, kunya tana daga cikin imani. Muslum ya ruwaito
Malamai sunyi bincike domin gano wadannan rassa, sun wallafa littafai da dama akan haka, abinda suka kawo, daga Alkur'ani mai girma, da ingatattun hadisai, kuma sun gaya mana cewa wadannan rassa sun fito daga aiyukan zuciya, da aiyukan harshe, da aiyukan gabbai, kuma imani yana karuwa yana raguwa.
1- Imani da Allah, shi yayi halitta, shi ya mallaka. shi yake gudanarwa.shi ya cancanci bauta. Da sunayansa da siffofinsa.
2- Imani da Mala'ikun Allah, da siffofin su da aiyukan su, da sunayansu.
3- Imani Da Manzannin Allah swt.
4- Imani da littafan Allah swt,
5- Imani da ranar Lahira.
6- Imani da kaddara mai dadi da mara dadi.
7- Imani da tashi bayan mutuwa
8- Imani da tattaruwa a gaban Allah domin hisabi
9- Imani da Aljannah da Wuta.
10- Kaunar Allah,
11- Tsoran Azabar Allah
12- Kauna juna da Fatan samun rahmar Allah
13- Wajabcin dogaro ga Allah
14- Wajancin Kaunar Manzon Allah saw.
15- Wajabcin girmama Manzon Allah saw.
16- kula da addinin sa da kishinsa.
17- Wajabcin Neman Ilmi.
18- Yada ilmi da koyarwa.
19- Girmama Alkur'ani karatunsa, fassararsa, aiki dashi
20 -wajabcin yin tsarki,na wanka da alwala da taimama.
21- Kula da salloli,biyar akan lokaci.
22- Fitar da zakka, ga wadanda suka cancanta.
23- Azumin Ramadan.
24- Shiga i'itikafi, sunnah ne, yana kara imani
25- Aikin Hajji, sau daya wajibi, komawa sunnah.
26- Jihadin kare addini da yadashi, bisa ilmi.
27- Rashin gudu daga filin daga idan ana yaki.
28 – Bayar da daya bisa biyar, ga abinda mutum ya samu na Rikazi, wato ( tono kudi a kasa)
29- Fitar da kaffara idan ta hau kan mutum, na kisa ko rantsuwa, ko zihari, ko karya azumi da gangan
30- Cikawa da Alkawari idan an dauka.
31- Rikon Amana
32- Godiya ga ni'imar Allah da rashin butulci.
33- Kiyaye harshe, fadin alkhairi ko shiru
34- Tsare kafofin musulunci, kamar (media) wanda ya taba addini a mayar masa da martani.
35- kada mutum ya kashe kansa. Ta ko wacce hanya
36- kamai mutunci,
37- Nisantar cin Haram
38- Tuba daga laifuffuka.
39 Bin sunnah sau da kafa da zuciya
40- Yin aiki da lklasi (ayi aiki don Allah kawai)
41- Hakuri, da rashin zalama
42 – Tausayi da jin kai
43- Tawali'u da kan-kan da kai
44- Zuhdu, gudun duniya, da abin hannun mutane
45- Girmama Manya da tausayawa na kasa.
46- Yawan Addua
47, Yawan Zikri
48, yawan salati ga Annabi saw.
49, Yawan Kyauta da alkhairi
50, Yawan Istigfari
51, sada zumunta
52, Biyayya ga iyaye.
53, Tarbiyyar y'ay'a
54, Kula da hakkin iyali.
55, Biyyaya ga na gaba cikin bin Allah.
56, Tsayar da adalci, ga masoyi da makiyi
57, Yin Sulhu tsakanin Jamaa
58, Umarni da kyakyawa da hani da mummuna
59, Yin Gaskiya
60, Neman kudi ta hanyar halal
61, Yin sallama da amsa sallama
62, Bayan da rancan kudi babu ruwa
63, Girmama bako
64, Amsawa mai atshawa
65, Taimakekiniya wajan aikin alkhairi.
66, Dauke abinda zai cuci mutane daga hanya.
67, ka fifita dan uwanka akanka ko kana da bukata.
Allah ya bamu ikon aikatawa.
11 October 2014 at 05:39

MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ? – SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

••••••••DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA•••••••••
••••••••••••••••••••••••
MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ?
Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda zaa guje musu.
Allah ya bamu ikon kiyayewa.
1- Shirka da kashe-kashenta
2- kisan kai
3 – Tsafi
4- Wasa da sallah
5- Hana zakka
6- Sabawa iyaye
7- Cin riba
8- Cin dukiyar marayu
9- yiwa Annabi saw karya
10- Karya Azumi da gangan
11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini.
12- Yin Zina
13- Shugaba mai hainci ga talakawansa.
14- Shan giya da sarrafata
15- Girman kai da takama da jiji da kai
16- Shedar Zur
17- Luwadi da mdigo
18- Yin kage ga muminai
19- Satar dukiya daga baitul mali
20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba.
21- Sata, da sane.
22- Fashi da makami
23- Rantsuwar karya
24- Yawan karya
25- Wanda ya kashe kansa da gangan
26- Mugun Alkali,
27- Maza masu koyi da mata da Mata masu koyi da maza
28- Masu auran kisan wuta
29- Masu cin mushe da shan jini da alhanzir
30- Rashin tsarki daga fitsari.
31- Masu karbar dukiyar Jamaa babu dalili
32- Munafinci
33- Ha'inci
34- Yin ilmi don duniya da boye ilimi mai amfani
35- Yin gori idan ka yiwa mutum wani alkhairi,.

36- Karyata kaddara
37- magulmaci
38- Mai yawan laantar mutane
39- mayaudari
40- Gasgata bokaye da yan tsibbu
41- Mace mai tsiwa ga mijinta
42- Rashin sada zumunta
43- Sassaka gumaka
44- Annamimanci
45- Kukan mutuwa (yin hawaye babu laifi)
46- Sukan Nasabar mutane, da cin mutunci.
47- Cutar Jamaa, ta kowacce fuska.
48- Kafurta mutane,babu dalilin daga sharia
49- Dunguma ashariya da yawan zage- zage.
50- Zagin waliyai da bayin Allah malamai
51- Jan tufafi a kasa,
52- Sanya tufafin alhariri,
53- Yanka dabba da sunan wani. ba Allah ba.
54- Wanda ya shiga iyakar kasar wani, ko gonar sa ko filinsa.
55- Zagin sahabbai.
56- Mace mai karin gashi.da zane, da yin wushirya da aske gashin gira.
57- Kiran Mutane zuwa ga bata, ko koyar da barna.
58- Wanda yake yiwa dan uwansa barazana da makami.
59- Mai daukan rahoton musulmi yana kaiwa makiyansu.
60- Tauye mudu
61- Jayyaya da musu mara amfani a cikin addini
62- Mutumin da baya jingina kansa ga iyayansa.
63- fidda tsammani daga Rahmar Allah.
64- Camfi
65 – Shan ruwa ko abinci a kofin zinarai.
66- Gaba da juna
67- Butulci
68, Caca
69- Keta alfarmar haramin Macca da Madina.
70 – Cin Zarfin makoci.
ALLAH YA TSARE MU.
9 October 2014 at 08:13·

FALALA ASHIRIN (20) MARABA DA RAMADAN

Mal.Aminu Ibrahim
Daurawa
FALALA ASHIRIN (20)
MARABA DA RAMADAN
1, A cikin sa aka saukar
da Alkurani mai girma,
Bakara 185
2, Dukkan littafan Allah
mai girma, a cikin sa aka
saukar da su, takardun
Annabi Ibrahim a daran
farko na watan,
Attaurar Annabi Musa a
ranar 6 ga watan, Injilar
Annabi Isa 13 ga
watan, Alkur'anin
Annabi Muhammad
saw, a ranar 24 ga
watan, Musnad Ahmad,
shaik Albaniy ya
ingantashi.
3, Ana bude Kofofin
Aljannah a cikin watan,
4, Ana rufe kofofin
wuta
5, Ana daure
kangararrun shedanu
6, Ana bude kofofin
Rahma
7, Ana bude kofofin
sama
8, mai kira yana kira, ya
mai neman alkhairi
gabato, ya mai neman
sharri, kayi nisa
9, A ko wanne dare,
Allah yana yanta bayi
daga wuta
10, A cikin watan akwai
daran lailatul kadri
wanda yafi wata dubu,
11, Ana kankare
zunubin shekara, Annabi
saw yace, Daga
Ramadana Zuwa
Ramadan aka kankare
zanubi duka, mutukar
an nisaci kaba'ira
12, An durmuza hancin,
Duk wanda Ramadana
ya kama har ya wuce
baiyi aikin da zaayi
masa Rahma ba.
13, Umra a cikin watan
Ramadan daidai yake da
aikin hajji tare da
Annabi, saw a wajan
lada.
14, watan da akafi
shiga I'itikaf, a goman
karshe
15, Watan da ake amsa
Addu'a
16, Watan da akeson
yawaita Karatun
Alkur'ani mai girma,
akalla sauka hudu, duk
sati daya.
17,Watan Alkhairi da
kyauta da ciyarwa, da
samun dumbin lada, duk
wanda ya ciyar da mai
azumi, zai kara samun
lada kamar yayi azumi.
18, Watan da akafi
yawan kiyamul laifi da
tarawih da Tahujjud da
Asham, don kara
kusanci da Allah.
19, Watan neman
nasara akan makiya,
Sahabbai sukanyi
amfani da watan
Ramadan, wajan addua
mai tsanani akan
makiya.
20, watan sada
zumunta,da karfafa,
yan uwantaka ta
musulunci,
Allah ka kaimu
Ramadan, da imani da
son Allah da Manzonsa,
Ka karbi ibadun mu ka
yafe mana. Ya Hayyu Ya
Qayyum.

MUHADARA MAI TAKEN WA YA KASHE HUSSAIN?? AUDIO MP3

MUHADARA MAI TAKEN WA YA
KASHE HUSSAIN?? AUDIO MP3 Sheik Aminu Ibrahim Daurawa &
Dr. Abdallah Saleh Pakistan. -Wannan wata Kasaitacciyar
Muhadara ce da aka gabatar a
ranar 17/08/2008 a Masallacin
Kawu Ilya dake Unguwar Brigade a
Yankin karamar Hukumar
Nassarawa a Jihar Kano. -Muhadarar wadda Sheik Aminu
Ibrahim Daurawa Ya Gabatar
sannan Sheik Dr. Abdallah Saleh
Usman Pakistan Yayi masa
Ta'aliki. -Ka daure ka saurari wannan lakca
tana da matukar amfani kwarai
domin ta kunshi Dumbin bayanai
abin sai ka saurara. Muna Addu'ar Allah ya sakawa
wadannan maluma da Al-khairi
ameeen.
DOWNLOAD
•Ga masu matsalar Downloading
sai subi ta wannan link dake kasa:
DOWNLOAD