SUMA AHLUL- BAITI NE DOMIN ANNABI MUHAMMAD(S.A.W)YA HAIFE SU

SUMA AHLUL- BAITI NE DOMIN ANNABI MUHAMMAD(S.A.W)YA HAIFE SU
.
Via:-Garkuwan Magabata
.
A duk lokacin da ya’yan yan shi’a jebberiyya ko zakzakiyya suka tashi yin magana zaka ji suna cewa wai ahlulsunnah basa son ahlul baiti, amma yanzu zamu gani idan da gaske ne, yan uwa mu karanta wannan.
Dan uwa musulmi ko kasan ya’ya
nawa ne Allah(s.w)ya baiwa Annabi muhammad
(s.a.w) a rayuwarsa ta duniya? To idan baka
sani ba yana da ya’ya guda bakwai (7) ga su
kamar haka:-
1.Zainab r.a
2.Rukayya r.a
3.Ummu khulsum r.a
4.Fadima r.a
5.Abdullah r.a
6.Al-kasim r.a
7.Ibrahim r.a
Wadan nan
sune ya’yansa,shidda(6) daga cikinsu duk diyan nana
khadija r.a ne,ibrahim ne kawai a dan mariya
r.a.To ya yan shi’a basa maganarsu? Bari kuji
abinda yasa basa maganarsu,zainab r.a ta aure
wani dan qabilar banu umaiyya mai suna Abu
al-as dan rabi’i.Rukayya kuma ta aure usman
ibn affan r.a na ukku daga khulafa’u rashideen kuma shima daga banu qabilar umaiyya ne.
Ummu khulsum itama ta aure usman ibn affan r.a
bayan yar uwarta rukayya a.s ta rasu. Fadima r.a
ta aure sayidina Aliyu r.a.Amma su yan shi’a
sai suka dauke fadima r.a cewa ita kadai ce a
diyar annabi sallallahu alaihi wasallam,da hakane jahillai suke daukar
cewa fadima ce kawai a diyarsa,kuma sai aka yi
dai dai da koda annabi s.a.w yayi wafati
fadima ce kawai a raye.da haka ne jahillai a
basu iya gane cewa yan shi’a karya ce suke
yi.don haka muna kira da ayi soyayya da ya’yan
annabi(s.a.w) baki dayansu babu wariya daga daya
daga cikinsu. Hakama a janibin sahabbai(r.a)bamu ware ko daya daga cikinsu,Don haka mu ahlulsunnah bamu
ware daya daga cikin Ahlul baiti ko sahabbai muce bamu sonsa.
kuma bamu sukar ko mutun daya daga
cikinsu, asalima duk muna sonsu(ahlul baiti da sahabbai) baki daya wannan itace hanyar gaskiya.Amma
hanyar da yan shi’a zakzakiyya da jebberiyya suka dauka ta ware wasu daga cikin sahabbai har yan Shi’a jebberiyya na cewa “wai su sun yarda da nagartatun sahabbai” shin abin tambaya anan akwai sahabin da ba nagartacce ba? Su kuma yan Shi’a zakzakiyya cewa suka yi” gaba dayan sahabbai
bancin guda shidda sun yi ridda sun bar musulunci bayan wafatin Annabi sallallahu alaihi was sallam”.hakama a gidan annabi (s.a.w) yan shi’a sun
ware matansa,hakama sun ware ya’yansa ban cin
fadima (a.s)daga cikin ahlul baiti ,to ya akayi kuna son diya
(fadima)amma baku son mahaifiyarta(khadija) ta zama cikin ahlul baiti?
Abin tambaya anan shine ai da fadima(a.s)da sauran biyar bancin
ibrahim duk diyan khadija ne,uwarsu daya
ubansu daya da nana fadima (a.s) ya haka? Duk da mun san cewa Annabi(s.a.w) yana cewa” fadima(a.s) tsoka ce daga cikin jikinsa” amma kuma wannan ba dalili bane da zai sa yan shi’a su mayar da sauran ya’yan annabi muhammad (s.a.w) saniyar ware ba sai dai su hade su gaba daya duk su so su.idan ba haka ba,sai mu ce anya
wannan soyayya ce?Allah yanasa umurnin mu da mu shiga
musulunci baki daya kada muyi munafucci a cikinsa ta hanyar daukar 6angare daga cikinsa mu bar wani 6angare.Ahlul baiti da sahabbai da
waliyyai da duk wani musulmi ahlulsunnah namu ne.
Allah ka bamu albarkar su baki daya. Shin anan waye masoyin ahlul baiti ahlulsunnah ko yan Shi’a?

Advertisements

*ZAN IYA FASA ABIN DA NA YI NIYYA A ZUCIYATA ?*

*ZAN IYA FASA ABIN DA NA YI NIYYA A
ZUCIYATA ?*
*Tambya Assalamu alaikum Malam, barka da
kokari tare da fatan Allah Ya saka da
alheri. Mutum ne abokin shi ya tambaye
sa bashi, shi kuma sai ya bashi amma a
zuciyar shi sai ya raya kyauta ya bashi.
bayan abokin ya samu sai ya dawo mashi da kudin shi kuma kawai sai ya karba
kayan shi. Malam Ya matsayin kudin a
wurin sa ?
*Amsa:*
Wa alaikum assalamTo dan’uwa tun da
riyawa ka yi a zuciya, ba ka furta ba, to hukuncin bai hau ba, kuma ba ka da laifi
in ka fasa, Annabi S.a.w. yana cewa :
“Allah ya daukewa Al’umata abin da suka
riya a zuciyar şu, mutukar ba su furta ba”
Bukhari hadisi mai lamba ta: 4869.
Saidai yana da kyau ka Sani cewa : duk lokaçın da za ka yi kyauta to Sheidan zai
dinga nuno maka talauci, duk wanda ya
bayar da wani abu saboda Allah, tabbas
Ubangiji zai mayar masa da ninkin-ba-
ninki, kamar yadda hakan ya tabbata a
ayoyi da yawa a cikin alqu’ani mai girma. Allah ne mafi sani.
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
8/1/2016.
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

*SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN ALBASHI ?*

*SHIN AKWAI ZAKKA A CIKIN
ALBASHI ?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum
Malam yaya zakkar ma’aikaci ya kamata
ta zamo? Domin wasu ma’aikatu sukan bada alawus a dunkule wanda ya isa
zakkah to amma wasu sukanyi gini ko
sayen filaye ko gonaki da kudin kafin
shekara ta zagayo sun kare
*Amsa*
Waalaikumussalam To dan’uwa, hukuncin wannan albashi
zai fara ne daga lokacin da ya shiga
mulkinsa, don haka mutukar ba su
shekara ba, to babu zakka a ciki, domin
ba kawai samun nisabI ne ya ke wajabta
zakka ba, dole sai an samu zagayowar shekara daga lokacin da kudin su ka
shiga mulkinsa, don haka duk albashin
da ya kai nisabin zakka, kuma aka ajjiye
shi ya shekara to ya wajaba a fitar masa
da zakka, amma mutukar shekara ba ta
zagayo masa ba, to zakka ba ta wajaba ba akan wanda ya mallake shi.
saidai yana daga cikin dabarun da sharia
ta haramta, mutum ya yi abin da zai
sarayar masa da wajibi da gangan, don
haka mutukar ya sayi filayan ne da nufin
kaucewa fitar da zakka, to tabbas ya sabawa Allah.
Allah ne ma fi sani
*Dr. Jameel Zarewa*
13/3/2014

Riba Goma sha Biyu (12) ga Auren Mace ‘Yar Izala!!!

Riba Goma sha Biyu (12) ga Auren Mace
‘Yar
Izala!!!
(1) In kana son zaman lafiya a gidan ka!
Auro ‘Yar Izala.
(2)Ilimi a gidanka! Auro ‘Yar Izala. (3)Tsoron Allah a gidan ka! Auro ‘Yar
Izala.
(4)Babu bin Malamai da Bokaye a gidan
ka!
Auro ‘Yar Izala.
(5)Ba Guru ba Laya a cikin Kitso! Auro ‘Yar
Izala.
(6)Kamala babu fidda tsiraici! Auro ‘Yar
Izala.
(7)Tarbiyan Yara! Auro ‘Yar Izala.
(8)Tsabta a gidanka! Auro ‘Yar Izala. (9)Wallahi sanin Darajar Iyayen ka! Auro
‘Yar
Izala.
(10)Jin Tausayin ka! Auro ‘Yar Izala.
(11)Tawakkali akwai da babu! Auro ‘Yar
Izala. (12)Amanar Aure! Auro ‘Yar Izala.
Kai abin yaimin dadi ya Allah ka Qara
Daukaka Sunnah da Jama,ar da suke
cikinta
da magoya bayanta a duk inda suke

NISABIN ZAKKAR KUDI DR. JAMILU YUSUF ZAREW

NISABIN ZAKKAR KUDI !
Tambaya : Malam donAllah
nawa ne nisabin zakka a
yanzu ?, saboda ina da wasu ‘yan kudade ne na
ke so na sani, ko akwai hakkin Allah a cikin su,
Allah ya kara maka albarka a rayuwarka.
Amsa : To dan’uwa amsa wannan tambayar yana da
mutukar wahala, saboda ya dogara ne da
sanin kudin gram din gwal a kasuwa, ko
kuma na azurfa, domin yana daga cikin kuskure
rubuta nisabi daya tal ga zakka, har zuwa
tsawon shekara guda, kamar yadda wasu suke
yi a calendar, saboda gwal yana tashi a
kasuwa yana kuma sauka . Wannan ya sa na yi
tattaki zuwa kasuwar masu saida gwal a
Madina ranar talata : 2/12/2014 , in da na samu
cewa har zuwa ranar ana saida kowanne gram
daya na gwal din da ba’a sana’anta shi ba akan
kwatankwacin naira : 5969, kamar yadda muka
sani gram 85, shi ne nisabin zakka, don haka,
in muka buga wancan adadin sau 85 , zai ba
mu : dubu dari biyar da bakwai da dari uku da
sittin da biyar (507365). Wannan shi ne nisabin
zakka, har zuwa tarihin da na rubuta a
sama, idan har kudinka sun kai wannan adadi,
kuma shekara guda ta zagayo musu, to zakka
ta wajaba a cikinsu, za ka raba gida arba’in
ka bayar da kashi daya . Allah ne mafi sani

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

YADDA AKE WARWARE
SIHIRI Tambaya :Assalamu
alaikum Dan Allah malam a fitar
dani cikin duhu game da abin da yake
damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin
malami ai mata naganin ciwon mara dz yake
damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma
likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai
malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai
yi mata magani nan take ta haife abinda yake
cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai,
sai take min magana in kawo kudi a sayi
tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya
malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne
shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin
wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan
bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin
biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina
da matsala , ta bangaren aqeeda mun
banbanta? Wassalam na gode malam Allah ya qara
basira. Amsa : To ‘yar’uwa tabbas ba a warware
sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware
sihiri ta hanyar ayoyin Alqur’ani, wasu malaman
sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta
hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da
Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa
ta 122, na suratul A’araf, sai kuma aya ta :
79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da
aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za’a karanta su,
sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya
guda bakwai, sannan ayi wanka da shi .
Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada
wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba’a
yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah. Ya
wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki
sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi yana cewa :” “Duk wanda ya
je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah
ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba’in”
kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai
lamba ta : 2230. Kin ga in mutum ya mutu a
wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma
tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita,
a wani hadisin kuma yana cewa : “Duk wanda
ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to
tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya
zo da shi” kamar yadda ya zo a Sunanu-
abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904, kuma Albani
ya inganta shi . INA GANIN DA IRIN
WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO
KAN HANYA. Allah ne mafi sani . DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN AUREN HANNU (Masturbation) ? DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN AUREN HANNU
(Masturbation) ?Tambaya:
Assalmu alaikum, Allah ya kara
ma malam lapiya da imani, malam
dan Allah menene hukumci masturbation
(Istimna’i) a musulunci Amsa: Wa alaikum
assalam,To ‘yar’uwa Babu nassi ingantacce
bayyananne yankakke da yake haramta
wasa da al’aura har maniyyi ya fito, saidai wasu
malaman sun haramta auran hannu saboda
aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan
bukatar sha’awa ta hanyar matar aure ko bayi
kawai, wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba
ba’a iya biyan bukata ta hanyar su. Yin wasa
da al’aura har maniyyi ya fita yana haddasa
matsaloli a likitance, saidai yana daga cikin
ka’idojin shari’a ; idan cututtuka biyu suka hadu
ya zama babu yadda za’a yi sai an aikata daya
daga ciki sai a zabi karama a aikata, wannan
yasa Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka
halatta auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma
ba shi da halin da zai yi aure. Idan mu ka ce
auran hannu haramun ne, saidai barnar dake
cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta
alfarma a ciki, sannan tana kaiwa ga
cakuduwar nasaba, ta yadda za’a haifi ‘ya’ya gantalallu,
marasa asali, wannan ya sa magana ta biyu ita
ce mafi inganci, mutukar an samu
sharudan da suka gabata . Don neman Karin
bayani duba : Muhallah 12\407 da Majmu’ul
fataawaa 34\146> Allah ne mafi sani.

********ASSALAMU'ALAIKUM YAN UWA BARKA DA ZUWA WANNAN SHAFI, SHAFI NA MUSAMMAN DOMIN YADA SUNNAR ANNABI SALLALLAHU ALAYHI WASALLAM ********