Category Archives: Uncategorized

*ZAN IYA FASA ABIN DA NA YI NIYYA A ZUCIYATA ?*

*ZAN IYA FASA ABIN DA NA YI NIYYA A
ZUCIYATA ?*
*Tambya Assalamu alaikum Malam, barka da
kokari tare da fatan Allah Ya saka da
alheri. Mutum ne abokin shi ya tambaye
sa bashi, shi kuma sai ya bashi amma a
zuciyar shi sai ya raya kyauta ya bashi.
bayan abokin ya samu sai ya dawo mashi da kudin shi kuma kawai sai ya karba
kayan shi. Malam Ya matsayin kudin a
wurin sa ?
*Amsa:*
Wa alaikum assalamTo dan’uwa tun da
riyawa ka yi a zuciya, ba ka furta ba, to hukuncin bai hau ba, kuma ba ka da laifi
in ka fasa, Annabi S.a.w. yana cewa :
“Allah ya daukewa Al’umata abin da suka
riya a zuciyar şu, mutukar ba su furta ba”
Bukhari hadisi mai lamba ta: 4869.
Saidai yana da kyau ka Sani cewa : duk lokaçın da za ka yi kyauta to Sheidan zai
dinga nuno maka talauci, duk wanda ya
bayar da wani abu saboda Allah, tabbas
Ubangiji zai mayar masa da ninkin-ba-
ninki, kamar yadda hakan ya tabbata a
ayoyi da yawa a cikin alqu’ani mai girma. Allah ne mafi sani.
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
8/1/2016.
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Advertisements

NISABIN ZAKKAR KUDI DR. JAMILU YUSUF ZAREW

NISABIN ZAKKAR KUDI !
Tambaya : Malam donAllah
nawa ne nisabin zakka a
yanzu ?, saboda ina da wasu ‘yan kudade ne na
ke so na sani, ko akwai hakkin Allah a cikin su,
Allah ya kara maka albarka a rayuwarka.
Amsa : To dan’uwa amsa wannan tambayar yana da
mutukar wahala, saboda ya dogara ne da
sanin kudin gram din gwal a kasuwa, ko
kuma na azurfa, domin yana daga cikin kuskure
rubuta nisabi daya tal ga zakka, har zuwa
tsawon shekara guda, kamar yadda wasu suke
yi a calendar, saboda gwal yana tashi a
kasuwa yana kuma sauka . Wannan ya sa na yi
tattaki zuwa kasuwar masu saida gwal a
Madina ranar talata : 2/12/2014 , in da na samu
cewa har zuwa ranar ana saida kowanne gram
daya na gwal din da ba’a sana’anta shi ba akan
kwatankwacin naira : 5969, kamar yadda muka
sani gram 85, shi ne nisabin zakka, don haka,
in muka buga wancan adadin sau 85 , zai ba
mu : dubu dari biyar da bakwai da dari uku da
sittin da biyar (507365). Wannan shi ne nisabin
zakka, har zuwa tarihin da na rubuta a
sama, idan har kudinka sun kai wannan adadi,
kuma shekara guda ta zagayo musu, to zakka
ta wajaba a cikinsu, za ka raba gida arba’in
ka bayar da kashi daya . Allah ne mafi sani

★YAD’A SALLAMA ACIKIN AL’UMMA★

★YAD’A SALLAMA ACIKIN AL’UMMA★
.
Sallama ita ce gaisuwar ‘Yan Aljannah,
ita ce farkon abunda Annabi Adam (AS)
ya fara yiwa Mala’iku. Amma da yawa
daga cikin Al’ummah basa bawa sallama muhimmanci, kuma haqiqa sallama tana
da daraja ta musamman acikin addinin
musulunci, haka zalika wasu sun dauketa
abun wasa sai ayi musu sallama baza su
masa ba ko kuma su fad’a waje ba tare
da sallama ba. .
Daga cikin Alqur’ani mai girma da Hadisai
masu inganci da dama sun zo dangane
da yad’a sallama acikin a cikin al’umma.
.
★ WASU AYOYI DAGA ALQUR’ANI MAI GIRMA DA SUKE TABBATAR DA
SALLAMA ACIKIN ADDININ ALLAH
.
●ALLAH (SWT) yace: ” Yaku da kuka yi
imani, kada ku shiga gidajen da ba naku
ba har sai kun nemi izini kunyi sallama ga masu gidan” [suratul Nur]
.
●ALLAH (SWT) yace: ” Idan zaku shiga
gida, to kuyi sallama akan kawunanku,
gaisuwa daga ALLAH mai albarka,
daddada”. [suratul Nur] .
●ALLAH (SWT) yace: ” Idan an gaishe ku
da gaisuwa mai kyau to kuma ku gayar
dasu da wacce tafi ta kyau ko kuma ku
mayar da kwatankwacin wacce aka
muku” [suratul Nisa’i] .
★HADISAI DAGA ANNABI (Sallallahu
alaihi wasallam) WANDA SUKE
TABBATAR DA SALLAMA ACIKIN
AL’UMMA:
. ●Yazo cikin Bukhari da Muslim cewa wani
mutum ya tambayi Manzon ALLAH
(Sallallahu alaihi wasallam) cewa wani
abu ne mafifici a musulunci, sai Manzon
ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) yace:
Ciyarwa, sannan yin sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba”
.
●Yazo daga Barra’u dan Azib (RA) Yace:
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) ya umurce mu da abubuwa
guda bakwai (7): gaisar da marar lafiya, da raka jana’iza, da gaisar da mai
atishawa, da taimakon raunannu,da
agazawa wanda aka zalunta, da daidaita
sallama da ku6utar da
rantsuwa” [Bukhari Muslim]
. ●Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) Yace: “Ya ku mutane ku yada
sallama, ku sadar da zumunta,kuma kuyi
sallar dare,lokacin da mutane suke bacci,
sai ku shiga Aljanna tare da
aminci” [Tirmizi] .
●Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi
wasallam) yace: ” Ba zaku shiga Aljannah
ba sai kunyi imani, kuma baza ku yi imani
ba har sai kun so junanku, shin bana
nuna muku wani abu da in kunyi shi zaku so juna ba? Ku yada sallama a
tsakaninku” [muslim]
.
●Daga Ammar (RA) Yace: Abubuwa uku
wanda duk ya hada su ya hada imani:
Mutum yayi adalci ga kansa, da yada gaisuwar sallama acikin al’umma, da yin
kyauta acikin rashin wadata”
.
[Bukhari da Fat’hul bari 1/82, ya ruwaito
shi daga maganar Ammar ba tare da ya
ambaci isnadinsa ba] .
★WASU HUKUNCE- HUKUNCEN
SALLAMA:
.
●Yin sallama Yayin da kazo cikin mutane,
da yayin da zaka rabu dasu. .
●Qarami shine zai yi wa babba sallama.
.
●Wanda yake kan abun hawa shi zai yiwa
na qasa sallama.
. ●Mutane kad’an su zasu yiwa masu yawa
sallama.
.
●Idan kayi sallama sau 1 ba a amsa ba
kayi haquri ka maimaitata har sau 3 har
ajika a amsa maka. .
●Idan kaje gidan mutane kayi sallama,
aka amsa maka kada ka shiga sai anyi
maka izini.
.
★SALLAMAR DA TAFI DACEWA: .
Mutane da yawa sunfi bada himma
wajen rubuta wadannan kalmomin a
matsayin sallama:
.
•slm, Aslm Alkm, wslm. .
A gaskiya Yan’uwa muyi qoqari mu ringa
rubuta cikakkiyar sallama ba abriviation
ba. domin inganta abunda yazo daga
Addininmu ba koyi da yahudu da Nasara
ba. .
Yazo acikin Riyadus-saliheen daga
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi
Wasallam) Yace:
.
● Assalamu Alaikum [Lada 10] .
●Assalamu Alaikum Warahmatullah
[Lada 20]
.
●Assalamu Alaikum Warahmatullah
Wabarkatuhu [Lada 30] .
ALLAH Ya bamu ikon tabbatar da Sunnah
a koda yaushe (Ameen)
.
-Faridah Bintu Salis
(Bintus~sunnah)

002. ADDU’AR SANYA TUFAFI

002. ADDU’AR SANYA TUFAFI GARKUWAR MUSULMI TA ADDU’O’I DAGA ALKUR’ANI DA SUNNAH (Hisnul Muslim) TA’ALIFIN Shaikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Alkandahi FASSARAR Dr. Bashir Aliyu Umar Hafizahullah GABATARWA. Abubakar Nuhu Koso <> . (5) ﺍﻟﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬِﻱ ﻛَﺴﺎﻧﻲ ﻫﺬﺍ ( ﺍﻟﺜﻮﺏ ) ﻭﺭَﺯَﻗَﻨِﻴﻪ ﻣِﻦْ ﻏَﻴْﺮِ ﺣَﻮْﻝٍ ﻣِﻨّﻲ ﻭﻻ ﻗُﻮﺓٍ ” Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda Ya tufatar dani wannan (tufa) kuma ya azurtani da ita, ba tare da wata dabara daga gareni ba, ko wani karfi. DUBA (5) Abu Dawud, Tirmizi da Ibn Majah, duba Irwa’ul Ghalil hadisi mai lamba 1989

DONALD TRUMP CIKIN FAGAUNIYA YA SAKE WANI ZALUNCIN KUMA: By Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

DONALD TRUMP CIKIN FAGAUNIYA YA
SAKE WANI ZALUNCIN KUMA:
1. A cikin ci gaba da fagauniyarsa da
shirmensa da yake yi wa al’ummar Duniya
shugaban Kasar Amirka Donald Trump ya
sake daukan sabon mataki na zalunci a kan Birnin Qudus; a inda ya ce ya amince
a hukumance cewa Wannan Birni na
Qudus shi ne babban birnin Isra’ila!
Donald Trump ya dauki wannan matsaya
ne duk kuwa da cewa ta saba wa dukkan
ka’idodin da Majalisar Kasashen Duniya ta ayyana a kundinta.
2. Muna yin tir da Allah wadai da wannan
mataki na tsokana da zalunci da neman
tada fitina cikin Duniya da Donald Trump
ya dauka. Muna kuma rokon Allah
Madaukakin Sarki da gaggauta kubutar da Wannan gari mai yawan albarka daga
mamayar azzaluman Yahudawa da
magoya bayansu. Ameen.

SHEKARU 25 DA RASUWAR SHEIK ABUBAKAR GUMI TAKAITACCEN TARIHINSA

An haifi Marigayi Shaikh
Abubakar Mahmud Gumi
ne a cikin garin Gumi
dake jihar Sokoto, a
shekara ta 1340 bayan
Hijira dai dai da shekarar
Miladiyya 1922.
Malam ya tashi ne cikin
kyakkyawar tarbiyya da
natsuwa da tsafta da
neman Ilimi karkashin
kulawar mahaifin sa
(Alkalin Gumi a wancan
zamanin).
Haka kuma marigayi
Sheik Gumi ya yi
karance-karance na
zaure a majalisi daban
daban na Malaman da
suka shahara a kasar
Hausa a wancan lokaci,
tare da karatu na
nizamiyya daga nan
kasar har kasar Sudan
da kasar Saudi Arabiya.
Shaikh Abubakar Gumi
mutum ne mai kokarin
binciken Al-kur’ani da
Sunna kan hukunce
hukuncen Shari’a, tun
daga abin da ya shafi
Tauhidi, Hadisi, Fikhu da
luggar Larabci, wanda
karantarwar da ya yi ta
tabbatar da haka.
Malam ya yi rubuce-
rubuce masu yawa,
kadan daga cikin su
akwai:-
*Al Akeedatus
Saheehah bi
Muwaafakatish Shari’ah
*Tarjamar Ma’a’nonin
Al-ƙur’ani Mai Girma.
Tafsirin Al-kur’ani:
*Raddul Azhaan ilaa
Ma’aanil Kur’an.
*Tarjamar littafin
Hadisin “Arba’uunan
Nawawiy”
Littafi mai suna
*Manufata” ko (Where I
Stand).
Wannan littafi ya na da
matukar amfani ga
sanin tarin siyasar
kasar nan da ta shafi
Addini da Mulki da
sauransu.
Sheik Gumi ya rasu ne a
ranar 11 ga watan
Satumba, 1992.
Marigayi Sheikh Gumi
baya zagi ko habaici ga
wani, hasalima in ka jefi
shi da baƙar magana,
shi sai ya jefo maka
fara tas.
Allah ya jikan Malam, ya
gafarta masa da sauran
Musulmai muminai
Amin.
Daga Jibwis Nigeria