SAKON KHUDUBAR JUMU’AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE GARIN MADINA

Sheikh Isa Ali
Pantami
SAKON KHUDUBAR
JUMU'AH DAGA
MASALLACIN MANZON
ALLAH (SAW) DAKE
GARIN MADINA DAGA
BAKIN SHEIKH, DR,
IMAM BABA ALIYYU BN
ABDURRAHMAN AL-
HUZHAIFIY (Rahimahul
Laah). JUMU'AH 21/
Rabiul-Awwal/ 1437AH
(1/1/2016CE).
Dattijon Arziki, Dr
Huzhaifiy (Hafizhahul
Laah) yayi khudubar
akan "DARAJAR
ADDU'AH DA
MATSAYINTA GA
MUSULMI."
1) Imam ya fara
khuduba da yabo ga
Allah (SWT) da Salati ga
Annabi (SAW) da
adduar alheri ga
Sahabbai (RH) da sauran
Salihan bayi.
2) Sannan yayi
wasiyyar Taqawah ga
Musulmai, cewa ita
taqawah ribar rayuwa
dukka ya tattara gare
ta ne.
3) Allah ya kaddara
dukkan alheri yana da
sababin aukuwarsa,
haka kuma kuma
dukkan sharri yana da
dalilan faruwarsa. Wajibi
ne muyi riko da dalilan
alheri, kuma mu nisanci
dalilan aukuwar sharri.
4) Duk wanda yayi riko
da alheri da kuma
hanyoyin alheri na
Duniya da Lahira, Allah
zai saka masa da
Aljannah. Allah (SWT)
yana cewa: Shin akwai
sakamakon alheri in ba
alheri ba? Maanarsa duk
wanda ya aikata alheri,
Allah zai saka masa da
alherin Duniya da lahira.
5) Addu'ah tana da
amfani cikin dukka abun
da ya faru ga Mutum a
rayuwa, da cikin dukkan
abunda bai faru ba.
6) Dalilan da ke kawo
wa mutum gyaruwa,
da rabautuwa, da
nagarta shine "Adduah
bil Ikhlas" wato yin
addu'ah da tsarkake
zuciya a cikinta.
7) Lalle Allah yace mu
roke Shi zai amsa mana.
Allah yana cewa a cikin
Qur'ani: "…Ku roke Ni zan
amsa muku. Lalle ne
wadanda suka yi
girman kai daga yimin
ibadah (addu'ah) zasu
shiga Jahannama…"
8) Annabi (SAW) yana
cewa: addu'ah itace
ibadah. (Abu-Daud da
Tirmizhiy suka ruwaito)
.
9) Allah ya karantar da
mu adduah, idan ba dan
ya koya mana ba, da
bamu iya ba.
10) Babu lokacin da
Musulmai ke bukatar
addu'ah kamar wannan
zamani na FITINTINU.
Zamani ne da musifu
suka yi yawa a Duniya.
Zamani da MUNANAN
AQIDU, MASU BATAR
DA JAMA'AH SUKA
YAWAITA. Zamani da
KAFURAI suka yi
chaaaaa akan Musulmai.
11) Wannan zamani
dole mu dage da
adduah. Domin shine
zamanin da Allah yake
cewa: "Wallahi zamu
jarrabeku da wani abu
na tsoro, da yunwa, da
tauyewan dukiyoyi da
rayuka. Amma kayi
bushara ga masu
hakuri."
12) Annabi (SAW) ya
karantar da mu addu'ar
Yunus (AS) na cewa:
Laa'ilaha illa Anta,
subhaaanaKa inni kuntu
minaz Zhalimin."
Annabinmu yace: babu
musulmin da zai yi
addu'ah da wannan
addu'ah face Allah ya
amsa ma sa.
13) Adduah tana saukar
da ALBARKA a rayuwa
kuma tana bada kariya
daga sharri. Kamar
yadda Allah ya amsa
addu'ar Annabi Ayyub
(AS) ya ba shi waraka
daga cuta.
14) Zuwan Dujal shine
mafi girman fitina da
Duniya ke fustanka.
Amma duk da haka
addu'ah tana
taimakawa wajen
samun tsira daga
fitintinun Dujal din.
15) addu'ar da Annabi
(SAW) yayi wa
Sahabbansa (RA) a
Badar na daga cikin
dalilin NASARAR
MUSULMAI A DUNIYA.
Wannan Nasara kuma
har zuwa ranar
Kiyaamah.
ADDU'AH TANA DA
SHARUDDA DA YAWA.
DAGA CIKINSU AKWAI:
16) CIN HALAL yana
daga cikin sharuddan
karban addu'ah. Kamar
yadda Annabi (SAW) ya
karantar da Sa'ad Bn
Abi Waqqas (RA).
17) RIKO DA SUNNAH
yana daga cikin
sharuddan karban
addu'ah.
18) Duk wanda aka
zalunce shi, Allah yana
amsa addu'ar sa, ko da
KAFURI ne, ko da DAN
BIDI'AH ne, Allah yana
amsa addu'ar su idan an
ZALUNCE SU.
19) Ikhlasi shima
sharadin amsa addu'ah
ne.
20) Yabon Allah lokacin
adduar.
21) Rashin gaggawa
lokacin adduah.
22) Dauwama kan yin
adduah shima sharadin
karban adduah ne.
AKWAI LOKUTAN
KARBAN ADDUAH SUNE:
23) Sulusin dare na
karshe. Wato ka shi
daya na ukun dare na
karshe.
24) Tsakanin kiran
Sallah da ta da iqamah.
25) bayan kammala
saukan karatun Qur'ani.
26) Lokacin ganin
Ka'abah.
27) lokacin ba da
Sadaqa.
28) Lokacin saukan
ruwan sama.
29) sannan haramun ne
yin adduah ta hanyar
rokon matattu.
30) Duk wanda yayi wa
Allah tarayya da wani a
cikin adduah, kuma ya
daidai Allah da waninSa
lalle yayi SHIRKA MAI
GIRMA.
RUFEWA:
31) Babban limamin yayi
Salati ga Annabi (SAW)
da salatin Ibraahimiyya.
32) Adduah da Sahabbai
da Tabi'ai da wanda
suka biyo bayansu da
kyautatawa.
33) Adduah ta
Musamman ga
Alkhulaafu Arrashidun,
Abubakar da Umar da
Uthman da Aliyyu
(Radhiyallahu anhum),
Allah ya kara yarda da
su.
34) Yayi Adduar neman
gafara ga Matattunmu
gaba daya, Allah ya
gafarta musu.
35) Yayi Addu'ah ga
marassa lafiya, Allah ya
basu lafiya.
36) Yayi Allah ya karya
Azzuluman da ke kashe
bayin Allah a kasar
Sham.
37) Yaa Allah ka taimaki
addininKa.
38) Yayi addu'ar Yaa
Allah ka datar da
"Khaadimul Haramayn"
ga duk abun da Ka ke
so, kuma ka yar da da
shi.
39) Allah ka bamu ruwa
mai albarka.
Fassarawa: Isa Ali
Ibrahim Pantami
(21/03/1437AH. Kai
tsaye daga Haramin
Madinah).
Yaa Allah ka bamu ikon
aiki da khudubar da
darussa da ke cikinta,
kuma ka amsa mana
addu'o'inmu,…

YIN MURNAR SABUWAR SHEKARA, MUSAMMAN TA KIRISTOCI BA TA DA ASALI! (Sheikh Isa Ali Pantami)

YIN MURNAR SABUWAR
SHEKARA, MUSAMMAN
TA KIRISTOCI BA TA
DA ASALI! (Sheikh Isa Ali
Pantami)

YIN MURNAR SABUWAR
SHEKARA, MUSAMMAN
TA KIRISTOCI BA TA
DA ASALI!
Manzon Allah (SAW)
yana cewa: "Yana daga
kyawun Musuluncin
Mutum, ya bar abun da
bai shafe shi ba.
” [Sunan al-Tirmidhî and
Sunan Ibn Mâjah]. Yaa
Allah ka bamu ikon
tsayawa akan Sunnah,…
ENGLISH: a Muslim
doesn't celebrate the
new year, particularly
gregorian calendar.
Allah’s Messenger
(SAW) says: “From the
perfection of a person’s
Islam is his leaving
alone what does not
concern him."
May Allah guide us to be
consistent in following
the teachings of the
Prophet,…

MUHIMMANCIN KARANTA “AMANAR- RASUL” LOKACIN KWANCIYA – Sheikh Isa Ali Pantami

Sheikh Isa Ali
Pantami
MUHIMMANCIN
KARANTA "AMANAR-
RASUL" LOKACIN
KWANCIYA: Yaa Allah ka
sa mu wanye lafiya,…
Annabi (SAW) yana
cewa: Duk wanda ya
karanta ayoyi biyu
(Amanar-RASUL) na
karshen Suratul-
Baqarah lokacin
kwanciya sun wadatar
masa- daga Komai da
Komai (Bukhari ya
riwaito a Hadith 5009).
Yaa Allah ka bamu ikon
karantawa, kuma ka
wadatar mana daga
dukkan abunda yake
gabanmu a rayuwa,…

Sheikh Isa Ali Pantami SAKON KHUDBAH DAGA MASALLACIN ANNABI (SAW) DAGA BAKIN SHAYKH DR HUSAIN BN ABDUL’AZIZ ALUSH- SHAYKH (HafizahulLaah)

Sheikh Isa Ali
Pantami
SAKON KHUDBAH DAGA
MASALLACIN ANNABI
(SAW) DAGA BAKIN
SHAYKH DR HUSAIN BN
ABDUL'AZIZ ALUSH-
SHAYKH (HafizahulLaah)
.
Bil hakika na saurari
Qhudbah mai ratsa jiki
da tasiri a zuciyar mai
yin Khudbar, kuma mai
tasiri a zukatan masu
sauraro a Masallacin
Fiyayyen Halitta (SAW).
Gaskiya khudbar na da
tsawo sosai, amma ga
dan kadan daga cikin
ma'anar ta.
1) Wasiyyar Allah ga
bayinSa shine muyi
taqawa zuwa gare Shi,
sannan mu bauta ma
sa SHI kadai.
2) Dukkan al'ummar da
su kayi wa Allah da
ManzonSa biyayya suna
samun rayuwa mai
da'di da kuma taimakon
Allah.
3) Dukkan wanda suka
juyawa dokokin Allah da
ManzonSa suna shiga
rayuwa mai 'kunci da
tsanani da 'kas'kanci.
4) Annabi (SAW) da
Sahabbansa (RA) sun yi
imani da Allah da
ayyuka masu Nagarta,
wannan ya basu nasara
da kuma taimako daga
gun Allah (SWT).
5) Mafiya yawan 'kunci
da kaskanci da tsanani
da al'ummah ta fad'a
ciki, sa'bon Allah ne ya
kai al'ummah. Domin
dukkan al'ummar da ta
yi watsi da taimakon
addini ta shagaltu da
neman Duniya kadai,
Allah yana 'dora ma ta
kaskanci. Don haka
masu neman canji dole
suyi biyayya ga Allah.
LIMAMIN YAYI ADDU'O'I
KAMAR HAKA:
1) Yaa Allah ka gyara
halayen Musulmai a
Duniya.
2) Yaa Allah duk wanda
aka ba shi jagorancin
al'ummah sai ya
tausasa mu su, Yaa
Allah ka tausasa ma sa.
Yaa Allah duk wanda
aka ba shi Jagorancin
al'ummah sannan ya
tsananta musu, Yaa
Allah ka tsananta
masa.
3) Yaa Allah ka shayar
da mu ruwan sama mai
albarka.
4) Yaa Allah ka
magance mana
damuwowin mu.
5) Yaa Allah ka amintar
da mu,…
Wannan shine sakon a
takaice. Muna addu'ar
Allah ka kar'bi wannan
addu'o'in kuma ka bamu
ikon aikin da sa'kon
khudbar,…

DON ALLAH! DON ALLAH!! DON ALLAH MUYI BIYAYYA GA WANNAN HADISAN NA MANZON ALLAH (SAW) MUSAMMAN A SOCIAL MEDIA!!! (Sheikh Isa Ali Pantami )

Sheikh Isa Ali
Pantami
DON ALLAH! DON
ALLAH!! DON ALLAH
MUYI BIYAYYA GA
WANNAN HADISAN NA
MANZON ALLAH (SAW)
MUSAMMAN A SOCIAL
MEDIA!!!
Annabi (SAW) yana
cewa: Duk wanda yake
Imani da Allah da ranar
Kiyaama, ya fadi alheri
ko kuma yayi shiru
(Bukhari da Muslim).
Annabi (SAW) yana
cewa: Duk wanda ya
lamunce min abunda ke
tsakanin habarsa biyu
(Harshensa kenan), da
abunda ke tsakanin
cinyoyinsa biyu (al'aura),
na lamunce masa
Aljannah (Bukhari 8:481)
Muna cikin jarrabawa da
yawa a arewacin
Nigeria, amma mun
shagalta da surutun da
bai da fa'ida wajen
samun mafita
completely, Don Allah
duk mai Magana ya fadi
alheri ko kuwa yayi
shiru. Akwai alheri cikin
'karancin Magana,…
Yaa Allah ka bamu
aminci, da zaman lafiya
da adalci a Nigeria,…

RAYUWAR MUMINI A LOKACIN FITINTUN – SHEIK ISA PANTAMI HAFIZAHULLAH

Sheikh Isa Ali
Pantami
RAYUWAR MUMINI A
LOKACIN FITINTINU
Malaman Sunnah (RH)
sun karantar da mu
wasu muhimman
darussa a lokacin
fitintinu. Duba littafin
"al-'Awaasim min al-
Fitan." Wadannan
abubuwa dole muyi ri'ko
da su. Gasu kamar haka:
1) cikakkiyar biyayya
zuwa ga Qur'ani da
Sunnah bisa ga
fahimtar Magabata (RH)
gabannin yin ko wace
magana ko aiki ko
rubutu ko hukunci.
2) Yin addua gadan-
gadan da ikhlasi. Ya
tabbata a Sunnah cewa
ana addu'ah a lokacin
fitintinu da cewa:
"Allahumma Innaa
Na'uzu bi Ka minal Fitan
maa Zahara min ha, wa
maa badan."
3) Nisantar wajen
fitintinu. Sunnah ta
karantar da cewa
"wanda ya Zauna a
lokaci fitina yafi wanda
ya tsaya, haka kuma
wanda ya tsaya yafi
wanda ya tafi zuwa
gare ta. Don haka ana
nisantar wajen fitina.
4) kaucewa Jita-jita a
lokacin fitina wajibi ne.
Wajibi ne duk labarin da
Musulmi ya ji, ya bincika
ya tabbatar gabannin
ya isar da shi gaba.
Haka Qur'ani ya mana
wasiyya da aikatawa.
5) Tausasawa cikin
hukunci da ayyuka bisa
ga Manhajin Manzon
Allah (SAW). Domin
Annabi yace:
"Tausasawa idan ya
shiga al'amari yana
kyautata shi. Idan
kuma aka cire shi a cikin
lamari, lalle lamarin yana
lalacewa. (sahih Muslim)
.
6) Kusantar Malaman
Sunnah, Shugabanni na
kwarai da dukkan
Salihan bayi. Domin sune
fitilu na al'ummah.
Annabi (SAW) yana
cewa: "Lalle a cikin
mutane akwai wanda
suke masu bude alheri
da kulle sharri."(Bukhari).
7) Yin Nasiha ga kowa
da kowa kan komawa
ga Allah da kuma kiyaye
amanar da ke wuyan
kowa. Saboda kowa
mai kiwo ne, kuma
Allah zai tambaye shi
kan kiwo da ya dora
masa.
Yaa Allah kabawa
Nigeria da salihan
Musulmai da Sunnar
Annabi (SAW) mafita
daga wadannan
jarrabawa,…
Yaa Allah ka shiryar da
Shugabanni zuwa ga
abun da ka yadda da shi
kuma ka ke 'kaunarsa,…
Isa Ali Pantami, PhD
2/Rabiul-Awwal/
1437AH