Category Archives: Sunnah

*Kishi Ko Hauka* *Tare da:* _Mal Muh’d Kabir Haruna Gombe {Hafizahullah}

*Kishi Ko Hauka* *Tare da:* _Mal Muh’d Kabir Haruna
Gombe {Hafizahullah}_ _ Wannan Itace Muhadarar Da Mal Ya Gabatar Ranar Litinin 28/04/1439//
16/01/218_ _ Malam Yayiwa Wannan Lackca Da Taken *Kishi Ko Hauka?* Masallacin
Juma’a Na Kofar Gidan Sarkin Kofa
Zaria_ _ Domin Sauke karatun Danna Wannan Blue Din Link Dake Tsakiya_ http://darulfikr.com/s/39525 Ayi sauraro lafiya Kasance da darulfikr.com domin samun karatun maluman Sunnah a
saukaka
Darulfikr taku ce domin yada Sunnah
┬ęCopyright:-
*_Abu Abdirrahman Assalafy Kano_*
29/04/1439 A.H 17/1/2018 C.E

Advertisements

*LAKCOCIN MAKON SAHABBAI*

*LAKCOCIN MAKON SAHABBAI* 1.Martabar Sahabbai Da Falalarsu
*Dr.Abdullahi Getso* http://darulfikr.com/s/39526 2.Wa Ya Kashe Hussaini ??
*Dr.Muslim Ibrahim* http://darulfikr.com/s/39527 3.Matsayin Batanci Ga Sahabbai
*Mlm Lawal Abubakar* http://darulfikr.com/s/39528 4.Da’awar Shi’a (Jiya da Yau)
*Dr.Mu’azzam sani* http://darulfikr.com/s/39529 5.Akidun Shi’a A Mahangar Shari’a.
*Dr.Rabi’u Umar R/Lemo* http://darulfikr.com/s/39530 5b.Dan Shi’a da ya dawo Sunnah
*Abba Koki Junior* http://darulfikr.com/s/39531 Wannan lakcocin an gabatar dasu ne a
massalacin almuntada dake dorayi tun
daga ranar asabar har zuwa laraba
karkashen *ALFURQAN CHARITABLE
FOUNDATION*
@copyright Darul Ihsaan Services +2348168015170/
+2348033459565

Tafsirin Suratun Nisa’i Verse 137-139 {Darasi Na 56} Tareda:- Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum {Hafizahullah}

Tafsirin Suratun Nisa’i Verse 137-139
{Darasi Na 56} Tareda:- Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum {Hafizahullah} Wannan Shine Tafsirin da Malam Yagabatar jiya Laraba a Masallachin
School of Nursing dake Nan Cikinjwa
Garin Bauchi. Da farko Malam Yayi Magana akan Wadanda Suke Aikata Zunubi sai su
Tuba, bayan kwana 2 sai su dawo! Allah
zai Toshe musu Duk wani Hanyar da zai
kaisu ga Tuba. Sannan Malam Yaja Hankalin Yan’uwa akan Kokarin Aikata Alkhairi,
Domin Duk Abunda ka aikata Ka Aikata ne
wa Kanka. Sannan Malam Yaja Hankalin Barayi masu Sace kayan mutane, akan Su sani
Duk wani abunda Suka Dauka na wani
zasu biya a Ranar kiyama, Ranar da Babu
Kudi ko Dirhami. Sannan Malam Yayi Magana Akan Siffofin Munafukai, Yakuma ja Hankalin
Al’umma akan Jibantar Kafurai. Da Karshe Malam Yaja Hankalin Matasa akan Harkan Kwallon Kafa http:// darulfikr.com/s/39521 Kucigaba Da Kasancewa Damu a http://www.Darulfikr.com Domin Samun Karatukan Maluman Sunnah.
┬ęCopyright:-
Muhammad Sageer Sautul Qur’an
01/05/1439.
18/01/2018

*THE CONJUGAL RIGHT OF MARRIAGE IN SHARI’AH* TARE DA *DR. BASHIR ALIYU UMAR*

*MUHADHARA DAGA GARIN ABUJA
CIKIN HARSHEN TURANCI* MAI TAKEN *THE CONJUGAL RIGHT OF MARRIAGE
IN SHARI’AH* TARE DA *DR. BASHIR ALIYU UMAR* DAGA *MASALLACIN ANNUR DAKE IBB WAY
WUSE 2 ABUJA*
30/4/1439-18/1/2018
Danna link na kasa domin downloading http://darulfikr.com/s/39637 Ayi sauraro lafiya.
Kasance da Darulfikr.com domin samun karatukan malaman Sunnah a saukake.
Darulfikr taku ce domin yada Sunnah.

*NEMAN AURE A MUSULUNCI .* Tare da :- *Sheikh Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya (Hafizahullah).*

*MUHADARA MUHADARA.* *Maudu’i.*
*NEMAN AURE A MUSULUNCI .*
Tare da :- *Sheikh Dr. Abdallah Usman
Gadon Kaya (Hafizahullah).* Ranar Alhamis
01/05/1439
19/01/2018
*Daga Masallacin Sa’ad Ibn Abi wakas
Kano.*
danna link na kasa domin downloading http://darulfikr.com/s/39628 Ayi sauraro lafiya.
kasance da Darulfikr.com domin samun karatukan malaman Sunnah a saukake.
Darulfikr taku ce domin yada Sunnah.

BA A KAFA KUNGIYAR IZALAH A KAN MAZHABAR MALIKIYYAH BA: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

1. Ba a kafa Kungiyar Izalah a kan
mazhabar Malikiyyah ko wanin
Malikiyyah ba daga cikin Mazhabobin da
ke cikin fage, a’a an kafa ta ne a kan yin aiki da Alkur’ani da Hadithi da kuma
Ijma’i.
2. A inda duk mazhabar Malikiyyah ko
waninta suka dace da Alkur’ani da
Hadithi da kuma Ijma’i, to lalle kungiyar
Izalah na tare da su a nan, a inda kuma mazhabar Malikiyyah ko waninta suka
saba wa Alkur’ani da Hadithi da kuma
Ijma’i to lalle kungiyar Izalah ba ta tare
da su a nan.
3. Lalle abin takaici ne har kullum ‘yan
bidi’ar da ba sa jin kunyar yi wa Duniya karya su rika cewa: an kafa kungiyar
Izalah ne a kan Alkur’ani da Hadithi da
kuma Mazhabar Malikiyya!
4. Tabbas babu inda lafazin ambaton
mazhabar Malikiyyah ya zo koda sau
daya ne a cikin constitution din Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis
Sunnah. Babu inda za a sami lafazin
Mazhabar Malikiyyah a rubuce tun daga
shafin farko na Constitution din Kungiyar
har zuwa shafinsa na karshe.
5. Lalle abin da yake rubuce cikin constitution din Kungiyar Jama’atu
Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah shi
ne: Ita kungiya ce ta addinin Musulunci
tsantsa kamar yadda Annabi
Muhammadu mai tsira da amincin Allah
ya taho ta shi, wacce take dogara da Alkur’ani da Hadithan Manzon Allah da
kuma Ijma’i.
6. Wannan shi ne hakikanin Kungiyar
Izalah da constitution dinta, ba wai
karairayin da wasu yan bidi’ah ke yadawa
ba game da ita. Allah Ya taimake mu. Ameen.

SUMA AHLUL- BAITI NE DOMIN ANNABI MUHAMMAD(S.A.W)YA HAIFE SU

SUMA AHLUL- BAITI NE DOMIN ANNABI MUHAMMAD(S.A.W)YA HAIFE SU
.
Via:-Garkuwan Magabata
.
A duk lokacin da ya’yan yan shi’a jebberiyya ko zakzakiyya suka tashi yin magana zaka ji suna cewa wai ahlulsunnah basa son ahlul baiti, amma yanzu zamu gani idan da gaske ne, yan uwa mu karanta wannan.
Dan uwa musulmi ko kasan ya’ya
nawa ne Allah(s.w)ya baiwa Annabi muhammad
(s.a.w) a rayuwarsa ta duniya? To idan baka
sani ba yana da ya’ya guda bakwai (7) ga su
kamar haka:-
1.Zainab r.a
2.Rukayya r.a
3.Ummu khulsum r.a
4.Fadima r.a
5.Abdullah r.a
6.Al-kasim r.a
7.Ibrahim r.a
Wadan nan
sune ya’yansa,shidda(6) daga cikinsu duk diyan nana
khadija r.a ne,ibrahim ne kawai a dan mariya
r.a.To ya yan shi’a basa maganarsu? Bari kuji
abinda yasa basa maganarsu,zainab r.a ta aure
wani dan qabilar banu umaiyya mai suna Abu
al-as dan rabi’i.Rukayya kuma ta aure usman
ibn affan r.a na ukku daga khulafa’u rashideen kuma shima daga banu qabilar umaiyya ne.
Ummu khulsum itama ta aure usman ibn affan r.a
bayan yar uwarta rukayya a.s ta rasu. Fadima r.a
ta aure sayidina Aliyu r.a.Amma su yan shi’a
sai suka dauke fadima r.a cewa ita kadai ce a
diyar annabi sallallahu alaihi wasallam,da hakane jahillai suke daukar
cewa fadima ce kawai a diyarsa,kuma sai aka yi
dai dai da koda annabi s.a.w yayi wafati
fadima ce kawai a raye.da haka ne jahillai a
basu iya gane cewa yan shi’a karya ce suke
yi.don haka muna kira da ayi soyayya da ya’yan
annabi(s.a.w) baki dayansu babu wariya daga daya
daga cikinsu. Hakama a janibin sahabbai(r.a)bamu ware ko daya daga cikinsu,Don haka mu ahlulsunnah bamu
ware daya daga cikin Ahlul baiti ko sahabbai muce bamu sonsa.
kuma bamu sukar ko mutun daya daga
cikinsu, asalima duk muna sonsu(ahlul baiti da sahabbai) baki daya wannan itace hanyar gaskiya.Amma
hanyar da yan shi’a zakzakiyya da jebberiyya suka dauka ta ware wasu daga cikin sahabbai har yan Shi’a jebberiyya na cewa “wai su sun yarda da nagartatun sahabbai” shin abin tambaya anan akwai sahabin da ba nagartacce ba? Su kuma yan Shi’a zakzakiyya cewa suka yi” gaba dayan sahabbai
bancin guda shidda sun yi ridda sun bar musulunci bayan wafatin Annabi sallallahu alaihi was sallam”.hakama a gidan annabi (s.a.w) yan shi’a sun
ware matansa,hakama sun ware ya’yansa ban cin
fadima (a.s)daga cikin ahlul baiti ,to ya akayi kuna son diya
(fadima)amma baku son mahaifiyarta(khadija) ta zama cikin ahlul baiti?
Abin tambaya anan shine ai da fadima(a.s)da sauran biyar bancin
ibrahim duk diyan khadija ne,uwarsu daya
ubansu daya da nana fadima (a.s) ya haka? Duk da mun san cewa Annabi(s.a.w) yana cewa” fadima(a.s) tsoka ce daga cikin jikinsa” amma kuma wannan ba dalili bane da zai sa yan shi’a su mayar da sauran ya’yan annabi muhammad (s.a.w) saniyar ware ba sai dai su hade su gaba daya duk su so su.idan ba haka ba,sai mu ce anya
wannan soyayya ce?Allah yanasa umurnin mu da mu shiga
musulunci baki daya kada muyi munafucci a cikinsa ta hanyar daukar 6angare daga cikinsa mu bar wani 6angare.Ahlul baiti da sahabbai da
waliyyai da duk wani musulmi ahlulsunnah namu ne.
Allah ka bamu albarkar su baki daya. Shin anan waye masoyin ahlul baiti ahlulsunnah ko yan Shi’a?