WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 11

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 11
95. Allah tsine wa duk wanda
Yas sa wa Allah andada
Zai dandana kuda tai tun da Bai zamto mai tauhidi ba
96. Kutse ba kyau kayin qadara
Duk wanda ya qi zai yi asara
Kunya da tsiya da yawan fatara
Tsira ba zai taba samu ba
97. Zai fada rudu, tabewa Sai ta aurai ba sa rabuwa
Zindiqanci zai komawa
Ba zai zama mai tauhidi ba
98. Al-arshi da Kursi tabbas ne
Allah daga su mawadaci ne
Bayin Allah mabuqata ne Ba za su wadatu da Allah ba
99. Allah ya kewaye Al-arshi
Ba ma yarda mu sifanta Shi
Mun gasgata manzo bawanShi
Manzon Allah bai qarya ba
100. Ibrahim ka ga Khalilun ne Allah ya riqe shi haqiqa ne
Haka nan Musa ko Kalimun ne
Ba za mu bi ‘yan ta’adili ba
101. Mun miqa wuya mun imani
Mun gasgata ayar Kur’ani
Ba ma bin duk wani shaidani Ba za mu biye wa son rai ba
102. Mun yarda da manzannin Allah
Annabbawa bayin Allah
Sun kawo addinin Allah
Ba su tauye saqon Allah ba
103. Mun shaida cewa aikinsu Wa’azin tauhidin Rabbinsu
Allah dada tsira a gare su
Ko da daya ni ban ware ba
104. Ahlul-qibla ko musulmi ne
Matuqar sun yarda suna a sane
Cewa manzo jagora ne Ba su canza mai addini ba
105. Ba su qaryata Manzon Allah ba
Ba su wa sunnanrsa jafa’i ba
Ba su qetare haddin sunnar ba
Ba mu kafirtar da musulmai ba

Advertisements

WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 10

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 10 81. Jimlolin nan da na shisshiryo
Zance ne sam ba wani boyo
Bawa mabuqaci dan goyo
Ba zai tsira bila wannan ba
82. Bayin Allah da waliyyanSa
Haka nan ulama’u mutanen sa Ita sun ka riqe gun bautar sa
Ba su qaryata Manzon Allah ba
83. Nan sun ka tsaya ba su gota ba
Haddin da a kai ba su keta ba
Gona da iri ba su zarce ba
Bautar Allah ba su daina ba 84. Ilmi ka san fa gida biyu ne
Na dayan su akwai shi sananne ne
Shi kau na biyun boyayye ne
Allah bai ba bayi shi ba
85. Imani ba shi da inganci
Sai an sa ilmin adalci An bar kutse bisa jahilci
Ba ra’ayin qartin banza ba
86. Lauhun da Kalam mun imani
Dukkan qadara an yi bayani
A rubuce ciki mun imani
Allah ya qadarta ba wai ba 87. In da bayi za sui gayya
Don canza abin da ya shisshirya
Kari da ragi ko jayayya
Wallahi ba za su iya mai ba
88. Jaffal qalamu ka ji batuna
Ma akhda‘ani bai samu na Akasin haka koda ban qauna
Ba zai kauce ga bari na ba
89. Bayi ku sani cewa Allah
Tuni yai tsari shi na jimilla
Bisa kan hikimar tsarin Allah
Ba sa haye tsarin Allah ba 90. Kuma babu ragi haka ba qari
Ba canji komai qamari
Haka cin gyara bar kurari
Ba za ka iya da Ilahiy ba
91. Ba mai iya qara halittunSa
Koko ya rage masa bayinSa Ko da a sama ko nan a qasa
Wannan fa dadai ba zai yiwu ba
92. Wannan a aqida asali ne
Ka riqe shi da kyau ko ka gane
Don ko maganar Kur’ani ne
Ba wai maganar bayi ce ba 93. Ahzab, Furqan ka karanta su
Farkon Furqan sai ka gamsu
Aya ta biyu an yi batun su
Harkar qadara ba wasa ba
94. Ahzab kuwa aya ta talatin
Da takwas, ka riqe wannan baitin Don na shirya da baqin Latin
Ba zai yiwu in ja ayar ba

WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 9

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 9
70. Allah ya dau alqawarin Sa
Kan ‘ya’yan Adam bayinSa
Cewa su za sui bautar Sa Ba za su yi sabon Allah ba
71. A’araf aya saba’in da biyu
Bayan ta dari kuma in ya yiwu
Ka bi sharhi ban da halin gayu
Kar kai jayayyar ‘yan taba
72. Adadin ‘yan Aljanna dukansu Da wadanda wuta ce qarshensu
Allah tuni ya lissafa su
Ba za ya rage ko qari ba
73. Af’alul Khalqi dukanninsu
Da sanin Sa suke yin aikin su
Aikin da suke Shi yay yi su Ba su da Allah in ba shi ba
74. Da hukuncin Shi yaw ware su
‘Yan aljanna Ya hukunta su
Haka ‘yan wuta ma Yaw ware su
Allah kuma bai zalunci ba
75. Asalin qadara wani sirri ne Allah Sarki mai baiwa ne
Shi dai ya sani don gaibi ne
Ba mai qadara in ba shi ba
76. Da Mala’ikku, Annabbawa
Ba wanda yake iya ganewa
Kuma ba kyau neman kutsawa Ba imani ne wannan ba
77. Dugyani ne da ranshin kunya
Ka kiyaye kar ka bi ‘yan baya
Bar waswasi bar zarbababiya
In ka qi ba za ka falahi ba
78. Allah Sarki ya dauke shi Ilimin qadara daga bayin Shi
Kuma ya hana nema na sanin shi
Bai yarda a nemi sani nai ba
79. La yus’alu amma yaf’alu
Ayar Allah ce tanzilu
Haka nan taz zo bisa tartilu Ba zance ne na mutane ba
80. Duk wanda ya ja da hukuncinSa
Ya qaryata ayar RabbinSa
Ya kafirce daga dininsa
Arne ne ba ko musulmi ba

WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Dr Kabir Asgar Post No. 8

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Dr Kabir Asgar
Post No. 8
60. Addinin Allah musulunci
Tawili ko wani batanci
Ba su da qima sai adalci Sai miqa wuya ba rikici ba
61. Mai kore sifofin Rabbani
Wannan ya qaryata Kur’ani
Hakanan wanda ya ba shi kamanni
Wannan aiki bai dace ba
62. Siffofin Allah kyawawa Sam ba su kama da sifar bawa
Sun sha bambam da na dan kowa
Wannan haka ne ba tababa
63. Ya daukaka Allah Mahalicci
Daga duk wani bawa mabuqaci
Sarki Allah bai zalunci Ka riqe wannan ka fada a gaba
64. Isra’i mun ce haqqun ne
Haka ma Mi’iraji tabbas ne
Baitul Maqadis daga nan shi ne
Yaj je sama ba qarya ce ba
65. Da jikin shi ya je ba barci ba Ba kuma ruhi ban da jiki ba
Manzonmu ba zai fadi qarya ba
Bai naqqasa saqon Allah ba
66. Allah ya daukaka manzona
Sallah yab bai wa masoyina
Allahs sa shi zai ceto na In tsira na zam ban tabe ba
67. Mun yarda da tafkin da ya ba shi
Don yas shayar da mutanenshi
Babu qishirwa bayan shan shi
Kuma dan bidi’a ba zai sha ba
68. Kofin sha ba zai yi kadan ba Wawa gun sha ba ta taso ba
Girmanshi ba za ya misilto ba
Sauran zancen sai an duba
69. Ceton shi da zai ai tabbas ne
Shi ne zai ceci mutane
Wannan zance ne fa sananne Tun ba a wajen malammai ba

WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 7

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 7
49. Wannan ita ce fa aqidarmu
Tafsirin ba ra’ayoyinmu Ingantattun nassoshinmu
Ba mu yarda da bin son zuci ba
50. Ba wanda ya tsira a addini
Sai wanda ya bar biye qaulani
Ya bi Manzon nan mai Kur’ani
Ga batun Allah bai ja mai ba 51. Shubuha ya buge ta ya dau haske
Kur’ani kuma yab bi da gaske
Haka sunnoni duka ban da sake
Ba tare da bin sambatu ba
52. Musulunci sam bai daidaita
Sai taslimi ya qasaita Istislami sai ka furta
Ba neman kaiwa matuqa ba
53. In ko ka zaqe kan ilminka
Ga abin da haramun ne kanka
Wannan shi ne zai cuce ka
Ba zai kuma kai ka ga tsira ba 54. Wannan bisa shirka zai kai ka
Ya hana ka fahimtar dininka
Ya raba ka da dan imaninka
Tauhidin ba zai saura ba
55. Sai dai ka zamo a cikin rikici
Ka fadi ka tashi munafurci Ba imani ba kafirci
Kuma kai ba ka ce qarya ne ba
56. Kai ba ka ce wannan daidai ba
Ba ka tabbata qaryar zance ba
Ka sa shakka ba ka huta ba
Kai ba tsantsar mai saiti ba 57. Sai waswasi ka zamo baidu
Ba ka a ruwa kai ba ka tudu
Susa ba ta yiwuwa da gudu
Ka yi marmaza kai saurin tuba
58. Duk wanda ya qaryata manzona
Cewa in an shiga Aljanna Za a ga Allah har ai murna
Ba zai amfana da wannan ba
59. Ko wanda ya murgude nassoshi
Yai tawili ya bi son ranshi
Ya guje wa tafarkin manzonshi
Wannan shi ma ba zai sha ba

WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 6

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 6
37. Manzonmu Muhammadu bawan Shi
Mun tabbata Shi yaz zabe shi
Ya riqe shi abin yarda gun Shi Bayan shi ba zai wani aike ba
38. Jagora ne gun manzanni
Shi ne yak kawo Kur’ani
Ya zamo qarshen ‘yan saqonni
Khalilin Allah ba wai ba
39. Duk wanda ya zo nan bayan shi Yac ce Allah ya aiko shi
Karya ce ko wane ne shi
Allah tsine masa ba wai ba
40. Allah ya aiko manzon Sa
Izuwa dukannin bayin Sa
Shiriya yak kawo hasken Sa Ya haskaka bai bar zulma ba
41. Kur’ani zancen Allah ne
Allah ya saukar wahayi ne
Kar wanda ya ce Makhluqi ne
Bidi’a sam ba kana ce ba
42. Muminnai sun ce haqqun ne Sun tabbata zancen Allah ne
Ba ya kama da batu na mutane
Hakanan yake sam ba tababa
43. Duk wanda ya ce zancen wani ne
Wannan tabbas ya zam arne
Sai ya ci wuta sai ya qone Matuqar bai tuba da sauri ba
44. Allah ya ce “uslihi saqar”
Duk wanda ya ce “qauli na bashar”
Daga nan muka sam tabbar amsar
Ba zance ne na halittu ba
45. Kafirci ne a sifanta shi Kur’ani da batun bayin Shi
Ka kula da batun nan da ka ji shi
Kauce masa ba tsira ce ba
46. Wannan zai sa ka yi tsantaini
Ka wuce arna masu bayani
Na zaqewa har ya zamo fanni Allah da halittu ba daya ba
47. Mun yarda akan ‘yan Aljanna
Su za su ga Allah har sui murna
Hakanan Kur’ani yan nuna
Amma bai ce ga yanayi ba
48. Ba ma wuce gona da iri mu Ba ma cewa da tunaninmu
Mun sallama imanin kanmu
Ba mu kutsa ko tababa ba

WAKEN AQIDAR DAHAWIY Na Kabir Asgar Post No. 5

WAKEN AQIDAR DAHAWIY
Na Kabir Asgar
Post No. 5
27. Ikonsa yana bisa kan kowa
Haka gun Shi buqatar dan kowa
Shi bai da buqata gun kowa Sauki komai yake gun Rabba
28. Huwa Rabbi Sami’un wa Basirun
Haka Allah laisa ka hu shai’un
Khalakal Khalqa summa sama’un
Ba su buya ga Allah Sarki ba.
29. Aqdar duka shi yas sanya su Haka yats tsaro ajalolinsu
Ya san aikin da suke yi su
Tun loton bai yi halittu ba
30. Ya umurce su su yi da’ar Shi
Haka nan ya hane su su sabe Shi
Kudurar Allah da mashi’ar Shi Bawa ba zai kuwa haura ba
31. Kudurarshi abar zartarwa ce
Bayinsa gaba daya ni na ce
Bisa damar Rabbi abar zarce
Suka juyawa ba su haura ba
32. Ma sha’a lahun wannan kana In ya qi ko to ai ba kana
Haka Rabbi yake Mahaliccina
Bai taba rauni gun iko ba
33. Shiryarwa da batarwa sai shi
Falala ga dayan adalcin shi
Ya tsare Yai ma jarabawarshi Allah sam bai zalunci ba
34. Bayi duka kai-kawowarsu
Bisa adalcin Mahaliccinsu
Ko ko falalar wanda ya yi su
Ba sa wuce wanga mataki ba
35. Shi bai da sa’a kuma ba tsara Ba mai hana aikin da ya tsara
Ko ture hukuncin da ya tsara
Yi masa gyara bai taso ba
36. Ba mai rinjaye a gare Shi
Duka wannan mu mun ka fade shi
Mun tabbata wanga da aikenShi Ba za mu sake mu yi qarya ba