FATAWAR MANYAN MALAMAN DUNIYA KAN WANTA BAI YI NIYYAR AZUMIN RAMADHAN BA SAI DA SAFE(Dr. Isa Ali Pantami)

Akwai fatawoyi guda
biyu na
Malamai ga Wanda ya
kwanta babu
labarin GANIN wata,
kuma sai da gari ya waye ya Samu
labarin
GANIN Watan.
1) Suna GANIN bai da
Azumi, sai
ya Rama, saboda Hadith da ke
cewa: “Babu Azumi ga
Wanda bai
YI Azumi ba gabannin
Alfijir”
2) Wanda kuma itace mafi inganci
ga Malamai irin
Shaykh
Nasiruddeen Albaniy,
Shaykh
Saleem bn Idd Alhilaliy, da Aliyu
Hassan Ali
AbdulHameed cewa
wannan Azumi yayi ko
da safe
mutum yayi NIYYAR. Sun kafa
hujja da cewa
A) Hadithin da masu
cewa Azumi
bai YI ba, yana
magana Akan Wanda ya bar
NIYYAR da ganganci,
ba Wanda ya bari a
rashin sani ba.
Wannan shine
Maganar Abuddarda, Abu-Dalha, Abu
Huraira, Bn Abbas,
Huzaifa. Duba
Taaliqut-Taaliq.
B) Cewa Hukuncin
farilla baya canjawa, kuma a
farkon Musulunci
lokacin da aka
farlanta Azumin
Ashura, akwai
Sahabbai da sun YI breakfast da sabe.
Amma Manzon
Allah, sai ya ce suyi
Azuminsu,
kuma bai ce su Rama
ba bayan RAMADHAN. (Duba
Bukhari 3/212,
Muslim 1125).
C) Masu cewa a
“Kama baki” sai
bayan Ramadhan tukunna mutum
ya Rama, to gaskiya
babu wata
Ibadah Mai suna
Kama baki a
Musulunci. Kuma babu Nassi Akan
Kamun baki.
Don haka abunda yafi
karfin hujja,
itace Fatwa ta biyu.
Idan Baka da labarin GANIN Wata
sai da safe.
Sai kaci GABA da
Azumi ko da
bayan breakfast ne,
kuma Azumi yayi in sha Allah.
Wallahu A’alam.
Allah ya sa mu dace

Leave a comment