SHIA BA ADDININ MUSULUNCI BACE KAFIRCI NE TSANTSA: INJI YAKUBU YAHAYA KATSINA

SHIA BA ADDININ MUSULUNCI BACE
KAFIRCI NE TSANTSA: INJI YAKUBU
YAHAYA KATSINA
Hujja Takobin Ahlul Sunnah ba ma karya
ba ma yarfe sai dai muna fadin abinda
mutun ya fadi da bakin shi. Wannan Lecture ce da Yakubu Yahayya
yayi bayan dawowar shi daga Iran kuma
wannan shine a zuciyarshi Shi’a ba
Musulunci bane amma yayi maku halin
naku na munafurci wato TAKIYYA.
Shi yasa lokacin da Zakzaky yasa yaran shi sukai ma Atullahi Burtai rashin kunya
yaki zuwa Zaria lokacin hasalima ya tafi
amma da yaji linzami yafi karfin bakin
kaza sai ya dawo yaki ya ida isa.
Haka lokacin da aka kuresu daga
Masallacin Masarauta sai ya dauke ma mabiyan shi zuwa Sallar Juma’a.
Jiya kuma mun sanya ido domin muga
Malam ya fito domin zagayen Ashura
amma shiru kamar mushiriki yaci shurwa.
Duk wanda ya saurari wannan lecture da
ya gabatar yasan Malam yasan aikin banza ne suke dan haka ba zai yarda ba
yakai kanshi ga mutuwar asara.
Latsa wannan link blue domin
downloading
Ku saurara kuji Da kunnuwan Basira http://www.hausaloaded.com/2018/02/
audio-shia-ba-addinin-musulunci-
bace.html Allah ya kara shiryamu shiri na Musulunci

Advertisements

Littattafan ’yan darika ke kafirta su ba ’yan Izala ba – Sheikh Ahmadu Maidankoko

Sheikh Ahmadu Maidankoko sanannen
malami ne musamman a Kudancin kasar
nan. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce
littattafan ’yan darikar Tijjaniyya ne suke
kafirta su ba ’yan Izala ba, inda ya yi kira
ga ’yan darikar su koma ga sahihiyar akida ta Musulunci kamar yadda aka
saukar wa Annabi (SAW): Aminiya: Allah gafarta Malam ka ce kana da jan hankali ga al’ummar
Musumia kan mene ne?
Sheikh Mai dankoko: Bismillahir rahmanir
rahim. Wa sallallahu alan nabiyyil karim.
To abin da nake so na ja hankalin
Musulmi a halin yanzu shi ne, a gaskiya Musulmi sun saki hanya, ba sa yin
addinin nan kamar yadda aka saukar da
shi. Ya kamata su kama sahihiyar hanya
ta koyarwar Annabi Muhammadu (SAW)
kamar yadda aka saukar masa kuma ya
bar mana. Aminiya: Ka gano ana yin wani abu ne da
ba daidai ba ya sa kake cewa a koma kan
daidai?
Sheikh Mai dankoko: Eh, a zahirin
gaskiya ya kamata Musulmi na gaskiya
su bar bin wasu hanyoyi na wasu shaihunnai na darika, alhali kuma su
shaihunnan nan ba wahayi aka yi musu
ba. Babu wanda ake yi wa wahayi sai
Annabi kuma Annabi Muhammadu (SAW)
shi ne karshen Annabawa kuma a
karshen rayuwarsa aya ta sauka cewa addinin nan ya kammala, ba wani da
Allah zai sake aikowa da sako.
Wadannan shaihunnai ba su zo da komai
ba, kawai so suke su daukaka kansu su
azzama kansu, suna fada wa jahilan
mutane cewa su ne wani abu, idan an bi su za a yi kudi, kuma idan an bi su za a
samu gafara ko idan ka gan su Allah Ya
gafarta maka, idan an gan su za a shiga
Aljanna. Wallahil azimu karya suke yi.
Aminiya: Shaihunnan darika da kake nufi
na da ne ko na yanzu? Sheikh Mai dankoko: Shaihunnan darika
da na da da na yanzu duk aikinsu ke nan,
idan ba haka ba ina hujjar da mutum zai
ce Annabi ya dawo duniya bayan ya
shekara dubu daya da dari daya da
hamsin da barin duniya? A ce Shehu Tijjani ya ce ya ga Manzon Allah (SAW),
ya zauna sun yi hira da Manzon Allah
(SAW), har Manzon Allah (SAW) ya ce
masa Salatul Fatihi kafa daya ta fi saukar
Alkur’ani sau dubu shida.
Wai kuma a zahiri ba a mafarki ba, ga shi ga Annabi (SAW), yana yi wa Manzon
Allah (SAW) tambayoyi, Manzon Allah
(SAW) yana ba shi amsa. Duk wani shaihi
ko na ina ne a nan duniya, ko na Najeriya
ko na Kaulaha na kalubalance shi ya
kawo hujja idan ba a rubuta haka ba a cikin littattafansu ba. Wannan haka yake
a rubuce a cikin littafinsu mai suna
Jawahirul Ma’ani. Idan Manzon Allah
(SAW) zai dawo duniya ya fadi wata
magana babu wanda zai fadawa sai
sahibinsa Abubakar Siddiku da Umar da Usman da Aliyu (RA).
Idan aka duba cikin littafinsu na
Jawahirul Ma’ani shafi na 137, mai
Salatul Fatihi cewa ya yi saukar masa da
ita aka yi, bayan ya shiga cikin Ka’aba ya
shafe shekara 40 yana ibada a ciki, yana rokon Allah Ya ba shi salatin da ta fi
kowace, ta fi Alkur’ani, ta fi duk abin da
Manzon Allah (SAW) ya fada a duniya.
Sannan ya ce sai Mala’ika ya zo masa da
ita Salatul Fatihi a cikin takardar haske.
Ka ga wahayi ke nan kuma ba a yi wa wani mutum wahayi bayan Manzon Allah
(SAW). Kuma mene ne matsayin
mutumin da ya ce ya roki Allah Ya ba shi
abin da ya fi Alkur’ani ya fi abin da
Manzon Allah ya zo da shi ko ya fada?
Aminiya: Malam kana nufin ba a kan daidai suke ba ke nan duk tsawon
shekarun nan har da wadanda suka
rasu?
Sheikh Mai dankoko: Wallahi wadanda
suka riga mu gidan gaskiya ina rokon
Allah Ya gafarta musu, domin Allah bai sa sun yi bincike sun gane ba ko kuma ba
su ga wadannan littattafai ba. Duk wanda
ya yi bincike a cikin Alkur’ani ba zai taba
yarda cewa ga wani mutum ya shiga
Ka’aba ya zauna kwana arba’in wanda
Annabi Ibrahim bai yi ba, haka dansa Annabi Isma’ila da suka gina Ka’aba tare
bai yi haka ba. Haka Annabi Muhammad
(SAW) bai taba shiga Ka’aba ya kwana
20 ba, ko goma ko bakwai. Sannan wani
mutum da ba Annabi ba, ba Manzo ba, ya
yi haka kuma a yarda? Sannan an ce duk wanda ya karanta wannan salati sau
daya tak an ba shi ladan saukar Alkur’ani
fiye da sau dubu shida, wato an kaskanta
Alkur’ani ke nan. Idan sun ce wannan
sufanci ne, an taba jin Sayyadina
Abubakar ko Abu Huraira ya ce ga wani abu idan an karanta shi ya fi a sauke
Alkur’ani sau dubu shida? A nuna mana a
ina takardar hasken take. Na kalubalanci
duk wani malami a Najeriya. Billahillazi la
Ilaha illa huwa idan ya kawo takardar
hasken nan na ba shi gidana. Aminiya: To idan ka ce haka, daga ina
darika ta samo asali?
Sheikh Mai dankoko: Wannan akidar ba
daga Musulunci take ba, ta Yahudawa
ce. Yahudawa su dama bukatarsu kurum
su rushe addinin Allah. A cikin sahabban Annabi (SAW) da tabi’ina da tabi’it
tabi’ina babu wanda ya taba fadar irin
wannan kalma cewa Annabi (SAW) ya
fada masa. Annabi ya ce duk wanda ya
aikata wani aiki da babu umarninsa ko na
Allah to wannan aikin ba karbabbe ba ne a wurin Allah. Ina kira ga shaihunnan
darikar Tijjaniyya da mukaddamansu da
muridansu su tuba ga Allah su daina yin
abin da suke yi, sun bar koyarwar
Manzon Allah.
Kuma akwai wasu maganganu biyu da Shehu Tijjani ya yi da nake so a fada
kowa ya ji. A cikin littafinsa Yakutatul
Faridah, ya ce zai shigar da mabiyansa
cikin Aljanna ba tare da an yi musu hisabi
ko azaba ba. Kuma ya ce ko ka yi zunubin
duk duniyar nan zai shigar da kai Aljanna. Manzon Allah (SAW) ya taba
fadar haka?
Aminiya: Ba ka jin ko yana da wata
fassara ta daban?
Sheikh Mai dankoko: Babu wata fassara
wacce za mu yarda da ita da ta shige wacce take cikin Alkur’ani. Na biyu kuma
Shehu Tijjani ya ce shi Annabi ne, ya
fada ya ce shi yana cikin Annabawa har
ma yana da matsayi na Annabi arba’in.
Idan ko wani zai ce ko almajirinsa ne ya
rubuta, to, me ya sa da ya gani bai yi magana ba? Don haka irin wadannan
abubuwa da ke cikin littattafansu ne ke
kafirta duk wanda ya yarda da su, ba ’yan
Izala ke kafirta su ba. Su fito su ce
wadannan abubuwa kuskure ne sun
barranta daga gare su mana. Martanin da na yi wa Sheikh dahiru Bauchi a
kwanakin baya kuwa a cikn jarida har
yanzu ya kasa ba ni amsa. Ka je ka duba
jaridar ka gani mana. Kuma a kan irin
wannan bayanin na yi masa.

KHALIFOFI 12 DA ANNABI (SAW) YA BA DA LABARINSU MASU MULKI AKE NUFI BA MARASA MULKI BA

KHALIFOFI 12 DA ANNABI (SAW) YA BA
DA LABARINSU MASU MULKI AKE NUFI
BA MARASA MULKI BA
HADISIN KHALIFOFI 12 HADISI NE DA
YA ZAMA BABBAR SHUBUHA GA
RAFIDHA ‘YAN SHI’A, HAR MA SABODA SHI NE AKA SAMU SHI’A IMAMIYYA
ISNA ASHARIYYA, WATO SHI’A MASU
DA’AWAR BIN IMAMAI 12. AMMA IN KA
TAMBAYESU INA DALILI A KAN
WA’DANNAN IMAMAI 12 NAKU?
SAI SU AMBATA MAKA WANNAN HADISI NA JABIR BN SAMURA (RA)
WANDA BUKHARI DA MUSLIM SUKA
RUWAITO SHI KAMAR HAKA:
ANNABI (SAW) YA CE:
«ﻻ ﻳﺰﺍﻝ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻋﺰﻳﺰﺍ ﻣﻨﻴﻌﺎ ﺇﻟﻰ ﺍﺛﻨﻲ ﻋﺸﺮ ﺧﻠﻴﻔﺔ « ، ﻓﻘﺎﻝ ﻛﻠﻤﺔ ﺻﻤﻨﻴﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ، ﻓﻘﻠﺖ ﻷﺑﻲ : ﻣﺎ ﻗﺎﻝ؟ ﻗﺎﻝ : » ﻛﻠﻬﻢ ﻣﻦ ﻗﺮﻳﺶ » “WANNAN ADDINI BA ZAI GUSHE BA
YANA DA IZZA DA KARIYA HAR ZUWA A
SAMU KHALIFOFI GOMA SHA BIYU
(12)”, SAI YA FA’DI WATA KALMA DA
MUTANE SUKA KURMANTAR DA NI
DAGA GARETA, SAI NA CE WA BABANA: ME YA CE: SAI YA CE:
“DUKKANSU DAGA QURAISHAWA
SUKE”.
WANNAN HADISI YANA NUNI NE GA
TSAWON LOKACIN DA ADDINI ZAI
ZAMA MAI K’ARFI DA ‘DAUKAKA, SHI NE A LOKACIN MULKI KHALIFOFI GUDA 12,
A BAYANSA.
TO, IN MUN DUBA TARIHI ZA MU GA
LOKACIN DA MUSLUNCI YA FI K’ARFI
DA ‘DAUKAKA SHI NE ZAMANIN
KHALIFANCIN WA’DANNAN KHALIFOFI QURAISHAWA MASU ZUWA KAMAR
HAKA:
1 – ABUBAKAR AL- SIDDIQ (RA).
2 – UMAR AL- FARUQ (RA).
3 – USMAN BIN AFFAN (RA).
4 – ALIYU BIN ABI DALIB (RA). 5 – MU’AWIYA BIN ABI SUFYAN (RA).
6 – YAZEEDU BIN MU’AWIYA (RH).
7 – ABDULMALIK BIN MARWAN (RH).
8 – AL- WALEED BIN ABDILMALIK (RH).
9 – SULAIMAN BIN ABDILMALIK (RH).
10 – UMAR BIN ABDIL’AZEEZ (RH). 11 – YAZEED BIN ABDILMALIK (RH).
12 – HISHAM BIN ABDILMALIK (RH).
WA’DANNAN SU NE KHALIFOFIN DA
ADDINI YA ZAMA MAI K’ARFI DA IZZA A
ZAMANINSU, WANDA HAR SAI DA
FA’DIN DAULAR MUSLUNCI YA ISA TA GABAS TUN DAGA CHINA HAR ZUWA
FARANSA TA YAMMA A ZAMANIN
HISHAM BN ABDILMALIK (RA), AMMA
KUMA TUN DAGA BAYAN RASUWARSA
DAULAR MUSLUNCI TA FARA KOMAWA
BAYA, HAR ABIN YA LALACE. KUMA DUKKANSU WA’DANNAN
KHALIFOFI 12 QURAISHAWA NE.
SABODA HAKA WA’DANNAN AKE NUFI
A CIKIN HADISIN, SABODA DUKA SUN
YI KHALIFANCI, NA SHUGABANCI DA
MULKI, SABODA DA MA KHALIFOFI MASU MULKI AKE AKE NUFI, BA
KHALIFOFI MARASA MULKI BA.
DALILI A KAN HAKA SHI NE; ABIN DA
BABBAN MALAMIN SHI’A ABU JA’AFAR
AL- SADUK, MUH’D BN ALIY BN
BABAWAIHI AL- QUMIIY YA RUWAITO DA ISNADINSA KAMAR HAKA: ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﻘﻄﺎﻥ ﻗﺎﻝ : ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺑﻮ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﻠﻰ ﺑﻦ ﺍﺳﻤﺎﻋﻴﻞ ﺍﻟﻤﺮﻭﺯﻯ ﺑﺎﻟﺮﻯ ﻗﺎﻝ : ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﻟﻔﻀﻞ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺠﺒﺎﺭ ﺍﻟﻤﺮﻭﺯﻯ ﻗﺎﻝ : ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﻠﻰ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻳﻌﻨﻰ ﺍﺑﻦ ﺷﻘﻴﻖ ﻗﺎﻝ : ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺑﻦ ﻭﺍﻗﺪ ﻗﺎﻝ : ﺣﺪﺛﻨﻲ ﺳﻤﺎﻙ ﺑﻦ ﺣﺮﺏ ﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﺳﻤﺮﻩ ﻗﺎﻝ : ﺍﺗﻴﺖ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻓﺴﻤﻌﺘﻪ ﻳﻘﻮﻝ : ﺍﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻻﻣﺮ ﻟﻦ ﻳﻨﻘﻀﻰ ﺣﺘﻰ ﻳﻤﻠﻚ ﺍﺛﻨﺎ ﻋﺸﺮ ﺧﻠﻴﻔﻪ ﻓﻘﺎﻝ ﻛﻠﻤﻪ ﺧﻔﻴﻪ ﻓﻘﻠﺖ ﻻﺑﻲ : ﻣﺎ ﻗﺎﻝ؟ ﻓﻘﺎﻝ : ﻗﺎﻝ : ﻛﻠﻬﻢ ﻗﺮﻳﺶ . ﺍﻟﺨﺼﺎﻝ – ) 485 / 1 ( ، ﻋﻴﻮﻥ ﺃﺧﺒﺎﺭ ﺍﻟﺮﺿﺎ ) ﻉ ( ) / 2
51)
A TASA RIWAYAR SAI YA CE:
ﺍﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻻﻣﺮ ﻟﻦ ﻳﻨﻘﻀﻰ ﺣﺘﻰ ﻳﻤﻠﻚ ﺍﺛﻨﺎ ﻋﺸﺮ ﺧﻠﻴﻔﻪ
“WANNAN AL’AMARI BA ZAI GUSHE BA
HAR SAI KHALIFOFI GUDA 12 SUN YI MULKI”.
* KA LURA DA KYAU, CEWA YA YI:
ﺣﺘﻰ ﻳﻤﻠﻚ
“HAR SAI SUN YI MULKI”.
SABODA HAKA MU ABIN DA MUKE
TAMBAYA ‘YAN SHI’A SHI NE; MUN SAN CEWA RAFIDA ‘YAN SHI’A SUNA KAFA
HUJJA DA WANNAN HADISIN A KAN
IMAMANSU 12 DA SUKA YI IMANI DA
SU, TO SHIN A CIKIN IMAMAN SHI’A
GUDA 12, SU WANENE SUKA YI
SHUGABANCI NA MULKI??! IN MUN DUBA ZA MU GA CEWA; ALIYU
(RA) NE KAWAI YA YI MULKI, SAI
‘DANSA HASSAN (RA), SHI MA BA
CIKAKKEN MULKI YA YI BA.
DON HAKA SU SHI’A KHALIFOFI SUKE
DA SHI KO KUMA IMAMAI??! IN IMAMAI 12 NE, TO INA DALILI A KAN
WA’DANNAN IMAMAI NAKU GUDA 12, A
INA KUKA SAMOSU??!

SUMA AHLUL- BAITI NE DOMIN ANNABI MUHAMMAD(S.A.W)YA HAIFE SU

SUMA AHLUL- BAITI NE DOMIN ANNABI MUHAMMAD(S.A.W)YA HAIFE SU
.
Via:-Garkuwan Magabata
.
A duk lokacin da ya’yan yan shi’a jebberiyya ko zakzakiyya suka tashi yin magana zaka ji suna cewa wai ahlulsunnah basa son ahlul baiti, amma yanzu zamu gani idan da gaske ne, yan uwa mu karanta wannan.
Dan uwa musulmi ko kasan ya’ya
nawa ne Allah(s.w)ya baiwa Annabi muhammad
(s.a.w) a rayuwarsa ta duniya? To idan baka
sani ba yana da ya’ya guda bakwai (7) ga su
kamar haka:-
1.Zainab r.a
2.Rukayya r.a
3.Ummu khulsum r.a
4.Fadima r.a
5.Abdullah r.a
6.Al-kasim r.a
7.Ibrahim r.a
Wadan nan
sune ya’yansa,shidda(6) daga cikinsu duk diyan nana
khadija r.a ne,ibrahim ne kawai a dan mariya
r.a.To ya yan shi’a basa maganarsu? Bari kuji
abinda yasa basa maganarsu,zainab r.a ta aure
wani dan qabilar banu umaiyya mai suna Abu
al-as dan rabi’i.Rukayya kuma ta aure usman
ibn affan r.a na ukku daga khulafa’u rashideen kuma shima daga banu qabilar umaiyya ne.
Ummu khulsum itama ta aure usman ibn affan r.a
bayan yar uwarta rukayya a.s ta rasu. Fadima r.a
ta aure sayidina Aliyu r.a.Amma su yan shi’a
sai suka dauke fadima r.a cewa ita kadai ce a
diyar annabi sallallahu alaihi wasallam,da hakane jahillai suke daukar
cewa fadima ce kawai a diyarsa,kuma sai aka yi
dai dai da koda annabi s.a.w yayi wafati
fadima ce kawai a raye.da haka ne jahillai a
basu iya gane cewa yan shi’a karya ce suke
yi.don haka muna kira da ayi soyayya da ya’yan
annabi(s.a.w) baki dayansu babu wariya daga daya
daga cikinsu. Hakama a janibin sahabbai(r.a)bamu ware ko daya daga cikinsu,Don haka mu ahlulsunnah bamu
ware daya daga cikin Ahlul baiti ko sahabbai muce bamu sonsa.
kuma bamu sukar ko mutun daya daga
cikinsu, asalima duk muna sonsu(ahlul baiti da sahabbai) baki daya wannan itace hanyar gaskiya.Amma
hanyar da yan shi’a zakzakiyya da jebberiyya suka dauka ta ware wasu daga cikin sahabbai har yan Shi’a jebberiyya na cewa “wai su sun yarda da nagartatun sahabbai” shin abin tambaya anan akwai sahabin da ba nagartacce ba? Su kuma yan Shi’a zakzakiyya cewa suka yi” gaba dayan sahabbai
bancin guda shidda sun yi ridda sun bar musulunci bayan wafatin Annabi sallallahu alaihi was sallam”.hakama a gidan annabi (s.a.w) yan shi’a sun
ware matansa,hakama sun ware ya’yansa ban cin
fadima (a.s)daga cikin ahlul baiti ,to ya akayi kuna son diya
(fadima)amma baku son mahaifiyarta(khadija) ta zama cikin ahlul baiti?
Abin tambaya anan shine ai da fadima(a.s)da sauran biyar bancin
ibrahim duk diyan khadija ne,uwarsu daya
ubansu daya da nana fadima (a.s) ya haka? Duk da mun san cewa Annabi(s.a.w) yana cewa” fadima(a.s) tsoka ce daga cikin jikinsa” amma kuma wannan ba dalili bane da zai sa yan shi’a su mayar da sauran ya’yan annabi muhammad (s.a.w) saniyar ware ba sai dai su hade su gaba daya duk su so su.idan ba haka ba,sai mu ce anya
wannan soyayya ce?Allah yanasa umurnin mu da mu shiga
musulunci baki daya kada muyi munafucci a cikinsa ta hanyar daukar 6angare daga cikinsa mu bar wani 6angare.Ahlul baiti da sahabbai da
waliyyai da duk wani musulmi ahlulsunnah namu ne.
Allah ka bamu albarkar su baki daya. Shin anan waye masoyin ahlul baiti ahlulsunnah ko yan Shi’a?

ZAKZAKY SHINE YA KAWO GURBATAN MUSULUNCI A NIGERIA TUN YA SHIGO DA KWANGILAR ADDININ SHI’A DAGA IRAN. By: Abu Uthaymeen

Wannan maganar zata kada hantar
jahilai masu son abar addinin musulunci
ayi addinin shi’a, to musulmai masu ilimi
da hankali sun gano sharrin da yakawo cikin musulunci.
:
Ko kuso, ko kar kuso, mu musulmai Allah
da ManzonSa SAW muke bi sannan
muna son Ahulul baiti gabaya, muna son
sahabbai gabaya kamar yadda Allah ya sosu, baza mu bi wani gardi Zakzaky
wanda shine yazo da sharrin addinin
shi’a yana canza hakikanin addinin
musulunci a Nigeria.
:
Addinin musulunci a Nigeria tun kafin Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodio bata
san da wani addini mai suna shi’a ba
masu kiyaya ga sahabbai RA da kawo
wasu abunda baya daga cikin koyarwa
addinin musulunci, haka ma lokacin
Shehu Dan Fodio ba a san da wani addini shi’a ba na kin sahabbai RA da matan
Annabi SAW ba, bayan addini musulunci.
Kuma babu inda akace Dan Fodio ya
taba cin mutunci Sahabbai RA ko matan
Annabi SAW duk da yawan rubuce
rubucen Dan Fodio babu inda yayi rubutu don kiyayyar Sahabbai RA da matan
Annabi SAW ko taba mutuncinsu. Kuma
babu inda Dan Fodio yace ayi addinin
shi’a na kin sahabba RA da Matan Annabi
SAW koma bayan addinin musulunci.
Addinin da Dan Fodio ya rayu akai kuma ya mutu akai shine addinin musulunci ba
addinin shi’a na kin sahabbai da matan
Annabi SAW ba.
:
A tun lokacin da Zakzaky yazo da
kwangilar addinin shi’a daga Iran zuwa Nigeria, sai yafara tunkude tsarin da
musuluncin da Sheikh Mujaddadi Dan
Fodiyo yazo da shi, misali daga cikinsu
shine rashin girmama Sahabbai da matar
Annabi SAW, da kawo wasu ibada wai
TATTAKI, da auren mutu’a bayan addinin musulunci ya haramta, da sauransu.
daga wancan lokacin da yakawo addinin
shi’a wasu jahilai suka daina hakikanin
Musulunci a
kasar nan, suka dawo cin zarafin
sahabban Annabi SAW da matansa, an rudar da jahilai da sunan gwagwarmayar
kafa gwamnatin musulunci, Zakzaky sun
canza tsarin da Allah ya aje Ahlul baiti
sun cire matan Annabi SAW bayan
Kur’ani ya tabbatar, an shafe shekaru
masu yawa a baya ba a san mai zagin sahabbai ba sai da Zakzaky ya shigo da
sharrin zuwa Nigeria, ba a san aje goshi
akan wani kasko ko kasan wani gari
daban idan ana sallah ba sai da Zakzaky
yazo da sharrin addini shi’a, Zakzaky ya
raba Al’umma da Imanin su, ya chanza tunanin jahilan Musulmai, ya chanza wa
jahilai tsarin zuwa Makabarta irin na
addinin musulunci zuwa irin na kafure, ya
kuma chanza tsarin maulidin masu
maulidi, yakawo musu kadede cikin
maulidinsu, ya canzawa jahilai fadin Amin kamar yadda Annabi SAW ya nuna,
Zakzaky yace su dinga cewa ILAHEE
memokn Amin, yacewa jahilai su dinga
kiran Ya Husain ko Ya Mahdi ko Ya Ali ko
labbaika ya El-Zakzaky yayin musifa
memokon su kira Allah. ;
Zakzaky shi yazo da tsarin a karbi shi’a
abar tsarin musulunci, shi ya
kawo kin Sahabbai da Matan Annabi
SAW irinsu Abubakar, Umar,
Usman,Aisha, Hafsa da sauransu, shi ya yaudare matasa cewa shi
Gwagwarmayar Musulunci yake asai
addini shi’a yake kafawa ba gwamnatin
musulunci bane. Domin masu hankali da
suka bisa a farkon fari sukace me yakawo
kin sahabbai cikin kafa gwamnatin musulunci, a lokacin ne masu hankali da
ilimi da hangen nesa suka rabu da
Zakzaky da addinin shi’a da yazo dashi.
:
Yaku ‘yan bana bakwai masu addinin
shi’a kuje kuyi bincike akan wannan rubutun nawa zaka ga hakikanin gaskiya
cewa Zakzaky yazo da sharri ne zuwa
Nigeria. Allah yashir yar daku, kubar
addinin shi’a zuwa addinin musulunci.
:
Mu musulmai munbi Allah da ManzoSa, kuma muna son dukkan iyalan gidan
Annabi SAW da Sahabbansa sannan
muna son duk me son gaskiya kuma akai
zamu mutu insha Allah.
:
Signed: Abu Uthaymeen

BA KIN ZAKZAKY MUKE BA, AMMA MUNA KIN SHARRIN DA YAKAWO NIGERIA NE TUN DAGA 1979. BY: Abu Uthaymeen

Zakzaky yakawo sharri zuwa Nigeria
nacewa abar addinin musuluncin da Annabi SAW yazo dashi sai ayi addinin
shi’a da Zakzaky ya karbo daga kasar
Iran a shekarata 1979.
.
Addinin musuluncin da Annabi SAW yazo
dashi bai san wani abu wai kiyayar Sahabbai RA ba ko kuma kiyayyar Matan
Annabi SAW ba, addinin musulunci bai
san wani abu wai nemo kurakuren
Sahabbai RA ba bayan Allah yace ya
yarda dasu suma sun yarda daShi.
Addinin musulunci ya yarda cewa dukkan Sahabbai RA mutanen kirki ne kamar
yadda Allah bai ce banda wane da wane
ba. Addinin musulunci bai san wani abu
wai TATTAKI ba.
.
Amma addinin shi’a wanda Zakzaky ya karbo kwangilarsa daga Iran, addini shi’a
addini ne wanda ya ginu akan kin
Sahabbai da zaginsu da cin mutuncin su
da yi musu karya da kazafi kamar yadda
kuke jinsu sunayi a zahiri da kuma yadda
suke rubutawa a social media. Sabanin addinin musuluncin da Annabi SAW yazo
dashi.
.
Addinin musulunci wanda Annabi SAW
yazo dashi ya haramta auren mutu’a
. Sannan addini shi’a wanda Zakzaky ya
kawo Nigeria suna zagi da cin mutunci da
karya da kazafi akan matan Annabi SAW
musamman Ummuna Aisha da Hafsa RA
kamar yadda kun sha jin sunayi kuma
suna rubutawa a social media. Sannan kuma suna riya cewa Ummuna Aisha da
Hafsa su suka kashe Annabi SAW
sabanin addinin musulunci.
.
Addinin shi’a wanda Zakzaky ya kawo
Nigeria sun kirkiri wani abu wai TATTAKI da sunan addinin a shekara ta 2012.
.
Addinin shi’a wanda Zakzaky yazo dashi
Nigeria sun halatta auren mutu’a sabanin
addinin musulunci wadda ta haramta
daga baya. .
Zakzaky ya haramta karatun boko a
farkon da’awarsa na addinin shi’a, wanda
hakan ya janyo mana koma baya ga
al’ummar addinin musulunci a wancan
lokacin. A lokacin wasu sun bar karatun bokon wasu kuma sunki shiga kuma
sunki su sa ‘ya’yansu.
.
Zakzaky ya yaudare al’ummar addinin
musulunci dayawa a farkon da’awarsa,
domin yazo da yaudara cewa kafa gwamnatin musulunci ne zaiyi a lokacin
ashe manufarsa gurbata addinin
musulunci sai yavyada addinin shi’a.
.
A wancan lokacin wadanda suka bishi da
kyakkyawar niyar kafa gwamnatin musulunci sai suka jisa yana cin
mutuncin Sahabba da matan Annabi
SAW, sai suka fahimci cewa to me
yahada kafa gwamnatin musulunci da
kuma zagin wadanda suka yada
musuluncin zuwa sassan duniya. Anan ne masu yi da gaskiya suka fahimci cewa
ba gwamnatin musulunci ake son kafawa
ba, ashe gwamnatin gurbata addinin
musulunci ne zuwa addinin shi’a. A
wannan lokacin ne masu hankali da ilimi
da hangen nesa suka watse suka barshi da kwangilarsa da ya karbo daga kasar
Iran watau yadda addini shi’a.
.
Zakzaky ya bata wa mabiya darika masu
yin maulidi tsarin maulidinsu wadda aka
sani darika sunayi ba tareda ganguna da jiya da piyano amma yau sanadin
gurbatar Zakzaky ya kawo musu ana
buga ganguna da kayan kade kade
hadda rawa tareda mata da ‘yan mata.
.
Zakzaky ya jefa wasu daga cikin musulmai wadanda basu fahimci
manufarsa ba cikin halaka. Wadda hakan
yajawo muna asarar yayukan ‘yan kasa.
.
Allah kashiryar damu tafarkin hakikanin
Addinin musulunci wanda Annabi SAW yazo dashi. Allah ya nesantar damu daga
sharrin dake cikin akidun shi’a. Allah
kashiryar da wadanda ake yaudararsu
cikin addinin shi’a. Allah ka kashemu
muna cikin addinin musuluncin da Annabi
SAW yazo shi. .
Signed:
Abu Uthaymeen
.
20/Rabi’ul Thani/1439
08/January/2018